Hausa Novels

Lu’u Lu’u 42

Bismillahir rahamanir rahim_

*42*

 

Wani mahaukacin yadi ne aka mishi babbar riga da yar ciki kalar bleue daya k’ona, bak’ak’en takalmi ya saka da hula bak’a kamar d’inkin da aka ma rigar, haka ma agogon hannunshi ta fata bak’a ce, yayi kyau matuk’a ya kuma gama had’uwa.

Haka ma Haman matsayinshi na babban amininshi ya shirya cikin farin yadi, shi ma tsaf ya fito abun shi gwanin sha’awa, yana mak’ala agogon hannunshi fara k’irar Gucci Umad kuma na fesa turare Rexona mai sanyayyan k’amshi ya kalli Haman kamar mai tuhumarshi yace “Haman, matata ka ke so ko?”

Da wani irin sauri Haman ya kalleshi yana rarako ido kamar zai had’iyeshi da su, tabbas da abinci yake ci da ya sark’e, ganin ya dakata daga d’aura agogon yasa Umad aje turaren hannunshi ya kama hannun Haman d’in ya fara d’aura masa agogon, d’aga idonshi yayi cike da miskilanci da kayar da gaba ya zuba a fuskar Haman da ya gama rud’ewa yace “Na san shirinku kai da yayarka, ta so ka auri matata saboda mijinta ya hak’ura da ita dan ita ma ta samu daraja a gunsa, k’ok’arinta mai kyau ne, saidai niyyar ce mummuna, hakan yasa na muku uzuri kai da ita d’in, komai ya wuce.”

Kanne masa ido d’aya yayi yace” Ka birgeni kai ma, saboda ni da kai duka manufar mu d’aya ce ta tunkarar Zafeera, wato *soyayyar d’an uwa*.”

Yana gama mak’ala masa ya bubbuga kafad’ar Haman d’in sannan yace” Mu je, lokaci ya yi.”

Da kallo ya bi Umad d’in sanda ya juya zai fita, jin bai biyoshi a baya ba yasa ya juyo yana kallonshi, murmushi ya sakar masa yace” Come on! Mu je mana.”

Da k’yar ya d’aga kansa ya jinjina alamar to, jiki a sab’ule ya fara takawa har saida ya kai kusa da Umad, sai kuma ya had’e fuska yana kallonshi yace” Amma dai fatana shi ne a ce babu soyayyarta a zuciyarka, Haman kishinta na ke fiye da yanda ka ke tunani.”

Ya d’aga k’afa zai fita Haman yayi saurin rik’o hannunshi yace “Umad, ba haka ba ne, ka fahimta mana, ni dama ban tab’a jin son ta a zuciyata ba, kawai ina yi ne saboda yar uwata.”

Wani murmushi ya sakar masa marar manufa sannan ya fice a d’akin ba tare da ya sake bi ta kan Haman d’in ba, d’akinshi ya shiga inda aka kwantar da mahaifinshi, kwance yake idonshi a rufe yana bacci har yanzu, tsaye yayi bayan ya rufe k’ofar yana kallon mahaifin na shi, a raunane ya girgiza kai yana tambayar kan shi “Wannan wace irin jarabawa ce?” *Lu’u lu’u*? Kowa ita ya ke son samu, kuma dan duniya kawai, babu mai son ta a yanda take sai dan d’aukakar da zai samu ta dalilinta, yanzu ga son zuciya ya d’ora kowa a muk’amin daya dace da shi, mahaifinshi wanda ya haifeshi yana kwance da ciwon son matar da ya ke aure, bugu da k’ari matar nan ta gama haramta ga mahaifinshi saboda abinda ya shiga tsakaninsu. Ina ma kafin ya musulunta ne lokacin bai samu ak’ida ba, da yana iya jarumatar sadaukarwa mahaifinshi ita, sai ya ga me zai faru bayan haka, amma yanzu ko mutuwa ya yi mahaifinshi ba zai tab’a aurenta ba.

A hankali y k’arasa kusa da shi ya zauna bakin gadon, rik’o hannunshi yayi na dama mai d’auke da zobuna na alfarma biyu ma su d’auke da dutsin gwal d’aya kuma lu’u lu’u, murza hannun ya shiga yi sanyaye kamar zai fashe da kuka y furta “Abba na.”

Yanda yake har yanzu haka yake ba wani canji, dan haka ya sake furta “Abba na…bud’e idonka ka ganni, ni ne Umad d’in ka.”

Duk da bai bud’e idonshi ba amma sai na’urar dake gefen gadon mai daidaita bugun zuciyarshi da numfashin shi ta d’an fara k’ara tin! Tin! Tin.

Da sauri ya kalli na’urar sannan ya sake kallon Wudar da k’wayar idonshi ke motsawa duk da idon rufe suke, alamar yana so ya bud’e idon, sake matsawa Umad yayi daf d shi a sanyaye ya sake cewa “Abba…”

Sannu a hankali sai kuwa ya bud’a idonshi tare da kiran sunan “Umad…”

Cikin wata murya mai gurguri dake nuna jikkatuwa ya yi maganar, da azama Umad ya sake maida hankalinshi akan mahaifinshi ya amsa da “Na’am, ina jin ka Abba na, bud’e ido ka gani ni ne.”

K’ara bud’a idon Wudar yayi ya sauke a kan Umad ya rik’e tafin hannunshi gam wanda ke cikin hannunshi, shi ma Umad taimaka masa ya yi ya sake had’e hannayen na su da kyau, cike da kulawa da buk’atuwa Wudar ya saka idonshi cikin na Umad yace” Zafeera…Zafeera Umad.”

Kamar saukar mari haka ya ji maganar da saida ta sa shi rufe idonshi, daidaita nutsuwarshi yayi a hankali ya bud’e idon ya kalleshi, a sanyaye a kuma ladabce yace” Baa, Ayam tana nan lafiya.”

Cike da damuwa ya nemi tashi zaune yana fad’in” Ka kai ni wajenta Umad, ina so mu yi magana da ita ka ji, ka kai ni wajenta.”

Mayar da shi yayi kwance yace” Shiiiii! Ka nutsu Abba na, za ta zo, Ayam za ta zo.”

Kallonshi yayi cike da gigin tsufa yace” Umad, da gaske wai ka aureta?”

Zuba masa ido yayi na d’an lokaci da tunanin amsar da zai ba shi, nauyayyen numfashi ya sauke har iskan bakinshi na fitowa kafin ya d’aga bakinshi da k’yar yace” E Abba, na aureta.”

Da sauri ya zabura ya tashi zaune yana fad’in” Umad kana da hankali? Baka san cewa ni nake so na aureta ba, yanzu matar ta w…”

Zunbur raba hannayensu tare da mik’ewa da sauri tsaye ya bashi baya, dafe k’ugu yayi yana feso huci daga bakinshi. Fahimta da ya yi kamar ya fara hassalashi kuma ya san waye shi yasa ya marairaice yace” D’ana, yanzu ba za ka saurare ni ba? Ba za ka zauna na fad’a maka damuwata ba?”

Juyowa yayi ya kalleshi ya ma rasa me zai ce masa, ba tare da ya ce komai ba kawai ya juya ya fita a d’akin duk da kuwa yana ci gaba da masa magana, saida ya rufe k’ofar ya kuma sauke wani wawan numfashi sannan ya ja tsaki ya kalli k’ofar d’akin, girgiza kai kawai yayi ya kama gabanshi.

*Filin taron*

A d’an k’ank’anin lokaci filin ya cika da manyan bak’in da dole zaka san bikin na manya ne, jama’a ne ta ko ina ka kalla, kama daga bak’in da aka gayyata, wasu a tsaye suke yayin da hadimai da kuma ma’aikatan da aka d’aukosu dan rabawa bak’i abun sha da abinci suke ta kai da kawowa, wasu kuma na b’angaren da kujerun zama suke suna zaune, duk wanda ka kalla yana cikin shiga ta alfarma, ko dai jinin sarauta ne ko kuma wani babban ma’aikacin gwamnati.

Juman da mahaifiyar Bukhatir da kuma Kossam ne suka fito da Ayam, tana tsakiyarsu cikin doguwar riga kalar ruwan gwal ta tattausan yadi, babban mayafi suka rufe mata kan ta da shi sannan suka saka mata k’ananun abun da suka rik’e mata shi, sannan aka saka mata wani k’aramin kambu a kan ta wanda ya dace da kalar kayanta, sosai fuskarta ta yi kyau ta fito shar shar da ita.

A tsanake suka rakata kan kujerar da aka tanada domin su suka zaunar da ita, daidai lokacin Umad shi ma ya shigo falon, Kossam ce ta masa alama da ya zo, a hankali kuma a gadarance ya shiga takowa saida ya zo ya tsaya, kamashi tayi ya zauna kan kujerar shi ma, kallonsu sukayi suka saki murmushi, Kossam wata yar k’walla ta share tare da fad’in “Kun yi matuk’ar kyau sosai, Allah kareku daga sharrin mutane.”

Da sauri Umad ya d’aga idonshi ya kalleta jin ta ambaci Allah a bakinta, wani murmushin ta kuma sakar masa ta lumshe ido alamar “Kar ka damu.”

Hannu Juman ta kai kan farantinbsilbar dake hannun adimarta ta d’auki farantin silbar mai d’auke da had’in madara da zuma ta kafawa Ayam a bakinta, yatsina fuska tayi ta d’ora bakinta ta d’an kurb’a sai kuma ta janye bakin, zaro mata ido tayi tace” Shanyewa za ki yi.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button