
dan haka ta hak’ura tace inbai zoba da safe taje tagani ko lafiya.
Da haka ta hak’ura taje ta kwanta.
Momy ko tana ganin ya samu bacci takoma part É—inta ciki da farin ciki.
Tana ƙarasawa wayarta ta ɗauka takira Hajiya Shafa.
Ringing da bai wuce uku ba ta É—aga.
bayan sun gaisa Momy ke faÉ—amata abinda yafaru, aikuwa murna awajanta ba’acewa komai, dan har rawa saida ta taka kana tace, “gobe insha Allahu a gidanki za’ayi meeting, dan haka kisa ta haÉ—a mana lunch mai kyau”.
Momy tace, “angama Hajiya tah kada kidamu tunda safe zata tashi ta É—ora”.
Haka nakeso kafin itama tabar gidan taci ubanta,gobe ko wani taga zai auri É—aya daga cikin mazajenmu nasan bazata bashi shawara ba”.
Momy tace, “sosai kuwa, ko Zainab da take goyon bayanta yanzu ko ta daina dan haka sai gobe ma idan kunzo”.
Tace, “ba damuwa sai munzo”.
Sallama sukayi Momy tayi wanka ta koma part É—in Daddy.
Koda gari ya waye da zazzaɓi ta tashi dan ko baccin kirki bata samu ba dan sai gaf da asuba ta samu bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta.
Tana cikin bacci ta mai daÉ—i dan ko sallah asuba bata samuyi ba,cikin barci taji anayi Mata knocking da Æ™arfi kamar za’acire Æ™ofar.
Tashi tayi da addu’a abakin ta, yadda take jin jikin ta kamar ba zata iya tashi ba amma saboda bugun Æ™ofar yayi yawa dan haka tayi Æ™arfin hali ta tashi ta fara tafiya ahankali har takawo Æ™ofar dan har jiri take gani.
A hankali ta murɗa handle ta buɗe ƙofar, Momy ta gani tsaye fuskar ta haɗe, jikinta ne yaɗau karkarwa batasan lokacin da ta furta cewa,
“Momy dan Allah kiyi hakuri wallah yanzu na farka daga barci”.
Sai da Momy tayi mata kallon sama da ƙasa kana ta yatsine fuska sannan tace,
” haÉ—a mana breakfast yanzu, indan kuma kika gama ki maida sanwar Rana saboda muna da baÆ™i yau agidan, Kinji ko bana son asamu matsala don haka tun yanzu kije kifara”.
Cikin muryar masu zazzaÉ“i tace, “to momy bari nayi sallah dan yanzu na tashi”.
Momy tace, “ba ruwana kije can idan kin gama sai kiyi dan mijina yanzu zai fita dan haka kiyi sauri ki haÉ—a mana breakfast kafin ranki ya É“aci”.
Ba musu ta raɓa ta gyafin Momy ta wuce kitchen.
Momy sai da taga ta shiga kitchen kana ta koma É—akin Daddy ta kwanta suka cigaba da barcin su.
Ita ko koda taje kitchen rasa abinda zatayi tayi,duk tunanin ta Yana Kan Daddy,watau jiya gida ya kwana,to amma me ya hana shi zuwa dubata? kodai dan ya kira ne banyi picking ba? Tambayoyi take tayi barkatai acikin zuciyar ta.
Sallah ta farayi kana ta fara haɗa breakfast tanayi tana zama tana hutawa dumin yadda takejin jikinta ba ƙarfi, saida ta kammala sannan ta jera saman dinnig sannan ta wuce part ɗinta. tana zuwa saman gadu ta faɗa saboda yadda jiri ke ɗibarta ko gani batayi sosai dan haka ta kwanta domin ta huta.
Momy ita da Daddy sune basu farkaba sai 10:am, kana sukayi komai atare sannan suka fito domin suyi kalaci.
A falo suka same su Zainab, dan Ummi da Kulsum su sunje school tun safe.
Zainab ce ta fara gaishesu sannan Nabila, zama sukayi sukayi breakfast É—insu cikinsu babu wanda yayi maganar Fatima har shi kansa Daddy haka sukayi breakfast É—insu su kaÉ—ai bayan ya kammala yafita ba tare da ya nemi Fatima ba, dan shi a yanzu gabaki daya ya manta da ita.
Haka momy tayi masa rakiya har wajan motar sa,sai da driver yaje sannan tadawo tasame Su Zainab suka cigaba da firarsu.
Momy ta dubi Zainab tace,”kije kitchen ki duba man ko yariyar can tayi akin dana sata”.
Zainab tace, “to Momy bari na duba”.
