KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Bayan sun gama gaisawa, Hajiya Sa’a tafad’ama ta tafiyar Fateema gobe.

Mahaifiyar Fatima tayi murmushi, sannan tayi musu fatan alhairi.

Mik’e wa tayi ta d’auko wasu Kaya aleda ta mik’awa Hajiya sa’a tace,”ga sak’o ki Kai wa fatima.

Hajiya sa’a ta amshi kayan, sannan sukayi bankwana ta tashi ta tafi.

Ab’angaren su Mummy tunda safe taje gidan Hajiya Safa,basu b’ata lokaci ba suka kama hanya sukaje wurin malamin su.

Koda sukaje mutane sunyi yawa, sai da suka bari mutane sun rage sannan suka shiga.

Bayan sun kai gaisuwa gareshi sannan suka k’ara kora musu bayani, Hajiya Safa tace, “Malam gamida maganar da kasani ce har yanzu abu yak’i k’arewa.

Malam Yayi murmushi irin na mayaudaran malamai yace,”ku tsaya na duba maku na gani.”

Wani babban faranti yajawo wanda aka zuba yashi aciki.

yatsun hannun sa d’aya, yasa yafara layi _layi, jin kad’an kana yad’ago ya kallesu yace,” gaskiya gamida ita Fateema, akwai wani b’oyayyen wani abu, wanda nakasa ganin miye shi, amma kubari nan da kwana biyu kuda wo, amma gami da wannan auren da kuke tsammani, to baza’ayi shi ba, amma kusa ido kuyi kallo”.

Sukace,” to Malam, dan Allah ak’ara dubamana, dan Yanzu ma haka sun d’auke ta daga gida, kuma Malam, dan Allah ina son acire son da ‘yata Zainab kema Fateema, saboda abun nadamu na.

Malam yace,”bakida matsala.

Wani d’aurin magani yabata, yace kizoba mata ga abinci ko lemu tasha ki tabbatar da tasha shi.

Ta mik’a Hannu ta amshi maganin tace,”to Malam na good.”

Malam Yayi dariya yace,”aiku na waje na ne, kuje kawai zakiga abunda zai faruwa,

Haka suka dawo gida, da dad’i ba dad’i,.

Mummy kai tsaye d’akin su Zainab tace wuce.

Kwance ta same ta Mummy tace,” Zainab yau mi kika girka mana?”.

Zainab tace”, Mummy kindawo?”.

Mummy tace,”Yanzu nadawo, kin gama abinci?”

Zainab tace,”nakusa kammalawa.

Mummy tace,”to bari nak’arasa, dan nasan ke kad’ai ce kikayi aiki banda Nabila”.

Zainab tace,”a’a Mummy,kibari nakusa k’arasawa. kedama kika dawo Yanzu.”

Mummy tace,”ko yanzun nadawo, nagaya miki ni zan k’arasa girkin.dan haka banasun gardama.”

Zainab tace,”to Mummy gani nayi kamar kingaji, amma kiyi hak’uri”.

D’akinta ta tafi ta rage kayan jikin ta tasa marasa nauyi, tafito kai tsaye ta nufi kitchen, ta cikaba da aikin.

kununun aya tahad’a tasanya kayan gyaran shi yayi dad’i sosai, d’akin ta ta koma tad’auko kullin maganin da akabata, tadawo kitchen,kofi tad’auko tazuba kunun ayar sannan tazuba maganin a ciki ta d’an jujjuya Shi sannan ta b’oye sauran da sauri.

Dakin Zainab din ta nufa tace,”Zainab taso kiji.”Zainab Tace,”to mummy.

Tana fad’a Mata ta juya ta koma kitchen d’in.

A kitchen tasame ta tace,” Mummy gani.”

Mummyn ta juyo ta kalleta tana murmushi tace,” Dama kunun Aya ne na had’a naji kamar baiyi dad’i ba,amma kisha kiji dan kinsan ni bancika gane dad’in abunba”.

Mik’o mata kofin tayi tace,”ki sha kiji”.

Karb’a tayi tana maikaiwa abakin ta.

Gabaki d’aya, tashanye Shi, saboda tana tsananin sonshi sosai.

Kofin tamik’a wa Mummy tana cewa,” Mummy k’aramun yayi dad’i sosai”.

Mummy tayi wata irin dariya ta Jin dad’in samun nasara tace,”sarkin kwad’ayin kunun Aya,to bazan k’araba.”

Zainab ta marairaice tace,” Mummy dan Allah ki karaman ko kad’an ne”.

Mummy “tace kije zuwa anjima idan yayi sanyi sai kisha”.

Zainab cikin murnarta to,”to mummy.”

Dak’in su takoma, tunda takama hanyar d’akin su sai ta dunga Jin kamar juwa nad’aukar ta.

Da k’yar takai d’akin su,tana zuwa saman gadon ta ta kwanta,bata jima da kwanciya ba wani bacci mara dad’i yad’auke ta.

