
“Dan haka ba gudu ba jada baya sai kin aureshi”.
Kaka Amo bata kai da rufe bakin ta ba, su kaji ana cewa “ina shigiyar take ita da uwar ta?”.
Wa zasu gani in ba momy ba ita da kawar ta Hajiya Safa .
Da k’arfi! Fatima tace, “Momy lafiya wani abu ya faru ne?”.
Momy tace, “yau sai naci uwarki, niza kici amana ki auremi miji, wallahi kinsha k’arya da ke har muna fukar uwarki?”.
Haniyar da Ummar Fatima da ta jiyo ne yasa ta fitowa daga d’akin ta.
Momy naganin mamar Fatima tafi to daga É—aki ita ko tak’arasa tana nunin ta da yatsa tace, “kece uwar ta to bari kiji da ke har ita ni ba sa’arku bane dan haka tun wuri kujan ye wan-nan zancen aure tsakanin ku da mijin na ko kuyi mamaki na”.
Tana ce musu haka suka juwa suka fita suka bar gida.
Har zasu fita sai ga Hajiya Sa’a zata shigo cikin hanzari.
Kallon-kallo, suka farayi tsakanin su da su momy, amma bawan da yayi ma d’an uwansa magana hakan kowanin su yayi gaba yana ta sake- sake aran sa.
Fitar su keda wuya Fatima ta É—ora hannu akai ta fashe da kuka tana cewa,wallahi bazata aureshi ba sai dai akashe ta”.
Sai Ummah Fatima tace, “Fatima daina kuka, dan bawan da zaiyi miki wanna auren dan wallahi bazan bari ba”.
Aikuwa Kaka Amo da sauri tak’arasa wajan da Ummar Fatima da take nunan ta da d’an yatsa tana cewa, “wallahi bari kiji ko gawar Fatima ce sai ankai ta gidan Alhaji Mansur”.
Suna ciki haka Hajiya Sa’a ta k’araso da sauri tayi wajan su, tana tambayar su meyake faruwa?
Kaka Amo tayi sauri tace, “baki ga wasu mata biyu ba yanzo da zaki gashigo”.
Hajiya Sa’a tace, nagansu, wani abu sukayi muke ne?”.
Sai Kaka Amo tace, “basu yi mana komai ba sun dai yi mana bara zanar kada musake ayi wannan aure”.
Ajiyar zuciya Hajiya Sa’a ta sauke kanan tace, “lnna ku k’yalesu ba a bunda zasuyi ku dai kawai ku cigaba da shirye- shiryen biki”.
Sai Ummar Fatima tace, gaskiya Hajiya bawani shirye -shirye da za’ayi dan y’ata baza tayi wan nan auren ba”.
Aikowa karkusu ku ga yadda Kaka Amo tayi cikin Mamar Fatima tana masifa.
Ita Fatima ba’a bunda takeyi sai kuka dan k’ar Hajiya Sa’a ta shawo kan Kaka Amo tak’yale Ummar Fatima ita ko ta wuce gida.
Aikuwa Baba Babba, nada wowa gida shida Baban Fatima tatashi.
Baban Fatima nadawo wa gida Bayan ya huta sai Ummar Fatima ta fad’a masa duk abunda a ke ciki, yace, “gaskiya wannan abun baiyi ba amma bari naje wajan Yaya muyi magana dashi”.
Sai Ummar Fatima tace, “gaskya katashi kaje kuyi magana”.
tashi yayi yaje wajan Yayan nasa koda yaje ko a can yasame Kaka Amo suna magana da shi.
Bayan yashigo ya zauna ya gaishe su cikin ladabi.
Kowanni su ya amsa ciki-ciki bayan sun amasa sai yace, “Yaya wa nene kuka tsai damma Fatima a ma tsayin miji”.
Ai bai kai da rufe baki ba Kaka Amo tayo cikin sa da masifa.
Tace, to bari kaji wallahi idai ina raye sai Fatima ta aure shi,bari kaji kona mutu wannan auren ba fashi”.
Sai Baban Fatima yace, lnna dan Allah kuyi hak’uri wannan mutum ba tsarar auren ta ba ne, kuma kinga ita d’iyar sa abokiyar ita Fatima ce fa”.
Sai da Kaka Amo tanumfa sa kanan tace, “kai bari kaji kowaye yake awajan ta in dai addini ya yadda Fatima ta aureshi to sai ta aureshi”.
“Tak’ara da cewa, kasan asbar akace za’ayi wannan auren ko to bari kaji ta kai dubanta ga Baba Babba, tace, kaima kanajina” yace, “eh lnna”.
Tace, “kira Alhaji kace, ni Kakar yarin ya nace, gobe za’ayi d’aurin auren shi da Fatima kuma idan ya wuce gobe to nafasa bashi ita”.
