KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Hajiya Ummu Tace “Baki da matsala indai wannan ne” ta mata sallama, sannan ta tashi taje d’akin da Fatima take shigarta keda wuya wayar Fatima tafara ruri, ta tsaya a bakin k’ofa tana kallon Fatima Tace mata ” Ba wayar ki bace take ringing?” Fatima Tace “eh itace” Hajiya Ummu Tace “kid’au ka Mana koba mijinki bane yake Kira?” Tace “eh shine” Tace “ki d’auka Mana Kuma kisan yadda Zaki magana dashi ba kamar yadda zakiyi da sauran mutane ba, ki lank’wasa muryar ki ki karai rayata” koda Hajiya Ummu takai k’arshen maganar ta har Kiran ya katse wani ya saki shigowa.

Fatima ta d’auka tace “Assalamu Alaikum” tana Mai jin kunyar hajiya Ummu, ajiyar zuciya yafara yi Mai k’arfi kamin ya amsa sallamar da “Wa’alaikumus Salam” Tace “Daddy Ina wuni?” Yace “Lafiya k’alau kwana biyu nabar jinki nayi missing d’inki sosai, Baki ko nema na” Tace “Hmmmm Daddy ya aiki?” Yace aiki Alhamdullillah Yaya ta d’auke Mani ke ko? Amma idan nadawo Zaki koma ko?” Tace “umm” hajiya Ummu ta Harare ta ta mata alama da ba haka zata ce ba Tace “eh zan dawo” yace “yauwa” haka yayi tajan ta da fira tana nok’ewa duk da hajiya Ummu na hararar ta, Amma ta kasa sakin jiki dashi sosai.

Yace “Fatima Baki ma kewata ba ko?” Tace “A’a Daddy nayi kewar ka” yace “Hmmm kozaki zo kitayani aiki idan nagama muzo tare?” Dayake wayar a handsfree take sai Hajiya Ummu ta harereta, Tace “duk yadda kace Daddy” yace ohk “inaso kizo idan na kammala aikin da nake sai mu dawo tare” tace “to Daddy” daganan sukayi sallama da ita.

Bayan sun kammala wayar hajiya Ummu Tace “yanzu Fatima haka zakije kina wannan kunyar, koma miye gara ki ajeshi tun anan tunda Allah ya Riga da ya k’addara mijinki ne ba yadda zakiyi, Kuma aljannar kice Zaki nema idan kin tsaya Dan kanki idan ma Baki nema ba Dan kanki kowa tashi tafishe shi, Dan ko mamar ki aljannar ta take nema.

Dan Haka kema ki tsaya kinemi taki, Tace “insha Allah zan kiyaye nagode” Tace “Allah yasa danma Kar watarana naje gidan ki Naga sab’anin abunda nakoya maki Allah zamu sab’a dake” Tace insha Allah hajiya bazamu sab’a ba”.

A b’angaren Alhaji kuwa bayn sun gama waya da Fatima ya Kira Hajiya sa’a, yace “Yaya dama k’anwar ki nakeso ki aramani tazo ta tayani aiki kamin na kammala saimu dawo tare” Tace “bazan bayar ba salon kamayar da ita ‘yar aiki” yace “haba Yaya Wallahi bazan mayar da ita ‘yar aiki ba, karmuyi haka dake pls” Tace “bafa zan bayar ba Dan haka sai anjima” tafad’i haka tana Mai niyyar katse kiran.

“Yace Dan girman Allah Yaya kada ki kashe ki bani ita sati biyu kacal ne zamuyi kamin na k’arasa mu dawo” Tace “Sai nayi shawara, idan nyi shawara zan Kira ka” ta datse kiran.

Bayn sun gama waya da daddy hajiya sa’a ta Kira hajiya Ummu tafad’a mata yadda sukayi da daddy, Tace tanason a k’ara shirya Fatima saboda tasan ko gobe Tace ma Daddy ta yarda biza kawai zaisa a mata ta biyoshi.

Kuma Bata shirya bashi ita ba yanzu sai komai ya kammala, Tace “kinsan cikin manya matane zata kishi banaso a samu matsala ko kad’an” Hajiya Ummu Tace” Baki da matsala indai akan wannan ne, Sukayi sallama.

Bayan kwana biyu daddy ya shama hajiya sa’a Kai Dan Allah ta yarda ta turomasa Fatima dak’yar ta yarda, murna a wurin sa ba’a cewa komai Yana ta murnar Fatima zataje wurin sa.

Bata yarda zata bashi itaba Saida ta gindaya Mai sharad’i “idn har suka dawo bataga Fatima ta canza ba shida ita har abada,” “yace ya yarda bama za’a samu matsala ba” Tace “zuwa ranar Friday za’a mata biza” yace “Allah ya kaimu” Tace “Ameen” sukayi sallama.

