KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace yana mai takawa abinsa.

“Ni nayi nan, Allah had’a ki da dai-dai ke sai aje can a ‘karata , misssss”.

Ya cigaba da tafiyan sa, kuka ta fashe dashi mai tsanani, ha’ki’ka yaci mata mutunci tace cikin zuciya, zuciya nata na mata ‘kuna.

” Wato nufinsa ni karuwa ce ko? hmmm” tace tana cije le’ban ta.

“Ba komai ba laifin ka bane, kuma nagode da taimako” bai masan tanayi ba domin yayi nisa.

Tayi nisa cikin tunani sai ta tuna inda take aiko bata san sand ta mi’ke da gudu ba tama manta bazata iya tafiya ba, duk da taji a jikin ta, amma guma ta tsira da mutunci ta.

Tafiya take tana tattare yagaggen rigan ta tana rufe ‘kirjin ta dashi.

A haka ta kawo har gida mutane nata kallon ta amma ko ajikin ta, hakan bai dame taba sam.

Tura ‘kofar gidan su tayi ta shiga, wurgar da yagaggen rigan tayi ya rage daga ita sai d’an guntun siket d’in ta.

‘Daura ruwan wanka tayi, domin a lokacin babu abinda take bu’kata da ya wuce hakan.

                  ***

Auwal kwance a gadon sa yana ta rafka uban kuka kamar wani mace, kuka ya’ke bil ha’ki da gaskiya, yayi dana sanin ganin ba’kin abinda ya gani a idonsa.

Zuciyar na masa zafi mai tsanani, da ya rufe idanun sa abinne ke bayyana masa kamar yanzu ake a gaban sa.

Yana hango abun dake fizgan zuciyar sa gare ta a hannun wani yana sarrafasu yadda ya gadama.

Wani irin ‘kara ya saki tare da ri’ke kansa.

“Duk ita ta janyo ta jama kanta, musulunci yayi, Allah ka ‘kara mana imani” yace tare da dafe zuciyar sa.

“Kullum bata da shiga sai wanda zai hankali mutum gare ta, kai anya ba ita tanemai ba?” yace yana cije le’be.

Kiran sallah ya tayar dashi, mi’kewa yayi direct toilet ya shiga wankan yayi sa’an nan yasa white d’in jallabiyan sa ya fito bayan yayi alwallah domin tafiya masallaci.

Jin idanuwan sa sun masa nauyi yasa shi saka gilasa a fuskan shi, domin baiso a gane damuwar sa.

Yana rufo gidan sa, yaji motsin tafiya, bayan ya rufe ya juyo domin tafiya, sai yaga Joy tsaye kusa da gidan nasa, ta jingina da bangon gidan su Aisha, hannun ta rungume a ‘kirjinta.

Idanu wan ta nakan sa tunda ya fito, d’auke kai yayi kamar bai ganta ba tare da had’e fuska ya fara tafiya.

“Nagode doctor” tace cikin za’kin murya, tsayawa yayi cak, tare da sauke ‘boyeyyen numfashi.

Can kuma mai ya tuno kawai sai ya wuce fauuuuuuu.

Murmushi ta saki tare da lumshe idanuna ta, tana mai bin bayan sa da kallo.

Bata bar kallon sa ba har dai ya kure mata.

Sa’an nan tayi gidan su Aisha.

Manager please

Share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????????

 (Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA

A fuwan my fan’s, bakuyi fushi bako? nama sani baza kuyi ba domin kun kasance masu ha’kuri dani, ina godiya sosai sosai.

Dedicated to my fan’s, luv you guys????

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????1⃣5⃣to1⃣6⃣

Shiga gidan su Aisha tayi, maman Aishan ne zaune a kusa da murhu tana fiffita wuta, “sannu da gida mama” tace tana d’an du’ kawa kad’an.
“Yauwa Joy” tace fuskan ta d’auke da murmushi, “mama Aisha ta dawo kuwa?” “a’a, amma yanzu zaki ganta don zataje islamiya anjima, okay” tace tana mai zama a kan turmi dake tsakar gidan.

Suna zaune shiru sai ga Aisha tayi sallama, ansa mata mama tayi. Ita dai Joy kallon ta kawai take.

“Besty yakike” cewar Aisha lokacin da ta’kariso gaban ta.

“Lafia” kawai tace da ita “zo muje ko?” Aisha tace, mi’kewa tayi sukayi d’akin Aishan.

Kwanciya kawai tayi a katifar Aisha daga shiga d’akin.

Kallon ta kawai tayi ta kyauda kai, domin tunda taga haka to miskilancin ne tsaba ya tashi.

