KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Daddy nashiga mota yatada bai tsaya ko inaba sai gidan babban abokinsa Alhaji Aminu.

Yana yin picking din motar sa kai tsaye parlour dayasan zai sameshi yaƙarasa.

yana shiga ko ya sameshi, yana kallon news hausa.

Dashigar sa firij yaÉ“uÉ—a ya d’auki ruwa masu sanyi yakifa abakinsa sai da yasha sosai sannan ya aje.

Tunda yashigo Alhaji Aminu yake kallon sa, yana mamaki yanayi da yashiga.

saida yabari yagama shan ruwa, ya kalleshi da kyau yace, Alhaji Mansur, lafiya naganka a haka kuwa?”.

sai da Daddy yayi ajiyar zuciya kana yace, iyayin Fatima aure zasuyi mata” yana faÉ—a kamar yayi kuka.

Sai Alhaji Aminu yace, “to miyasa zaka damu, bayan na gaya maka mafita amma kak’i yarda”.

Sai Daddy yace,” ba nak’i yarda bane, a’a ina dubin yadda zan aure abokiyar É—iyata kuma É—iya a gareni”.

Daddy yakara da cewa wallahi nayi nayi nafiddata araina amma nakasa, kamar ma ina kara cusata ne a zucuya ta”.

Alhaji Aminu yace, “kayi yadda nace ma,dan bari kaji,shi so idan bai shiga zuciya ba ne akecewa abarshi, amma da zaran kabari yashiga to fitar dashi abune mai wahalar gaske, dan haka kaje kanemi magani kafin yayimaka illah”.

Daddy yace, “to naji katayani addu’a, dan na sanar da Gwaggo tace Mani na hak’ura.kuma naje na faÉ—ama yaya tah.

Ni ina ma tsoron karta ce bazata samin hannu ba, tunda kasan yadda mukayi abaya”.

Alhaji Aminu yace, “Insha Allahu komai zaizo da sauÆ™i”.

Alhaji Aminu yakara da cewa,”ina son ka auri yarinyar nan ko dan ka kuÉ“uta daga hannun Hajiya Kulu, kada kaman ta, yanzu kashiga harkar siyasa abu kaÉ—an kayi sai duniya taji ka dan haka kakare mutuncin ka dana iyalinka”.

Sai da Daddy yayi ajiyar zuciya, kana yace, wallahi har da Æ™arin abunnan yasa nakeson nakara aure dan abun nadamuna, yakara dacewa,”insha Allah da komai yadawo dai-dai zanje na gaya ma yayata Hajiya Sa’a.

kai kuma abunda kaÉ—ai nakesu da kai ka tayani addu’a”.

Alhaji Aminu yace, “kada kadamu insha Allah zan tayaka komai, har sai kasamu abinda kakeso”.

Haka sukaci gaba da hira daga baya Daddy yayimasa sallama yayi tafiyar sa.

Bayan sun shirya da Gwaggo Maryam,ya fad’a ma Hajiya Sa’a tace,” yabar komai ahannuta.”

Bayan kwana biyu shiryawa tayi taji gidan su Fatima.

Koda taje akayi rashin sa’a Ummar Fatima batana be Nan ta tafi Unguwa. Kakar ta kaÉ—ai ce agidan.

Da fara’a Kakar Fatima ta tarb’e Hajiya Sa’a, badai kamar data ga yanayin shigar ta.

Bayan sun gaisa, Kakar Fatima tace, “
naso naganeki amma banganeki ba”.

Sai Hajiya Sa’a tayi murmushi tace,”Inna bazaki gane ni ba, dan koni bantaÉ“a zowa gidan nan ba sai yau”.

Sai Kakar Fatima tace,”to lafiya dai ko?”

sai Hajiya Sa’a tace, “lafiya Æ™alau, kodama alfarma nazo nema, akan yariyar da Æ™anena yagani a gidan nan, yace, yanaso”.

Sai Kakar Fatima ta gyara zama tace, “wacece, acikin su, ko ad’auku miki hotonan su dan ‘yan matan suna da yawa”.

Sai Hajiya Sa’a tace, “basai an dauko hoto ba”.

Dan Kaka Amo ta matso taji ko wacece, saboda y’an matan suna da yawa.

Sai Hajiya Sa’a tace, “sunan ta Fatima, dafatan dai ba’ayi mata mijiba”.

Sai Kaka Amo tace, “a’a ba’ayi mata mijiba, duk da dai shi Baban ta yace, zai samar mata miji cikin satin nan, amma tunda kinzo ai shikenan sai ayi daku d’in.”

Sai Hajiya Sa’a tace, “nagode sosai, sai dai shi Æ™anin nawa fah ba saurayi ba ne, yanada mata har ma da yara biyar”.

Sai Kaka Amo tace, “ai albarka akeso bawani zancen saurayi ba, dan haka kamar zuwa gobe sai kidawo.don kiga Shi baban nata da yamma.”

