
dan yanzu gaÉ—aya zaman ta yadawo gidan.
Duk da itama badan son ranta take zama gidan ba, sai dan Zainab da Daddy, domin kota koma gidansu, Daddy sai yaje shida Zainab sun É—aukota dan idan batanan ko abincin gidan Daddy baya ci.
Abun na d’aure ma Momy kai dan har saida takai da yimasa magana.
Yace, “mata kawai yanajin su ajikine saboda yaga suna ba karatunsu muhin manci shiyasa yake kara kulawa dasu”.
Momy tace, “to kadai rage, tunda ba su kad’ai ne ba, kuma fah, kada kamanta Zainab ce kaÉ—ai É—iyarka, bada Fatima ba.”
sai Daddy yace, “ni duk, É—aya na É—aukesu”
Momy bata sake magana ba tafita daga É—akinsa zuciyar ta na k’una.
Sai da tafice Daddy yace, nasan kishine bakomai ba inama acekin san me zuciyata ke ciki gami da ita Fatimar, da bansan mizaki kasance ba.
Babban tashin ahankalin Daddy duk bai wuce, ganin Fatima dawani saurayi suna zan ceba, aikuwa Daddy yashiga tashin hankali sosai, dan har sai da yakwanta,ciyo kwana biyu
Bayan yasamu sauk’i yakirata.
Bayan tazo ta gaida shi ya amsa. sai Daddy yace, “Fatima”.
É—ago kanta tayi ta Æ™alleshi,yace, “shekaran jiya, waye yazo wajanki kuna zance dashi?”.
Kasa tayi da kanta, batace komai ba, Daddy yace, “wai ba magana nake maki ba ne?”
konan batace komaiba, Daddy yace, “imma saurayinki ne to ki ajeshi waje daya, dan karatu nakeson kuyi ba soyayyaba, dan haka duk na sake ganinki dawani saurayi sai ranki ya É“aci, dan haka kitashi kitafi kuma ki gayama, Æ´ar uwarki sakona”.
Tashi tayi bata tsaya ko ina ba sai É—akin su.
Acan tasamu Zainab kwance, sannu sannu take tafiya kamar mai koyon tafiya, har ta kawo bakin gado ta zauna.
Zainab tad’ago kai ta kalleta tace, “my sweet sister, lafiya naganki haka, ko ankoma fad’a da hayat ne?”ahankali Fatima tace, “ko d’aya, takara da cewa, Daddy ne yaganmu shikaranjiya yazo fira, shine yanzu yakirani yamin kashedi akan karnasake kulashi, nan dai tagayama Zainab abunda Daddy yace.
Zainba tace, nikam gaskya nayi nisa wajan son Kabir , sai dai nace Allah ya tabbatarmuna da alhairi” dan dawanda keson Zainab da mai son Fatima abukaine dan lokacin da suka zo zance wajan Zainabu a lokacin Hayatudeen yaga Fatima, aikowa shikenan ya likemata saida yaga yasamu shiga a wajan ta.
Dan da farko tak’i saboda ita aganinta basudace ba badan komai ba sai dan shi iyayen sa masu haline ita saÉ“anin haka dan ita mahaifinta sai ya fitane suke samun abin kaiwa baki,
Zainab takara dacewa wai ma zaki tsaya jiran hayat d’inki har yadawo daga wajan karatu, koma naga kamar gidanku bazasu bari kicigaba da karatu ba har dai yadda nake ganin yanayin yayan babanku”.
Fatima tace, “nima haka nake gani,da wuya su barni” sai Zainab tace, “aikuwa da bansan yazamu kasan ceba, dan yanzu naga alamun, kina mutuwar sonshi”.
Sai Fatima tace, “yana iya tunda nayi ta kaucemasa amma yaki barina gashi yanzo abunda nakema godu yafaro dan nama dauka danace masa ba niba Æ´ar gidannan bace yara budani, amma a lokacin ma ya nuna yafisona, gashi yanzo yaddana kejinsa idan narashi bansan yazanyi ba”.
Tausayin ta yakama Zainab sosai dan tasan yadda takeson Hayatudeen dinnan koma koshi yana mutuwar sonta da har gidasu sunsan yana son Fatima dan ko Mamarshi naso Fatima sosai, danshi ma Fatima tak’ara yadda son gasky Hayatudeen kemata.
Kallon Zainab tayi dataga tayi shuru, tace, “my Zeey gobe zanje gida dan Ummah tace, nazo”sai Zainab tace, “to Allah yakaimu sai muje m muyi kwana biyu ko?” Fatima tace eh”.
Aranar haka ta wuni bawani kuzari ajikin tah..
Muje zuwa
Commet
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }
🎠```G•W•A```ðŸŽ
GASKIYA DOKIN ƘARFE•ðŸ‡ðŸ¼
Story & written
By
SumyâœðŸ?
