
Aikowa tana faÉ—awa jikinsa wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kana yace, “nima haka”.
Fatima kam tunda sukayi mata wannan kallon tayi tsaye kamar wadda aka dasa ta a wajan, tsaye tayi tana kallon su har suka shaga cikin gida, sai da Momy tafaɗa jikin Daddy ne sannan tafarga kunya ta kamata bata san lokacin da taja ƙafafunta zata shige cikin gidan ba.
Motsin da yajine da sauri yajanye Momy daga jikinshi, juyawa yayi dan yaga ko waye, Fatima ya gani sunye da kanta ƙasa.
Kafin yayi magana Momy tace, “sorry k’anwata duk ban lura dakeba” tana mai janyota jikinta.
Daddy yace, “Fatima mike damunki ko duk gajiya ce?”
Murmushi kawai tasakar masa batace komai ba.
Yace, “to kizo muÆ™arasa daga ciki” ya faÉ—i yana mai dubanta.
Momy hannun Fatima tariƙo har suka kawo Babbab falo, Daddy ne yafara zama saman kujera Momy taje takowa masa lemu mesanyi, kallon Fatima yayi yace,
“kinyi tsaye ki zauna ga lemu kisha”
kamar mejin tsoron wani abu sai tace, “a’a Daddy ina son naje na watsa ruwa ne”.
Yace, “ok”.
Key ɗin part ɗinta ya ɗauko yamiƙa mata, karɓa tayi tafara tafiya kamar wanda ƙwai ya fashema aciki.
Tana bada baya suka faki idon Daddy suka antaya mata harara Musamman Zainab dan ita a yanzo wata tsanar Fatima takeji aranta.
Ahankali take hawa step step har takawo cikin parlour, zama tayi saman É—aya daga cikin kujerun parlour tana tunani abunda Zainab tamata nako inkula, sai can tace,
“Æ™ila fushi takeyi dani dan ban faÉ—amata inda najeba, amma kuma ai ba laifinaba ne Hajiyar Mufidace tace kada nagayama kowa acikin su amma bari da safe naje nabata hakuri dan nasan Zeey nada sauÆ™i”
ita É—aya tai maganarta ahaka tasamu natsuwar abunda takeji aranta.
Fatima bata jima da tafiya ba shima Daddy ya tashi yace, “zaije ya watsa ruwa”.
Yana shiga Momy tabi bayanshi, suma yara suka tashi suka tafi mukwancinsu.
Toilet Mommy taje tahaÉ—amasa ruwan wanka sannan tace, ga ruwa na haÉ—amaka kaje kayi yi wanka.
Yace, “to” tashi yayi yaje yayi wanka yafito.
Yana fitowa bayan yashirya Momy takawo masa abincinsa, da kanta tayi serving nasa, “to Alhaji bismillah kafara ci”
har yazauna zai faraci ya tashi yace, “sorry Hajiya bari nakira k’anwarki please”.
Wani baƙin cikine ya tukare mata zuciyar amma komai bata cemasa ba har tafita.
Koda yaje bai sameta parlour ba dan haka ya ƙarasa bedroom ɗinta.
Motsin ruwan da yajine ya tabbatar masa da wanka takeyi dan haka yatsaya jira har tafito.
Bai jima da zama ba tafito, daga ita sai wani ƙaramin toilet iya cinyarta, batama kula da mutum ba dan haka wajan mirrow taje tafara shirinta.
turarukka masu ƙamshin gaske tabi jikin ta dasu, tana gamawa wata rigar bacci ta ɗauku ta sanya wadda da ita da babu duk ɗaya.
kallon da Daddy ke mata baki ɗaya sai ya daskare dan tin fitowarta ya kafeta da ido, so yake yatashi yaƙarasa gareta amma yakasa saboda shika ɗai yasan me yakeji gashi kuma ta sanya wannan rigar wadda tatafi da imaninsa, bashiri yatashi domin yaƙarasa gareta.
Tana cikin saka rigar kawai sai ji tayi anjawota, aikowa bashiri tabuÉ—e baki dan tasaka Æ™ara, da sauri yarufe mata baki yana faÉ—in, “haba Faty na nine fa”.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace, “Daddy yaushe kashigo ban saniba?”.
Bai bata amsaba bakinsa ya haÉ—e danata yafar kissing É—inta kamar ya haÉ—iyeta aikowa itama tafara mayar masa da martani aikowa Daddy gaba É—aya yafita hayyacinshi, yamanta ma inayake ,tsayuwar yaga tanane man tagagaresu dan haka cak yaÉ—auketa sai saman gado, abun na Daddy taga yanane man ya wuce wuri dan haka tafara yimasa magana tace,
“Daddy dan Allah ka Æ™yaleni wallahi agajiye nake inason na huta” yi yayi kamar bai jitaba sai can cikin kasalaliyar murya yace,
“Ko yanzo hutuwa zamuyi, dan Allah kiyi haÆ™uri bajimawa zamuyiba please Teemana”.
