
Har yatada kai alamun zaiyi sara, itakuma Fatima tafarka.
Daddy yana mai cewa, “Fatima bakiji ne ina maki magana kinyi shuru yana kai hannunshi jikin ta.
Afirgice tadawo duniyar tunani da tashiga, aikowa suna haÉ—a ido da Daddy tafashe da kuka, tana mai faÉ—awa jikinsa, tana cewa, Daddy dan Allah kamai dani gida wurin Ummah na.dan ina ji ajikina kamar wani abu zai sameni pls”.
Ta k’ara fashewa da sabon kuka.
Sai datayi mai isarta sannan tayi shuru, Daddy yafara cewa, “Fatima dan kinyi mafarkin wani abu shikenan zaki ce wani abu zai sameki? kenan kin san gaibu?”
Da sauri taÉ—ago kanta takalleshi tanamai girgiza masa kai alamar a’a,.
Numfasawa Yayi yace,”to in har bakisan gaibu ba, kidaina cewa haka kinji”
Fatima tace, “to Daddy”
Daddy yace, “kuma kitashi kiyi addu’a kikoma bacci,da ikon Allah bazakiyi kowane mafarkiba.”
Fatima a tsorace tace, “Daddy bazan iya bacci ba.”
Kama hannunta Yayi ya mik’ar da ita Yana cewa, “to tashi ki je kiyi alwalla kiyi sallah.”
Ba musu ta tashi ta bishi har toilet ya rakata tayi alwalla.
Sallaya ta shimfid’a ta kabbara sallah,
shima Daddy alwallar yayo ya rab’a kusa da ita ya fara sallar, suna masu kai kukansu ga mahalicinsu.
Sai da sukayi sallah asubah saku tashi, ita tafara tashi taje takwan ta Daddy sai da yaga bacci yaÉ—auke ta sannan shima yaje ya kwanta.
Daddy yafara farkawa tashin sa ba jimawa itama tafarka, dasauri tatashi cikin jin kunya tayi toilet.
saida tayi wanka, tafito, inda tabarshi annan tasameshi.
Har zata wuce, kuma ta tsaya nesa dashi, ta na mai duƙawa tace, Daddy ina kwana.
Ido yazuba mata yana mai kallon ta kamar bazai karÉ“a ba, yace, “kintashi lafiya?” tace, “lafiya Æ™alau”.
Bata sake magana ba shima haka, shiri takeson tayi amma takasa, saboda kallon ta da yakeyi, daya fahimce haka tashi yayi yakoma parlour.
DaÉ—i taji dan haka taji daÉ—an shirya wa cikin tsanaki.
Bayan ta kammala shirin ta ta zauna tayi tagumi tana tunanin ‘yan gidan su.
shi kuma Daddy ganin lokaci yaja, dan haka tashi yayi yaje yakirata domin suyi breakfast dan yanasun yafita, dan haka kai tsaye yashiga d’akin a haka Daddy yashigo yasame ta.
Bata masan ya shigo ba sai da taji yace,”fatima lafiyarki Æ™alau kuwa?” tace, ” ba komai Daddy” yace, “yaza kice bakomai, kuma gashi na sameki kina tunani.”
Fatima tace ina son ne nayi waya da gidanmu ne,.”tana magana da kanta k’asa.
Daddy yace,”to naji zan baki waya, amma sai nadawo dan fita zanyi jirana akeyi, dan haka kizo muyi brekafast kinji”.
bamusu ta tashi tabi bayan shi sukaje sukayi breakfast.
Bayan sun kammala agorgoje yaje yashirya ya fito inda yabar ta anan yasame ta yace, “my teema ni zan wuce kiyi hukuri zan barki ke kaÉ—ai.”
Fatima tace, “ba komai Daddy Allah ya kiyaye hanya”.
Wani farin cikine ya ziyarce shi,bai san lokacin da yace,”my teema na nagode kwarai.”
Har yakai Æ™ofa zai fice,juyuwa yayi yace kishirya idan nadawo za mu zagaya gari”.
Ahankali tace, to” bai jime tace ba dan haka yace, “Fatima kobazaki jebane?”
Tace, “Daddy zanje saika dawo koh.” yace, “eh”
Kana yaficewar sa.
Muje zuwa
Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }
🎠```G•W•A```ðŸŽ
GASKIYA DOKIN ƘARFE•ðŸ‡ðŸ¼
Story & written
By
Sumy
BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM
*Page* 1�8�
Da kallo tabishi har yafita, hawaye suka fara zuba a idon ta, ahankali tafurta cewa, “nikuma haka tawa k’addara take,baban Æ™awa ta shine mijina.
Tana tunanin tana kuka Mai ban tausayi.
Sai datayi mai isarta sannan tayi shuru.
Tunani haÉ—uwar ta da Zainab tafarayi.