BISMILLAHI
RAHAMANIR
RAHIM
Congrtulations
my
baby intayaki
murnar
kammala
`novel``` *`d'inki
BABUSHI* A ZUCIYATA Allah
yabaki
ladar
faÉ—a karwar
dakikayi
.
Page19*
Da sassafe suka shirya bayan sunyi breakfast, d’akin momy sukaje sukayi mata sallama, kana suka wuce part d’in Daddy domin shi ma suyi masa sallama.
Da sallama suka shiga, bayan ya amsa musu suka gaishe shi, sannan suka fad’amasa inda zasuje,dak’ar yabar su,kuma kwana d’aya yabasu.
Aikowa sunje gidan kwanan su biyu basu dawo ba Daddy da yamma yaje dumin ya É—auko su.
Koda yaje gidan su Fatima ya aika akirasu amma akacemasa basunan suna gidan yayan Baban su Fatima.
Aikawa ya kuma yi yace, “yana so akira mashi su.”
sai kanwar Fatima mai suna Salma tafito, bayan ta gaisheshi tace, mishi,” Ummah tace, na faÉ—a maka, ko dama can Baba babba shine ya aika akirata, dan haka yanzu tana can gidan sa”.
Sai Daddy yace, “kinsan gidan ne?” tace, “eh nasani”.
Sai yace, “zo muje ki kaini gidan.”
Salma tace, “to bari nagayama ummah”.
Daddy yace, “to jeki”.
Batajima dashiga gidanba, ta fito, tace, muje Daddy hanya tamiƙe zatayi tafiya.
Sai yace, “Salma zo kishiga mota muje ko”.
Tace, “Daddy ba nisa nan ne bayan gidan.”
Daddy yace, “duk, da haka kizo muje dan ni daga can nake son na wuce”.
Tace, “to” tana mai dawowa tashiga tana shiga ya tada mota suka tafi tana mai nuna masa hanyar gidan, bakin Æ™ofar gidan yayi parking.
Sunayi parking Salma tace, “ashe Baba babba ma yana gida.”
kallon ta yayi yace, “ina yake ne?”.
Tace, “gashi can bisa tabarma zaune.”
Daddy yace, “to bari naje mu gaisa.”
Salma tace, “to tana mai fitowa acikin motar.
Koda takawo wurin Baba babba, gaisheshi tayi ya amsa.
kallon ta yayi yace, “waye yakawoki a Mota?”.
Salma tace, “Daddy su Aunty Zainab ne yace nakawoshi gidannan”.
Har yaso yasake yin magana yafasa, saboda Daddy daya tunkaro wajan dayake zaune.sai yace mata,”kina iya tafiya.”
Tashi tayi ta shiga gidan,bata k’arasa shigaba Daddy ya k’araso wajan da Baba babba yake zaune.
Sallama Daddy yayi masa yana mai mik’a masa hannu dan su gaisa.
shima hannu yaba Daddy sukayi musabaha, kana yanunama Daddy wurin zama, bayan Daddy yazauna.
Sai Daddy yace, dama nazo na d’auki su Zainab ne akace sunanan”.
Sai da Baba babba ya numfasa kana yace,”eh sunanan ko kiramaka Zainab d’in za’ayi?”.
Sai Daddy yace, eh akiramin su dan gobe ne zasu koma makaranta”.
Sai Baba babba yace, a’a kayi hakuri bada Fatima ba, dan yanzu ko ina bazata koma tafiya ba, saboda data kammala makaranta aure zanyi mata”.
Arazane Daddy yad’ago idonsa ya kalle Baba babba, Daddy yace, “aure”.
Kai Baba babba ya d’aga masa, alamar eh, sai Daddy yace, “dama ammata miji ne?”.
Sai Baba babba yace, “a’a yanzu dai nakeson takawo mijin.”
yakara da cewa, inma bata kawo ba ni zan had’ata da wanda yadace da ita”.
Sai Daddy yace, “da anbarta takawo wanda take so
zaifi”.
Sai Baba babba yace, “intakowa dan kanta inma bata kawo ba ni ina da wanda zanbata”.
Sai Daddy yace, “miyasa bazakubarta tayi karatun taba, inyaso, koda tana cikin karatune idan tasamu wanda takeso, sai ayima ta auren”.
Baba babba yace, “bamuyi tun farko ba, dan haka bazamu fara akanta ba.saidai indai tayi aure mijin ta yabar ta, to wannan kam bazamu hanaba”.
Daddy babu yadda bai nunama Baba babba sai yace, “a’a.”
Jikinsa amace yayi mishi sallama yayi tafiyar sa,dan bai ma tsaya aka kira masa Zainab saboda cikin tashin hankali yake.