Tundaga lokacin Nan kullum sai ya Kira Fatima, mafi akasarin wayar su a gaban hajiya Ummu takeyi tana koya mata yadda zata Masa magana aikuwa ya k’ara rud’ewa yaga duk Jumu’a ta dad’e Bata zoba.

Burinshi kawai Jumu’a tazo ranar da zaiga Fatima shi ko zai samu natsuwa, haka akayi ta shirya Fatima kamin ranar Friday Koda ranar Friday tayi idan kaga fatima bazaka gane taba saboda yadda Tasha gyara.

Fatan ta sai walkiya takeyi tayi sulb’i ga wani fresh din datayi ga wani sihirtaccen kamshi da takeyi…………

Muje zuwa

Comment
And
Share
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

     *KAWAR 'YATA CE*

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira.}

  🎐G. W. A🎐

GASKIYA DOKIN K’ARFE.🏇

Story & writing
By
Sumy

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

Page1�4�

A b’angaren su Hajiya Shafa sun sake shirya meeting d’in, kamar yada suka Saba had’uwa su bakwai yau ma sun Had’u, bayan gabatar da gaishe -gaishe tsakanin su mommy Tace.”A gaskiya naga abun nan yak’ici yak’i cinyewa, kuma gashi Hajiya Sa’a ta d’auke yarinyar nan bansan a inda takai taba nayi bincike iya bincike bangane inda takai taba, kuma an tabbatar man da fatima Bata gidan, Hajiya Sa’a dan Haka nake so aman bincike akan ina ne Hajiya Sa’a ta kai Fatima”.

Hajiya Shafa tace “yaushe tazo ta d’auke ta?”. Mommy Tace “wllhy bayan tafiyar Alhaji tazo ta d’auke ta”. suka ce “ai baki gayamana ba tun lokacin da sai mu San abunyi”. Tace “ai nazo nafad’a sai naji ance auren Alhaji sulaiman za’ayi shiyasa hankali na ya d’auku ban fad’aba”.

Nan suka ce “bari harda shi zamu sa a bincika a inda yarinyar take”.

Tace hakan ma yayi dan dai ni gaskiya banaso yarinyar ta zauna a gidan, kwata- kwata bana so ace wannan yarinyar itace kishiya ta koda ta zauna a gidan nafiso ta zauna a matsayin’yar aiki na, amma ba’a matsayin kishiya ba ko bai sake ta ba sunji sungani zata iya zama to a maisar Mani ita a matsayin ‘yar aiki gidana dan banaso ace kishiyata ce.

Hajiya binta Tace “Nima dai gaskiya a san abinyi dan bama son ace tashigo gidan”.

suka ce dukkan mu yakama ta mu d’au mataki dan tunda biyu suka fara, suma sauran a can sukayi.

Hajiya Shafa tace “hakan ma suke nufi dan da Hajiya Sa’a baza ta cema Alhaji Aliyu ba saura shi ina tunanin gaba d’aya take son su kara, kuma wallahi Bata isa ba Dan bazamu k’yaleta ta ba Muna kallon ta, Dole mu d’au mataki akanta”.

Haka dai suka k’arasa meeting d’in su, sun yanke shawarar sake ziyarar malaman su kafin jibi Dan ita Hajiya Hadiza gaba d’aya ta rud’e tafiso a mayar da yarinyar gidan ta ta cigaba da mata bauta, Dan bataso yarinyar ta zauna a gidan Hajiya Sa’a a haka dai suka watse daga gidan.

Mommy na komawa gida ta iske su Zainab a falo suka mata sannu da zuwa, ta amsa sannan ta d’aura dacewa.

“Angama aikin gida Hala?”.

Suka ce eh Khalsum tace “Mommy Wai yaushe Daddy zai dawo ne?”.

Tace “sai Nan da sati biyu yace zai dawo”.Tace “Allah Mommy nidai ki kaini wurin daddy” Tace “naji zan kaiki” Tace “to nidai Mommy ki Kira Mani shi pls”.
Tayi maganar kamar wanda take shirin yi kuka.

Tace “bazan kiraba ki bari idan ya kira zan Baki”.

Da k’yar’ir tasamu Khulsum ta k’yaleta dan a gajiye take, burinta kawai tashiga d’akin ta kwanta.

Har zata shiga bedroom d’inta tace “Zainab kimana girki ko kad’an ne”.

Zainab ce ta bata amsa da cewa,”Toh Mummy”.

Mumy Kallonta ta maida ga Nabila dake kwance tace “Ke meza kiyi?”.

D’agowa tayi ta kalleta sannan tace. Hmmmmmm Mummy kinsan yau a gajiye na dawo daga school, bazan iyayin komai ba”.

Mummy tace “ke daman Nabila ba aiki kike soba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button