Sai dai abin mamaki gani kawai tai lokacin da ta waigo tana ta faman murmushi.

Cire hijabin hada tayi tare da d’aukan na islamiya ta saka.

Zama tayi kusa da ita tare da cewa “besty zani islamiya, zanje na dawo nasha labari domin da alama dai wanan murmushi da ake saki zanji labari mai dad’i”.
Ta’ba baki tayi tare da mi’kewa ” sai ina kuma besty? inace zaki jirani na dawo ne?” “Uhu’um” tace da ita tare da riga ta barin d’akin.
Sometimes tana mamakin ‘kawar nata, “wata irice ita gadai tanan”.
Fito wa tayi lokacin har takai ‘kofar gida, ‘kofar gidan su ta tsaya tana kallon gidan Auwal.
Fitowan Aisha yasa ta kauda fuskan ta daga wurin ta maida kan Aishan.
” Besty sai na dawo ko?” d’aga mata kai kawai tayi, ita kuma ta wuce makaranta ta.

“Baki gajiya kedai, kullum makaranta, ina zan iya wannan wahala, ga wani abu biyabiya dashi”.
Tace tana ta’be baki tare da barin kallon ‘kawar tata.

Tsawon lokaci tana tsaye a wurin kafin tayi cikin gida.

Koma wanta da kad’an maman ta ta dawo, saukan ta a mashin Auwal ya fito daga gidan sa, da murmushi ya’ke yace “sannu da zuwa, yauwa yaron kirki” tace dashi “Joy ta dawo kuwa?”.
Wani ‘kululun ba’kin ciki ya tokare masa, amma ya daure yace ” uhmm”.

Shiga gida tayi shi kuma ya wuce inda zashi.

               ****

Watan Auwal shida a ‘KAUYEN ‘YAR KADDE, abubuwa da dama sun faru, daga ciki akwai yawan shige masa da Joy keyi, kamar idan ta gansa ta gaishe sa da dai sauran su, ta rasa maike damun ta dangane dashi, kuma sau goma zata masa magana bazai tanka taba, duk sanda ya ganta idan a hanya ne canza hanya yake, idan kuma ta tasame sane sai ya d’auke kai yayi kamar bai ganta ba.

Auwal kwance yana waya da mami sai faman narke mata yake tana biye masa “mami don Allah ki ro’ki Dady ya yarda na dawo, wallahi mamina nayi missing d’in ki, ga ‘kauyen ko dad’i babu, har yanzu ban saba dashi ba”.

” Ga sister zata dawo nan da sati mai zuwa,”.
“Ni Auwal bansan yadda zanyi ba, nayi nayi koni nazo na ganka ya’ki, bansan yadda zanyi ba nima inason naga boy d’ina” tace tana murmushi.

Turo baki yayi tare da cewa “mami niba boy bane gaskiya na girma” “da gaske my son? uhum”.
“Amma mami na haka zanta zama sai na shekara sanan zan ganku?, eh son tunda haka Dadyn ku yake so”.
” Haba sai kace mara gata, mara galihu? hab fisabilillahi kamata haba mami na, do something “.

” Hmmm, bari zan jaraba Allah sa adace, amin mami na, ko kuma kawai kisa ‘yan gaban goshin sa agaba nasan suna cewa zaiyi na’am”.
“To bari suzo muga” “yauwa mamina shiyasa nake tsananin ‘kaunar ki, love you mum” yace tare da sakin masa kiss ta wayar.

Dariya tayi tare da kashe wayar, shiko wani farin cikin da yadad’e baiyyi ba yaji ya mamayeshi smiling kawai yake.
Tashi yayi daga kwancen tare da shiga toilet yayi wanka, T-shirt mai ratsin baki da fari yasaka da ba’kin wando, kayan sun matu’kar kar’ban sa.

Kallon kansa yayi a mirror shi kansa yasan ya had’u, smiling yayi tare da cewa “yaron mami ka had’u” tare da cewa yima kansa kiss ta mirror d’in.

Bayan ya kintsa ya fito domin le’ka asibiti lokacin la’asar ne sakaliya.
Yana rufe gida ya juyo yaga mutum a bayan sa, kauce wa yake ninyan yi ta tare, tace tana ya mitsa fuska “doctor cikina na ciwo ko zaka taimakamin please?”.
Kansa na kallon gefe yace ” nan ba asibiti bane, baya ga haka kije kinemi wani not me”.
Kallon sa take ta ‘kasan ido, “zaki iya bani hanya na wuce” yace fuskan sa kamar wanda bai ta’ba dariya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button