KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani saurayi ne yace akaita asibiti kawai, basu jada maganan saurayin ba suka kinkimeta sai asibiti.
Pastor nan na tsine ma wannan saurayi a zuciyar sa.
****
Asibiti………
Sunje aka kar’be su cikin gaggawa, sai dai me wanda zai duba ta baizo ba aka sanar masu.
Cikin kuka da tashin hankali madam Gloria tace “” ku taimakeni karta mutu kunemoshi kunji Ku taimaka”” tausayin ta suka ji fita wani yayi ya nufi gidan Auwal duk da jiya ya sanar zai rin’ka huta wa duk weekend.
Da ‘kar da sud’in goshi Auwal ya biyo wanan saurayin suka nufo asibiti.
Sai mita yake…..
Direct d’akin da take yanufa ana nuna masa, yana gaf da shiga maman ta tace “” don Allah doctor kaceto mini yarinyan yaya,ita kad’ai gareni”” tsaki yayi a zuciyar sa, “” yanzu akan ‘kazaman arnan nan ne banzan can ya tasoni?”” Tsaki yayi ba tare da ya kulata ba yayi ciki.
Shigo masa da kayan aiki akayi ya fara duba ta batare da yaga fuskan taba.
Koda ya gama ya gano matsalan don haka fita yayi bayan yayi mata aluran da zai rage mata zugin.
Yace ma maman ta samesa a office d’in shi.
Bayan tazo bayani yayi mata da cewa “” yarki zata fara al’ada ne”” nan dai yayi mata bayani dangane da damuwar ‘yar NATA ya rubu ta musu magungunan da zasu siya.
Godiya tayi masa ta tafi sayowa a cikin asibitin.
****Da alluran barci ya had’a mata don haka bata farfad’o ba har sai bayan la’asar, bata abinci sukayi sa’anan tasha magani.
Taji dama dama sosai, don haka sukaje suka sanar dashi .
Yazo kwanan da zai sa dashi da d’akin saiga Aisha, kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai.
Shiga d’akin yayi itama ta mara masa baya.
Idonnun sa basu sauka a ko’ina ba sai kan fuskan Joy………………….
Ina bu’katan comments sosai my lovely fan’s
Luv you all????????
Share pls????????????????????????????????
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA
Dedicated to my fan’s
Bismillahir Rahamanir Rahim
????1⃣1⃣to1⃣2⃣
“” Haba biri yayi kama da mutum, ba banza ba ashe ba musulma bace”” yace a zuciyar sa. Shanye mamakin sa yayi tare da
Matsewa ya shiga, dudduba ta yayi tare da mata tambayoyi, tana basa ansa yana rubutawa, koda ya gama tunda yaga ta samu sau’ki sosai kawai sai ya sallame su tare da cewa yana mai kallon maman ta “” madam zaku iya tafiya, ba wani matsala bane sosai mata da yawa suna irin wanan ciwon, a kula da shan maganin ta””. Godiya tayi masa shi kuma ya fita ba tare da ya sake ko kallon taba, tattara kayan su suka bar asibitin, bayan sun dawo gida uwan ta cigaba da kula da ita, har tasamu lafia, duk da bawai ya bar mata bane, yana mata kawai dai tana daurewa ne.
Yana tashin mata lokaci zuwa lokaci, shi kuma Auwal da sanin sa ya sallame ta, domin haka kawai yaji bazai iya juran ganin ta ba, kuma ma wai shine zai rin’ka duba ta.
Yasan dai in dai suka kula da maganin zataji dama dama, domin mafiya yawancin irin wanan ciwon sai mace tayi aure take bari.
Ya sallame ta amma bai huta ba sam, domin sallaman kawai yayi amma hankali sa nakan yarinyan, bai san mai yasa tunanin ta yasashi gaba ba kusan kwana biyu kenan.
Kuma tun daga ranan bai sake sata a idon saba, tunin ta yayi masa yawa wanda har yana son shafan aikin sa, dare bai da sukunin barci yadda ya kama ta, idon sa photon yarinyan kawai yake gani, musamman wasu surori na jikin ta dake firgita shi, duk lokacin da ya tuno wani sura na jikin ta, to tabbas sai yasha magani yake samun sukuni.