Godiya Hajiya Sa’a tayima Kaka Amo, jikar ta ta É“uÉ—e kuÉ—i masu yawan gaske Hajiya Sa’a ta ajema Kaka Amo, tace, “gasunan, asai goro”.

Aikowa Kaka Amo bakinta kasa rufuwa yayi, É—aukar kuÉ—in nan tayi tanata juyawa, tana cewa, “kunga rabo ko. arziki yazo maka har gida.

kana tamaida kallon ta ga Hajiya Sa’a wadda itama ita take kallo, tace, “gobe kidawo in dai aure ne babu fashi. nice nan kakar yarinya sai yadda nace za’ayi”.

Hajiya Sa’a godiya tak’arayima Kaka Amo kana tayi mata sallama tawuce tace Sai zuwa goben.

Muje zuwa

Comment
Nd
Share
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

 *KAWAR* *'YATA* *CE* 

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     🎐 ```G•W•A```🎐

GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼

Story & written
By
Sumy✍�

Bismillahi rahamanir rahim`

My baby inatayaki murnar fara sabo book dinki mai suna lZZAR SARAUTA Allah yabaki ikon kammala shi lafiya

Page 2�0�

Da yamma Kaka Amo tashirya taje gidan Baba babba, dan a lokacin ne takesa ran dawowar sa gida.

Aikowa tana zuwa ta same shi a gida. Bayan sun gaisa da matar sa, tashi tayi tabasu wuri dan tasan halin lnna Amo sarai.

Fitar ta keda wuya, Baba babba yace, “Inna lafiya kika zo da kanki ai da aikowa kikayi kira na da yafi.”

Inna Amo tace, “a’a magana ce mai muhimmanci, dan shi yasa kaga nazo da kana”.

Yace,”wace magana ce lnna?”.

Tace,” kan maganar minjin Fatima, ko ka tsaida wanda zaka bata ne? ko Kuma ita takawo wanda take so,?”.

Baba Babba Yace,” a’a lnna ko d’aya ba’ayi ba, dan ita wannda tace tana so ma karatu yakeyi, mu kuma bazamu tsaya jiranshi har ya kammala karatunshi tana gida zaune ba.”

Kaka Amo tace, “a’a baza mu jira sa ba kam.

sai kuwa Inna Amo ta gyara zamanta, ta kwashe duk yanda suka yi da Hajiya Sa’a tagaya masa.

Takara da cewa, “kuma daganin ta matar y’ar babban gida ne,dan har kud’i tabani akalla zasu kai dubu dari.

Da karfi Baba Babba yace, “dubu dari fah kika ce lnna? “.

Tace, “sosai kuwa,don shiyasa ma nazo dasu dan kagan su”.

Jikkar dake sanye ajikin ta taÉ“uÉ—e ta É—auko masa kuÉ—in tace,” gasu ka Æ™irga kagani”.

KarÉ“a yayi hannusa na karkarwa yace, “lnna duka tabaki?”.

Tace, “sosai kuwa, kaga abin “arziki har gida ko?”

Inna Amo ta numfasa sannan ta k’ara da cewa,”ni tsoron da nike yarinyar nan kada tayi mana tsiya”.

Da sauri Baba Babba ya É—ago kai ya kalli lnna Amo yace, “lnna bari ma wannan zancen, dan indai naga shi wannan daki kace yayimin to ita Fatimar ko bayyi mata ba baruwana, kuma yadda nace haka za’ayi da ita,ko uwar ta tayi kaÉ—an ta canja abinda nace”.

Numfasawa Yayi sannan yaci gaba da cewa, “badai kince gobe ita Hajiyar zata dawo ba?”.

Inna Amo tace, “tabbas gobe zata dawo.

Sai Baba Babba yace, “zan tsaya na jira ta ma”lnna Amo tace, hakama zaifi kyau,don gaskiya ayi komai a gama”.

Haka sukaci gaba da fira sai da akayi kiran sallah, Baba babba yatashi yaje masallaci, itama Kaka Amo takoma gida.

Koda ta koma Umma dasu Fatima duk sun dawo, amma komai bata ce wa mahaifiyyar fatimar ba.

Koda gari yawaye Kaka Amo tashirya tanajiran zowan Hajjiya Sa’a, kusan sha biyu na rana, sai ga Hajiya Sa’a tashigo da sallamar ta.

Da fara’a Ummar Fatima ta amsa ma ta, aikuwa Kaka Amo da sauri tafito daga d’akin ta, dan har Hajiya Sa’a zata shiga É—akin mamar Fatimar,sai Kaka Amo tafito tana cema, “mamar Fatima bafa wajenki tazo ba,ehe wajena tazo kisani”.

Sai Ummar Fatima tace, “lnna kiyi hakuri naga kar a bar ta a tsaye ne shiyasa nace, ta shigo, kuma bansan wajenki ta zoba dana kai ta wajenki”.

Hajiya Sa’a ita dai kallon ikon Allah take yi.

Inna Amo tace, “Hajiya mutafi can gidan yayan Babanta”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button