KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Batayi magana ba, ita ko Hajiya Sa’a har zataje takira doctor sai taji anrik’e hannu.
Tace “,a’a Sa’adatu ba ,abunda kemin ciyo, nadai yi mafarkin da na saba”.

Tace “a’a gwaggo yanzo ba mafarkin bane basujima da bari wajan nanba Kuma nasan yanzo zasuzo”.

Tace “,to Allah kasa”.
Tace “,Ameen”

Bajimawa ko, sai gasu sun zo ,zaune suka sameta rik’e da kufi ahannuta tanashan tea.

D’ay, bayan d’aya, suka fara shugowa har suka shigo gaba d’aya, da ido take kallon su .

Gaisheta suka farayi Amma ba ,Wanda ttakarbma ma

Haka suka rinka jinyar ta kullum suna can Amma bawanda ta tab’a yima magana.

Kwananta uku akasela meta, dan taji sauki sosai, haka suka dawo gida kullum suna saman hanyar gidan, kuma har yanzo, inba sallama ba ba abunda ke, had’asu.

Sunyi Bata hakur har sugaji amma ko kallo basu samuba da ita har yayar su.

Dan haka suka yanke shawara suje sugayama Malam Usuman.

Bayan “,sungaya masa yace suje gashinan zowa”.

Sai da yabiya gidan Malam Garba yafad’a masa abunda kefaruwa Malam Garba yace “,to muje”.

Haka suka Isa gidan bayan sunyi sallam, tabasu izinin shiga, suka shigo, bayan sungama yima ta yajiki, suka d’aura da cewa ,”kuma gami da yaran nan ne, dan Allah kiyi hakuri, sunyi kuskure kuma sungane kuskurinsu, duk, da munsan bayin kansu bane da haka dan Allah kiyi hakuri.

Dak’ir sukasamu tayi hakuri Amma kushi da sharad’i Malam Garba yace “,to akirasu”.

Bayan ankirasu Malam Usuman yace “, munajinki”.

Gwaggo Maryam tace “,na d’aya shine suje suneme yafiyar yayar su Sa’adatu.”

Tace “,na biyu kowanen su Ina sun yasake aure ma’ana inasun sukara mata”.

Tace “,kuma babu dole “.

Da ,”sauri suka cemata sun amince”.

Nan su Malam Usuman “,suka fara fad’i Alhmdllh”.

Nan Malam Garba yayi musu nasiha mai ratsa jiki, yasa musu albarka, yace ,”sutashi suje gidan yayar su”.

Suka ce “,to”.

Haka suka tashi sukaje gidan inbanda ma mijinta sanannena agari da baza su gane gidan ba.

Suna kowowa mufida da Ammar zasu fita, da sauri takara suwajan su.

Gashesu tafara yi kana tayi musu iso zuwa falon bak’i.

Sai da takawo musu abunsha sannan taje, tafadama Momy su.

Koda Hajiya Sa’a ta k’arasa falon, tsaye tayi nabin su da kallo suma haka.

Suleman yace ,”Yaya dan Allah, ki karasu kizauna please”.

Ahankali tataku har takawo tazauna saman kujera.

Sun d’au lokacin bawanda ya iya cewa komai.

Sai can Munsur yayi k’arfin halin, fara magan,

Yace ,”dan Allah kiyi hakuri munsan muyi ba dai dai ba duk ni nasan bayin kammu neba, wallahi yaya kaba d’aya mantawa muka yi damuna da wasu ‘yan uwa dan Allah yaya kugafar cemu”.

Nan suma suka fara bata hakuri.

Tace bakumai,” Allah yaya femuna”.

Nan sukacigaba da fira har suke gayamata abunda gwaggo Maryam tace musu.

Tace “,amma gwaggo tayimin dai dai, saura kuma naji shuru”.

Suka ce ,”a’a wallahi zamu samu matan nan bada jimawa ba”.

Sai Alhaji mansu yayi gyaran muraya yace ni gaskiya Ina da wadda nake so duk da nikaina inaganin abun ba maiyuwa ba ne dan nayi taciri abun araina amma kamar lokacin nakesa shi ,bansa yadda zamisilta muku yadda nakeson yarinya ba “.

Yakuma cewa “,kunsa kuwace ce?”.

“Suka ce a’a”.

Sai da ya d’au lokaci, yana mai duk’ar da kanshi a kasa, saboda abun yayi mishi nauyi fad’a a aharshe.

Yace ,” Fateem K’awar ‘yata Zainab”.

Nura da Abbas tari suka had’a baki wajan kiran “,mika ce?”.

Yace ,”abunda kukaji nafad’a”.

Hajiya Sa’a dataga zasu kawo mata wata hujjar da bata yadda da ita ba, tace ,”kuda kata”.

Gabadaya, sukayi shuru, tace ,”Mansur kana son ta ko?”.