Safe ma haka kai a ta’kaice wuni yake cikin tunanin ta, ya Kuma rasa dalilin hakan. Yau kusan sati bai sata a ido ba ko ‘kawarta bai sake gani ba, don haka wani iri yakejin sa. Monday ne yau amma sam yaji baisan zuwa asibitin, ko wanka bai ba ya fito waje ya tsaya daga bakin ‘kofar gidan sa, lokacin wurin 7:35pm ne, ko minti biyar da tsayuwa baiyi ba sai gashi sun fito daga gidan su Joy d’in, jikin su sanye da uniform, idon ya kafa mata a fakaice ya d’auke kai. Ajiyan zuciya yayi tare da cewa yana kallon su suna tafiya cikin natsuwa, “” ta rame sosai, kar dai nace ciwon ne har yanzu?”” yana mai cigaba da binta da mayatatcen kallo.
“” Oh, my god, duk ni naja hakan, laifi nane, bazan cire miki ba, amma da zan iya kula dake ki samu sau’ki fiye da yadda kika samu. Sorry! “” yace kamar tana gaban sa.
Bai koma gida ba har sai da suka ‘kule masa, shiga gida yayi yana mai jin ‘karfi a jikin sa.
Wanak yayi tare da had’a breakfast sa’an nan ya fito gidan domin wuce wa asibiti.
***
Abu ya zama wa Auwal kamar ibada, kullum sai yazo ya tsaya duk safe yaga wuce war su makaranta sa’an nan yake samun sukuni, ya rasa maike damun sa game da yarinya, ya damu sosai da ita.
Yanzu haka kimanin watan sa hud’u kenan a garin kuma tsahon wanan lokacin tunanin yarinyan ya’ki barin ‘ka’kalwar sa.
Satan kallon ta ya zama masa kamar ibada, duk ranan da bai ganta ba bai samun sukuni.
Sau da dama yakan tsare kansa da tambaya “” meyasa Auwal, meye gamunka da ita?, ba musulma bace ba””. Ire-iren wad’an nan tambayan dama wasun su yake wa kansa, kuma har wa yanzu babu wanda yazo duba sa, domin Abba ya hana, tun ya damuwa da ‘bacin rai har yazo ya ha’kura. Yanzu ya saba da garin yana jin dad’in garin sosai, ya saba da mutane garin, harta madam Gloria suna mutunci sosai da ita, watarana ma har girki dashi take tana kai masa har gida, kyakkyawa alaqa ke tsakanin su, har yanajin tana d’ebe masa kewan gida sosai.
Ba musulma bace, bata ‘kaman musulmai, domin har yanzu tana tsanani son mijin ta duk da ya dad’e da mutwa.
Yau weekend, zaune yake a ‘kofar gidan sai ga Joy ta fito daga gidan su Aisha, sanye take da kayan da kusan kullum indai ba makaranta ba yake ganin ta dasu, kayan da duk yagan ta dasu yanzu yake jin ba’kin ciki sosai.
Riga ne white mai hannun vest, da gajeran wando, kayan sun matseta sosai.
Kallo d’aya ta masa ta d’auke kai, ciza yatsa yayi tare da ‘kwafa.
Gida tayi bayan ta yabi da kallo, gauda kai yayi da sauri idanun sa sunrine saboda ba’kin ciki, “” ita dai yarinyan nan kullum cikin shigan karuwai take”” yace yana mai da nasanin zaman sa.
Yana zaune madam Gloria ta fito zata anguwa, bayan ta Joy ne ta fito domin mata rakiya.
Da fara’a a fuskan ta tace “doctor hutawa ake?, eh madam”” yace yana hararan Joy, “” kutuman uba”” inji Joy.
“” Lafian ki kuwa?, keda wa?”” murmushi tayi domin bata San maganan nata ya fita ba, “” name mama, na ‘kaniyan ki, ba zagi naji kinyi ba?, a’ah, zagi kuma? ni banyi wani zafi ba”” tace tana rama hararan da yayi mata.
“” Ina wuni”” yace da ita, “” lafia qalu doctor, ya aiki dai?” “lafia qalu, za’a fita kenan?, eh doctor, to Allah tsare””.
“” Amin doctor, nagode”” tace tana murmushi, shi kuma yayi mata sai ta dawo.
Wuce shi sukai, raka uwan tayi da nisa saida ta samu mashin sannan ta dawo, zata cikin garine saro kaya domin kayan da take siyarwa duk sun ‘kare.
Dawo wa tayi tana zancen zuci, “” shege kawai d’an isaka, haka kawai ban maka komai ba ka kama hararan ta da shegun idanun nan naka mai kama da na mayu, shiyasa tunda naga take taken sa d’an iskan yanzu na gummaci ciwo ya kasheni da dai ya duba ni, ba ta’kaman sa da girman kan sa don yaga shike duba mutum ba?”” tayi ‘kwafa.