Aikuwa Mummy tunda taga Zainab tasha kunun Aya take cikin Jin dad’i dan har Hajiya Safa saida takira tagayama ta, aiko sunji dad’i sosai sukace yanzu sai mujira abunda zai biyo baya.

Zainab tunda ta kwanta ba ita tafarka ba sai yamma,afigice ta mike saboda wani mugun mafarkin da tayi,gaban ta yadinga dukan uku_ uku.

Nabila dake zaune gefen gadon takalle ta tace,” lafiyar ki kuwa?”.

Zainab tace,” lafiya k’alau, mikika gani?”.

Nabila tace,”nagakin wani tashi a har gitse?”.

Zainab ta share zufar data feso Mata tace,”ba komai.”

Tashi tayi tashiga toilet ta watsama jikin ta ruwa tayi alwalla dan tarama sallah la’asar.

Har dare haka takejin jikin ta kamar ba dad’i.

Koda Mummy ta tambaye ta sai tace,” ba komai mummy.”

Mummy bata k’ara cewa komai ba, saboda tasan kafin jikin ta ya warware sai zuwa gobe.

Daddy tun cikin dare yakira Hajiya Sa’a.

ita har tsoro taji data ji kira dai_dai wan’nan lokacin.

Bata ma tsaya duba waya kirata ba, d’auka tayi takara akunnen ta.

Muryarsa da taji ne yasa tace,”Shan wai kaine, lafiya kuwa ka kirani cikin daren nan?”.

Yace Kiyi hak’uri Hajiya,kinsan lokaci ba d’aya ba ne, nace bari nak’ara tuna miki,kinsan karfe tare ne zasu tashi.

“Hajiya Sa’a tace,” ina sane ban man taba, kuma bari kaji idan kadame ni ba inda zataje”Hak’uri yabata yayi mata sallama.

Har zata koma bacci taga hud’u saura dan haka tashi tayi ta d’auro alwalla tafara gabatar da nafiloli har akayi kiran sallah.

Hajiya Ummu da gama sallah asuba taje d’akin Fateema, koda taje saman sallaya tasame ta, tace,”Fateema kitaso muk’arasa kafin Hajiya Sa’a takaraso”.

Fatima tace, “to” tana mai tashi daga saman sallaya.

Hakata cigaba da gyaran ta har Hajiya Sa’a tak’araso, koda tazo har Fateema tayi wanka tayi breakfast tashirya.

Bayan sun gaisa Hajiya Sa’a tace,” tashirya ko, dan saura minti talatin su tashi”.

Hajiya Ummu tace, “komai angama, ke kad’ai muke jira”.

Godiyya Hajiya Sa’a tayi mata, tad’auko kud’i masu yawa taba Hajiya Ummu.

Hajiya ummu ta fara zuba godiya, sannan tayi masu fatan alhairi.

Kiran Fateema tayi, bayan tak’ara fad’a mata wasu abubuwan,sai ta rakasu har wajan motar su, saida taga sun d’aga sannan ta koma cikin gida cike da murnar kyautar da Hajiya Sa’a tayi mata.

Koda suka k’arasa filin jirgi, saura miti biyar jirgin yatashi.

Don mutane har sun farashiga, aikuwa ana kawowa gare ta, gabaki daya jikin ta yafara karkarwa.

Aikuwa sai tafashe da kuka, tana cewa dan Allah ku maida ni wurin Umma na.

Hakuri Hajiya tayi taba ta har suka samu ta shiga jirgin.

Hajiya Sa’a sai da taga tashinsu sannan takira Daddy ta fad’a mashi sun taso.

Muje zuwa

Comment
Nd
Share
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

KAWAR ‘YATA CE

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     🎐 ```G•W•A```🎐

GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼

Story & written
By
Sumy✍�

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

   *Page* 1�6�

Kai tsaye Hajiya Sa’a bata tsaye ko ina ba sai gidan Gwaggo Maryam koda taje a falo tasame ta tana kallon labarun hausa, da sallam tashiga falo.

Amsawa Gwaggo Maryam tayi dauke da murmushi a fuskar ta, tace,” Sa’adatu ce?”

Tace, “Gwaggo nice, daga filin jirgi nake kinsan yau amaryar Munsur zata je wajansa”Gwaggo Maryam tace to yanzo sun tashi ne?”.

“Hajiya Sa’a “tace eh yanzo suka tashi”fatar alhairi Gwaggo Maryam tayi musu, taÆ™ara da cewa, ” Sa’adatu nace wai yabatun amaryar Sulaiman bansa kijin me akeciba”.

Hajiya Sa’a “tace Gwaggo kinsa yanzo komai munkammala, gamida auren nashi lokacin da sukace kawai mukejira” sai Gwaggo Maryam tace” yanzo saura kwana nawa?” Hajiya Sa’a tace sati biyu yarage yanzo har É—aurin aure” gwaggo Maryam tace to itama yarinyar kina kulata kamar yadda kikema Fatima ko?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button