Yace “Inson ta Hajiya”.

Tace ,”ita yarinya nason ka?”
Yace ,”ita yarinya batama san Inson taba”.

Tace “to kaje kasameta kagaya mata, nikuma daganan na d’ura inda katsaye”.

Yace ,”Hajiya ta ina zan fara?”.

Tace “,kota ina za kafara kafini sani, kuma kwana biyu na baka kazo kagayamin mi ake ciki”.

Ta “,kuma cewa kuma akowani lokaci anajiran tako”.

Suka “ce insha Allah.”

Sai da suka ci hararsu ,sannan, sukayi mata sallam suka tafi.

Muje zuwa

Commet
Nd
Share
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

KAWAR’YATA CE

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta Sai b’ata, burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}

    🎐G. W. A🎐

GASKIYA DOKIN K’ARFE🏇

Story & writing
By
Sumy

Dedicated to my innaro🥰

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

Page 1�3�

Bayan kwana biyu sai alhaji mansur yaje ya gayama hajiya sa’a, “Yace ya fad’a mata Amma Dana fad’amata sai Naga duk ta rikice, sai hajiya sa’a tace “Badai ka fad’amata ba”? Yace “eh hajiya na fad’amata”.

Tace “To kaban address din gidan su” yabata address d’in gidan su, tace “Kataya mu da addu’a Allah yasa a dace. “Yace ai hajiya addu’a kullum cikin yinta muke, Dan haka Ni zan wuce duk abinda ake ciki muyi waya,”Tace to Allah ya kiyaye Amma kowane lokaci zan iya shigowa gidan naku “, yace “To hajiya yaya” ya mata sallama yatafi.

Bayan hajiya sa’a taje gidan su fatima dak’yar suka amince da maganar bayan fafatawar da akayi dasu.

A b’angaren su Hajiya Shafa suna ik’irarin cewa ba macen da ita Isa ta shigo gidan su Bale har tayi kishi dasu.

Cikin ikon Allah aka d’aura auren Alhaji mansur da Fatima aikuwa jikin su Hajiya Shafa yayi sanyi, Amma duk da haka basu yarda makaman ya’kin suba.

Cigaban labari

Tunda Daddy yayi tafiya bai sake Kiran mommy ba, har Saida yayi kwana biyu saboda ayyuka dasuka rik’esa bai samu kiranta ba lokacin daya kirata bai mayi tunanin zata d’auka ba, can sai ta d’auka “Yace fushi akeyi ne Dani”? Tace “Ni bana fushi dakai yace “Allah yasa, dafatar Kuna lafiya”? Tace “Lafiya k’alau muke” yace “Ina Yara da k’anwar ki na Kira wayar ta a kashe”?

Tace “Ai kafini sanin inda take” “Yace dana San inda take ai bazan tambaye ki ba” tace “ka tambayi yayar ka” yace “Hajiya sa’a”? Tace “eh ita” “Yace ki gaidaman da Yara na” Tace “zasu ji” sukayi sallama ya kashe waya.

Ya Kira Hajiya sa’a bayan sungama gaisawa yace “Fatima na wurin ki?”, Tace “eh tana wurina ko da wani abun ne?” Yace “A’ah dama Kira nayi naji ko tana lafiya”, Tace lafiyar ta k’alau” har zata katse wayar yayi sauri yace “Yaya!” “Tace Koda wani abun ne?” yace “eh, Bata kusa ne a Bata wayar?” Tace “wace?” Yace “Fatima” Tace “Bata kusa” har zata sake katse wayar yace “Yaya Dan Allah idan nayi wani laifi ne a yafemani ayi hak’uri” Tace “inaga kamanta gwagwar mayar da muka shiga kafin iyayen ta subamu auren ta” yace “wllahi A’a Yaya ban Manta ba” Tace A’a kamanta Mana, Dan inda baka Manta ba da bazaka barta a matsayin ‘yar aiki ba, to wallahi bari kaji bazan d’auka ba idan har ‘yar aiki ce bakuda ka nemota, Kuma kajawa matar ka kunne itada yaranta ba ‘yar aiki bace aka kawo masu “.

Yace “Wallahi Yaya banma San da cewa ana sata aiki ba, Amma kiyi hak’uri” ta k’ara d’aukar zafi tace “Inako zaka sani tunda baka kula da ita, Tace Kuma idan Kai baka d’au mataki ba wallahi nida kaina zan d’auka” tayi tamasa fad’a, shidai hak’uri kawai yake Bata daga k’arshe dai tace ta hak’ura ya bari ta turomasa number Fatima.

Bayan sungama waya takira Hajiya Ummu Tace “Ga mijin Fatima Nan zai Kira ta nuna mata yadda zatayi wayar dashi, danso nake tun a waya tarikitar dashi ya kasa hak’ura har sai ya kirani yace a mayar Masa da matar sa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button