Da sauri suka d’ago kai suka kalle ta.
Har zasuyi magana da sauri tada ka musu tsawa! tace, “duk wannda yayi musun wan- nan magana tawa to ban yafema saba, abunda nace kawai nakeson ayi”.
Tana kaiwa nan tatashi tafice tabarsu d’auke da mamaki!.
bayan fitar ta sunjima bawan da ya sake magana.
Sai can Baban Fatima yace, “Yaya kayi yadda lnna tace, nidai ina mata fatar Allah yasa hakashi ne mafi alhairi gare ta”.
Yana kai wa nan yatashi yafice a d’akin.
Ko Baba Babba dake son auren nan yajima yana mamaki lamarin lnnar tasu sai da yagama tunani yadda zaiyi, kana yad’auko wayar sa yakiri Alhaji Mansur ya fad’ama abun da a keciki.
Daddy yace, “bakoma duk da bana ma gari amma zan kir Yayana ya wakil ceni dan ni sai zuwa yamma zan dawo”.
Sai Baba Babba yace, “bakomai amma kafad’a masa kar fe biyu ne za’ayi”.
Daddy yace, “ba komai nagode” kanan sukayi sallam.
Koda Baban Fatima yakoma gida yafad’a musu abinda a keciki Ummar Fatima har da kukan ta, da k’yar Baban Fatima ya la-lashewa ta tayi shuru yace, “kawai muyi hakuri musa mata albarka”.
Ita kam Fatima yadda taga dare haka taga rana, dan cikin dare har da kayan ta tahaÉ—a dumin tabar gari da wannan bakin ciki da abin kunyar da zasu sata har tafi to cikin sanÉ—a har taka wo tsakar gida takama hanyar da zata sada ta da k’ofar fita, ita kuma Kaka Amo tafi to daga toilet, innuwar mutum kawai tagani aikowa tasake butar dake hannuta tana faÉ—in, kufito ga barawo aikowa Baban Fatima da Umman ta da sauri suka fito suna faÉ—in,” lnna nayake?”.
Jikin ta na karkawa tanuna musu hanyar fita waje.
Fitilar dake hannu Baban Fatima ita suka haska a wajan dumin sugani ko za su ganshi aikowa suna haska wa mizasu gani inba Fatima ba jikinta na karkarwa dan itama
Kaka Amo taba ta tsoro.
Fatima suka gani da jikar ta kuma dagani almun fita zatayi.
DaÆ™ar fi Baban ta yace, “Fatima! mi kikeyi anan?”.
Aikowa Kaka Amo najin ance Fatima da hanzari taje k’afafun ta tak’arasa wajan su.
Tana zowa taga Fatima É—auke da jakar ta.
Kaka Amo tace, “nashi ga uku ni Amina to mizan gani haka, ashe shirin da uwarki tashirya miki jiya ko shiyasa naga kuna kus-kus ko tana mai É—ura hannu saman kai tana mai fashewa da kuka.
Aikowa Baban Fatima a fusace yakal-le wajan da Ummar Fatima take.
Yace, “nizakiwa haka duk hak’urin da nabaki ashe bakiyi ba, to bari kiji in har ita Fatima batabar gidan-nan ba to ke yanzo zaki barshi”.
Cikin razana da maganar sa tace, “wallahi Baban Fatima bani nashirya Fatima tatafi ba dan Allah kayi hakuri”.
Tsawa! yadaka mata yace, “wallahi duk bakije ba yanzo zan katse igiyar aurena akanki “.
Bashiri ta É“uÉ—e k’ofa zata fice.
Sai Kaka Amo tace, “a’a babu inda zataje dan yanzu da taje gidan su k’arya da gaskiya zata faÉ—a musu suku ma su yad-da a dinga watsamu a gari”.
Amma tun da karan tse, ta kai duban ta ga Ummar Fatima”ke kifita idan kika kai wuri can da nanu na miki sai kidawo kinga ran tsowar sa ta fice kuma daga inda nace sai kidawo, haka kowa akayi tana fita tadawo.
Baiwar Allah
Kaka Amo tak’ara da cewa kodai bata fice ba idan na tambaye malam sai na san abunyi”.
Ita ko Fatima yana kowo wa wajan datake.
YaÉ—auke ta da wani marin dayasa ta dai na gani nawa ni É—an lokaci, sannan ya wul-lata tsakar gida.
Ya k’ara da cewa, “indai aure ne ba fashi”.
Tofah wannan kakar da rigema take
Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*KAWAR* *'YATA* *CE*
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }
🎠```G•W•A```ðŸŽ
GASKIYA DOKIN ƘARFE•ðŸ‡ðŸ¼
Story & written
By
Sumy�
DEDICATED To…
Maman Ammar💕💕
~Vote & Follow 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~
BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM