KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Hajiya Sa’a tace “to lnna muje”.

Inna Amo tana gaba itako Hajiya Sa’a nabiye da ita har suka kawo gidan Baba babba.

Da shigarsu kai tsaye d’akin Baba Babba lnna Amo takai Hajiya Sa’a.

Da sallama ta shiga, ya amsa mata da fara’a afuskar sa.

wajen zama ya nuna musu suka zauna. Bayan sun zauna ne lnna Amo tace ma Baba Babba,”ga fa Hajiya nan tazo”.

Baki ya washe ya gaishe ta ta amsa.

Baba Babba yace,”ai lnna ta faÉ—a min abunda ke tafe dake.”

Sannan yaci gaba da cewa,” toshi k’anin naki yafaÉ—ama ita Fatimar ne?”

Hajiya Sa’a tace, “nidai yace ya faÉ—a mata amma bansani ba ko da gaske ne? amma zaku iya tambayar ita Fatimar kuji”.

Sai Baba Babba yace, “a’a ai tunda ya gaya mata bakomai, kawai ko aiko da magaba tan ku”.

Abun yaba Hajiya Sa’a mamaki taga babu wani bincike sai kawai aturu.

Numfasawa tayi sannan tace, “to ai bakusan waye mijin ba kuma naji har kunce muturo, kodai yazo ne bansani ba?”.

Baba Babba ya shiga mazurai Saboda Shi kanshi yasan abinda sukayi ba Haka ya Dace ba,don haka Sai cewa yayi,”a’a bai zoba, Amma dai mun san zai zo kafin auren”.

Hajiya sa’a tace, “insha Allah”. Sannan ta kallesu gaba d’aya tace, “amma fa kusani, kar kuce kun bamu kuma daga baya ku ce kun fasa.K’ara ku fad’a mana gaskiya.”

Sai su lnna Amo sukace, ba komai indai tasan Æ™aninta mutumin kirki ne, to babu matsala”.

Hajiya sa’a ta girgiza Kai tace “a’a wannan ba hujja ba ce gaskiya”.

Takara da cewa,” amma, gaskya zan faÉ—a muku,kuma amatsayina na uwa mace gaskya zan iya bashi aure amma fa gamai irin ra’ayina, dan kaga shi ba yaro ne ba, saboda yace min ita Fatima abokiyar diyarsa ce, Zainab”.

Kaka Amo tace,” ai mutunci yafi komai tunda yanada mutunci ai babu matsala”.

Godiya Hajiya Sa’a tayi musu, sannan tayi musu alhairi mai tarin yawa wanda yasa Baba Babba rikice wa, har yanace wa yaushe magabatan sa zasuzo?”

Sai Hajiya sa’a tace, “dana koma gida munyi magana da Baba duk, yadda yace, zan faÉ—a muku”.

Sai Kaka Amo tace, “ba komai ai mun gode, haka suka rakota su nayi mata godiya, har tashiga mota ta wuce, tabar su nan baki yaki rufuwa.

Aikuwa cikin sati d’aya akayi komai amma, babu wanda suka gayama wa.

ko mahaifin ta kayan da aka kawo nasa ka rana suka gwada masa.

Sukace masa ga kaya nan, dan nan da sati uku masu zuwa za’ayi auren Fatima.

komai bai ce musu ba, addu’a yayi mata kana yawuce gida, badan yasan waye ne mijin taba.

Haka akayi ta shirye shiryen bikin Fatima, amma ko ita Fatima har yanzu bata san waye mijin taba.

Dan lokacin da Daddy, yake gaya mata yana son ya aureta bata fahimci mi yake nufi ba, ita dai abinda ta fahimta shine yana son yak’ara aure.

Haka abubuwa sakayi ta tafiya biki yarage saura sati d’aya Daddy yazo ya gaida Baba Babba shi da abokin sa Alhaji Aminu.

Bayan sun gama gaisawa, Alhaji Aminu yaga batar masu da kansu.

Kana yayi musu kyautar, kujerar Hajji da Umura.

Hmm zokaga murna wajen lnna Amo da Baba Babba, dan har makota sai da sukaji Mijin Fatima yabiya musu kujerar hajji.

Koda Ummar Fatima da Baban ta sukaji suka taya su murna.

Amma duk da haka Kaka Amo sai da taje har d’akin mamar Fatima taci mata mutunci, wai tayi bakin ciki, dan bada ita akace za’a ba.

Ita dai Ummar Fatima batace, mata komai ba, har ta gama tayi tafiyar ta.

Ai babu babban tashin hakali daya wuce Zainab, data kira Fatima take Mata,”Fatima Wai da gaske ne Daddy ke zai aura?”.

Fatima tana kwance ta mik’e zumbur ta tashi zaune tace,
“Zainab, wannan wace irin magana ce haka?”

“Daddy fa ki kace? to ko hauka nayi na warke bazan aure Daddy ba, danni uba yake gareni kamar yadda yake uba a wajen ki”.

Zainab tace,” naji to yanzu wanene mijin naki?”.

Sai Fatima tace duk jikinta Yayi sanyi”koni Zainab, bansan waye ba, dan bana bukatar na sani tunda ba shine zab’i na ba”.

Zainaba tace, duk da haka kije kiyi bin ciken waye mijinki”.

Bata bari tayi magana ba, Zainab ta yanke wayar.

Sai da ta gama nazarin maganar Zainab kana ta tashi tayi wajen Ummar ta.

Koda taje a d’aki ta same ta zaune tayi tagumi kamar mai tunani..

Muje zuwa

Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

 *KAWAR* *'YATA* *CE* 

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     🎐 ```G•W•A```🎐

GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼

Story & written
By
Sumy�

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

DEDICATED To
ALL GASKIYA WRITER’S
Aysher Aliyu Humaira (INNARO)💞💞💞💞
Marubuciyar
AISHATUL MUWAFAQA

   *Page* 2�1�

Da sallama tashi ga sai da ta samu wuri ta zauna takalle Umma ta wanda itama ita take kallo.

Tace, “Ummah” kuma sai tayi shuru.

Sai Ummah tace, “Fatima lafiya kowa?”.

“Gayamin mike da munki”.

Sai da tayi k’asa da kanta tace, “Ummah wai wane-ne su Baba Babba, suka tsayar min?”.

Sai da Umman ta kallata tace, “wallahi koni Fatima ban sani ba dan ni ba abunda nasani game da aurenki”.

Ido tad’ago ta kale Umma ta.

Umma tace, mi yasa naga yanzo kin damu keda bavkisa damuwa a ranki ba kuma yanzo naga kina son kisa?

Tace, “Ummah dole nasa, yanzu Zainab takirani take cemin wai da gaske Daddyn su zan aure,da sauri Umma ta É—ago kai ta kalle ta! tace, “shiyasa nake son nasani kuma kinsan ba yarone zan aure ba koda ganin irin kuÉ—in da yake sakar musu”. tana mai fashewa da kuka.

Umma ta saida tayi ajiyar zuciya.

Kana tace, “kidana kuka Fatima ba kuka ne mafita ba, komai lokaci ne dashi kiya hak’uri da duk in da kika samu kanki kikasance mai hak’uri da godema Allah, ina ce kinga yadda sukayi ma Yayarki kuma tayi hak’uri ta zauna dan haka kema kiyi hak’uri”.

Kuma kinga magana ce a keson nayi suci min mutunci dan haka ko inane za’a kaiki kiyi hak’uri dan Allah, nasan kome nene wata rana sai labari dan haka tashi kije ki cema Kakar ku taba ki number ango kina son kuyi magana da shi kin ga tanan zaki san waye ango” tace, “tau Ummah” Ummah tace, “yauwa y’ar albarka tashi kije”.

Tashi tayi ta tafi bata tsaye ko inaba sai É—akin Kaka Amo.

Kwance, tasame ta tana saurarin radiyo sai da tayi sallama da k’arfi! sannan Kaka Amo tasan da shigo war tah.

Tashi tayi da alamun fitina a fuskar tah. Tace, “lafiya kika zomin kamar wata muna fuka, ko sautin tafiyar ki mutum bayaji”.

Sai Fatima tace, “yaza’ayi ko kiji tunda ida kina sau raren radiyo har muÆ™ofta sai sun sani”.

Sai Kaka Amo tace, “ko Uwarki kaji bai dameni ba”.

Ta kuma cewa, “me kika zomin a É—aki ko ajiya kika bani”.

Fatima tace, “ko É—aya, nadai zone kibani numbar wanda zaku aure min ne”.

Sai Kaka Amo tayi mata kallon k’asa da sama kanan tace, “muna fukar banza wadd tayo gadon munafur ci, duk waya dakukeyi nina baki numbar sa ne?”.

Sai Fatima tace, “wace waya na taÉ“ayi dashi! ni wallahi bama san shiba bale nayi waya dashi”.

Ai kuwa wata kuru-ruwa! Kaka Amo tayi tayo cikin Fatima tana nuna ta da yatsa tana huci, tana cewa, “kun jimin muna fukar yarinya salon ace auren dole ne zamu yima alhali keki ka turu su wajan Baban ki?”.

Sai Kaka Amo ta k’ara da cewa, “dan ubanki jiyama bashi ne naga yazo ba har da kaya yakawo muku keda muna fukar uwarki?”.

Tsawa! tadaka mata tace, ko bashi ba ne?”.

Sai Fatima tace, “Kaka kinsan kowa ye yazo jiya, Daddy su Zainab ne fa”.

Kaka Amo tace, ko dai uban kine fa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button