Tace, “amma Daddy ba nan ya dace ka kwanaba wajan Momy” baima tsaye saurarin taba yaci gaba da abunda yakeyi mata, bashiri tabada kai.
Momy ko tunda taga Daddy bai dawo ba tafara safa da marwa, dan har zata zo part É—in Fatima ta fasa, ta cika tayi fam jira kwai take safiya tawaye taje wajan bokansu tafaÉ—a mishi Daddy ya dawo.
Kiran Hajiya Shafa tayi tafaÉ—amata duk abunda yafaru tace, ” Æ™yalesu in ya kwana yau ai gobe bazai kwana ba dan haka ki kwantar da hankalinki kinji zuwa gobe da kaina zanje wajan boka nagaya masa abunda ake ciki” sai da taga Momy ta É—an natsu kana sukayi sallama.
Daddy koda yadawo daga duniyar taurari kasa tashi yayi ya koma part ɗinsa, duk da Fatima taso yakoma amma ya ƙyaleta dan haka itama ta ta ƙyaleshi.
Kiran sallah farin suka tashi shida Fatima, tashi yayi ya koma part É—insa wanka yayi ya É—auro alwala yazo yayi raka’atanil fajar sannan yazo part É—in Momy domin yatashe ta amma yaji Æ™ofar akulle dan haka bai tsaye komai ba ya wuci masallaci.
Ita ko Fatima tana gama wanka tazo tayi sallah bayan takammala tajima zaune tana tasbihi kana tatashi ta koma bacci.
Shiko Daddy bai dawo gidaba sai da gari yayi haske kana yashigo gida, kai tsaye part É—insa ya wuce yaje ya kwanta dumin akwai gajiya atare dashi.
Momy ko data farka gari ya waye sosai dan har rana tafara fitowa, tashi tayi taje tayi wanka sannan tazo tayi sallah ta tashi, taɓata lokacin sosai wajan yin kwalliyar, tayi kyau sosai shadda ce ta sanya ash color sannan tafeshe jikin ta da tirare mai ƙamshin gaske, sannan tafito taje part ɗin yara ta tatashesu kana tayo part ɗin Daddy.
Koda taje Daddy baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, tajima zaune kafin Daddy yafarka yana buɗe idonsa wani ƙamshine yaziyar ceshi aikowa baisan lokacin da ya ida tashiba.
Momy tana gani ya tashi taje tahaÉ—a masa ruwan wanka tazo tace, yatashi yaje garuwa can tahaÉ—a masa.
Tashi yayi yaje yayi wanka yafito, koda yafito tafitar masa da shadda kalar tata, sai da tagoge masa jikinsa da ƙaramin towel ɗin dake riƙe a hannusa kana tashafesa da mayuka masu ƙamshin gaske.
Sai data taimaka mashi yasaka kayansa kana suka jero zowa falo domin suyi breakafast.
Koda suka fito gaba É—aya yaransu sunfito falo, suka É—ai sukejira, Kulsum tana gani sun fito tatafi da gudunta tafaÉ—a jikin Daddy tana masa barka da safiya.
Karɓawa yayi yana maiɗagata a sama yana murmushi.
Sai da suka kawo wajan dinning Momy taje masa kujera ya zauna.
Zainab da Nabila da Ummi sukazo suka fara gaidashi, ammasawa yayi ciki da nuna farin ciki, Momy tayi seving É—insa kowani su suka zuba zasu fara ci, sai Daddy yace, ” oh, bari naje nakira Fatima nasan har yanzo bata tashiba”.
Har zaya miÆ™e sai Momy tayi sauri tace, “a’a Alhaji bari Kulsum taje takira ta tunda gasu ba sai kaje ba”.
Bai musa ba ya koma ya zauna.
Yace, “ok kulsum jekikira Auntyn ki Fatima”
aikowa da gudonta tatashi dan taje, koda ta ƙarasa part ɗinta parlour tashiga bata nan dan haka kai tsaye bedroom tashiga.
Gaban mirrow tasameta, Æ™arasuwa tayi wajan ta tana faÉ—in, “Aunty Daddy yace kizo muyi breakfasat”
sai data dubeta da kyau kana tace, “Kulsum bako sallama, bare gaisuwa”.
Murmushi tayi mata tace, “to Aunty kiyi haÆ™uri bazan sake ba please”.
Tace, “to naji jekice ganinan zuwa”
tace, “Aunty karki jima fah”.
Tace, “to Kulsum”.
Kulsum natafiya tashi tayi tasanya tufafinta riga da sikrt na atamfa, tayi kyau sosai dan kayan sun karɓeta, mayafin ta taɗuko tayafa kana takama hanyar sauka ƙasa.