A watara akashirya debate a makarantarsu government school, ta Æ´an mata da private school, ta Æ´an mata.
Debate d’in daya É—au hankalin mutane da dama musamman malaman su.
Haka akaci gaba da fafatawa a wajan debate d’in, cikin ikon Allah makaran tar gwamnati ta canye, aikowa murna wajan malaman su ba’acewa komai.
Bayan an gama abunda za’ayi an raba kyautunkan da za’a raba, mutane suka fara watsewa, bayan mutane sun watse, akabar malamai da É—aliban dasukayi debate domin suyi metting, babban malamin su ya tashi yayi musu nasiha, yaÆ™ara da cewa,”kada kusama ranku komai, saboda bakuyi nasara ba, a’a kuma kunyi Æ™oÆ™ari sosai, kuma kada kuji haushin su kuÉ—auka haka shine mafi alhairi dan haka kada kusama ranku komai.”
Nunfasawa Yayi Sannan yaci gaba da cewa,” kuma kada kuÉ—auka dan kunfisu Æ™okarine, a’a kuÉ—auka Allah ne yabaku nasara.”
Haka yayi tayi musu nasiha har kowanensu sukaji zukatan su sunyi sanyi.
Bayan yagama bayani kowaninsu ya kama gabansa.
Bayan sun fito daga hall d’in dasukayi debate d’in. tana tsaye tana jiran abokan tafiyar ta, sai ji tayi anayi mata sallama, “Assalamu alaikum ya Fatima.”
Sallamar dataji anmata yasa ta kalli wajan da akemata sallamar.
Amsawa tayi tana mai kallon ta, sai tace mata,”da fatan kin gane ni.”
Fatima tayi murmushi tace, “sosai naganeki ba sunan ki Zainab ba? Ko bakece mukayi debate tare ba?”
Zainab tace, “eh nice,Amma Ina fatan zamu zama Æ™awayen juna.”
Fatima tayi murmushi tace,” miza hana, Allah dai kasama Æ™awancen albarka”.
Zainab tace, “ameen”sai Zainab tasake cewa, ko zan samu number ki?” Sai Fatima tace, “banida waye sai dai nabaki ta Ummatah”.
Sai Zainab tace “zaki iya bani inba damuwa”
Fatima tace, “badamuwa”
Bata number tayi itama Zainab ta rubutama ta tata sukayi sallama suka wuce akan sai sunyi waya.
Tunda ga wannan lokacin zumunci yaÉ—uru tsakaninsu, har suna kawoma junansu ziyara.
Har Zainab tasanya Baban ta ya maida Fatima makaran tarsu.don haka suka Zama makarantarsu d’aya.
Tunda ga wannan lokacin duk, abunda Daddy Zainab zaiyima ta sai yawa Fatima dan yanzu wata kulawa yake ba su yanaji dasu sosai.
Momy har mamakin Daddy takeyi, taga gabaki É—aya, ya É—auki kulawa yaba Zainab da Fatima ba kamar da ba.
Dan Daddy har wajan baban Fatima yaje yace masa,” “yana son yabashi Fatima takoma gidan sa da zama.sannan yak’ara dacewa amma inba damuwa.”
Baban Fatima sai da yayi ajiyar zuciya kana yace, “banki takaba,amma nasan ko ta koma wajan ka dazama to lalle yayana sai yadawo da ita, amma kayi hakuri zan shawarce shi, duk yadda muka yanke zan neme ka”.
Daddy yace, bakomai Baban Fatima.
Sannan ya mik’e tsaye Yana Mai cewa,” ni yanzu zan wuce, sai najika kenan.”
KuÉ—i masu yawa Daddy ya ajema Baban Fatima , yana cewa,” gasu aba yara.”
Baban Fatima yace, “haba Alhaji harda wata É—awainiya”
Daddy yayi murmushi yace, “a’a ko d’aya.”
Godiya Baban su Fatima yayimasa, yana mai rakashi har bakin motarsa kana ya shiga yawuce.shikuma Baban Fatima ya koma cikin gida.
Koda Baban Fatima yafaÉ—ama yayan sa, cewa yayi sam bazai yarda ba.
Dan haka,faÉ—ama Daddy duk yadda sukayi da yayanshi Yayi, sannan yahaÉ—a masa da ban hakuri.
Daddy yace, “bakomai tunda tana zuwa,watarana ma har kwana tanayi,ai ba komai”.
Tundaga wannan lokacin Fatima ita bata koma ba amma kamar ta koma dan idan kaganta agida bazakace ba Momy ta haifeta ba, duk, da ma Momy bason zaman nata takeyiba, dan bada son ranta take zama agidan ba.
Sai dan sanin halin Daddy datayi a yanzun.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya har su Fatima suka kusa kammala makarantar su.