Tashi tayi taje kitchen taga bata nan dan haka tazo ta faÉ—ama momy bata kitchen.
Momy tace taje part É—inta tagano ko tana can? tashi tayi ta tafi a hankali take tafiya har takai part É—inta,knocking tayi mata jin ba’ayi magana ba yasa ta tura Æ™ofar ta shiga ciki.
Cikin bargo ta sameta tayi rufa dashi tana makyarkyatar sanyi.
A hankali take takowa har tazo gab da ita, tsawa ta daka mata “tace hala bakiji ana knocking bane kinyi banza da mutane eh? “.
A hankali taÉ—ago kanta ta kalle Zainab tace, “haba Zeey kiyi hakuri wallahi banji ba kuma ko naji ba iya tashi nakeba”.
Zainab tace, “ba ruwana da baki iya tashi dan haka ki tashi kije ki Æ™arasa aikin da aka saki kinji ko”.
Komai batace mata ba dan ko magana bata sonyi, da Zainab taga bata ce komai ba dan haka taje ta gayama Momy wai tace baza tayi ba dan ita ta gaji, aikuwa ba shiri Momy tacema Nabila taje ta gayamata duk ta yadda tasame ta sai tayi dana sanin zuwan ta gidan.
Kafin momy takai ƙarshen zancen tuni Nabila ta fara tafiya.
Tana zowa da Æ™arfi ta buga Æ™ofar ta shiga bako sallama ba komai, yadda Zainab ta barta haka itama tazo ta sameta, da zuwanta bata tsaya komai ba tayaye bargon da ke rufe ajikinta, ido Fatima ta É“ude tace dan Allah Aunty Nabila kuyi hakuri wallahi banda lafiya”.
Aikuwa bata kai da rufe bakinta ba taji saukar mari har guda biyu hago da dama.
Kallon ta Nabila tayi tana huci kana tace, “har kin isa momy tasaki abu ki k’iyinsa? to wallahi bari kiji ko mutuwa zakiyi sai kinyi aikin da aka saki dan haki tun ranki bai b’aci ba kitashi kije ki Æ™arasa”.
Tana riƙe da kuncinta komai bata ce mata ba,tashi tayi tafara bin bango tana tafiya har ta kai bakin ƙofa jiri ya samu ɗibarta har zata faɗi tayi sauri ta riƙe ƙofar.
sai da taji dama-dama kana taci gaba da tafiya har ta Æ™arasa kitchen d’in.
Nabila ko tana ganin ta shiga kitchen taje ta gayama momy ta tashi har ta fara aikin sannan itama momy ta koma part ɗinta dan ta shirya tarbar baƙinta.
Ta jima zaune tana nishi kana tayi ƙarfin hali ta tashi ta kunna gas ta fara haɗa musu abinda sukace.
Tunda ƙamshin girkin da takeyi ya dake hancinta ba shiri zuciyar ta tafara tashi aikuwa tafara ƙoƙarin tayi ammai, amma ta kasa dan ba komai acikinta.
Tajima kafin abun ya saketa dan ta wahala sosai kana ta tashi taci gaba da aikin da suka sata.
Bayan ta kammala girki, tana cikin tsaftace kitchen sai ga Momy tazo tace mata taje ta gyara gida dan baƙin ta na kan hanya. To Fatima tace mata.
Sai da tagama gyaran kitchen kana ta taje ta gyara dukkan gida tanayi tana share hawaye tana tunanin ina Daddy yaje mi tayi masa da ko wayar ta bai kiraba. Haka dai tayi ta magana a zuciyar ta har ta gama ta koma part É—inta.
Wanka tayi da ruwa masu É—umi ko zataji Æ™arfin jikinta haka kuwa ya kasance da taji jikinta ya mata sauÆ™i sosai dan haka ta shafe jikinta da mayuka masu k’amshi kana ta kwanta.
Wayarta ta É—auka tadanna kira Daddy tana ringing amma ba’ayi picking ba, har saida tayi mishi kusan miss call biyar bai É—agaba. wayar ta tayi jefa da ita tana Mai fasa kuka cicin k’arfnta,kukan da takeyi irin kukan Nan ne Mai cin zuciya.
Tana kuka tana faÉ—in, “Allah kabani ikon cin wannan jarabawar daka É—oramin”.
Shiko Daddy koda ta kira bai ma saniba dan baya cikin hayacinsa, dan yau yafaÉ—a kaidin Hajjiya kulu.
dan baijima da zuwa office ba Hajjiya Kulu tazo wajansa taci kwalliya sosai gwanin ban sha’awa gawani Æ™amshi mai sanyaya zuciya tare da sanya nishaÉ—i musamman ga wanda yaji Æ™amshin.
Knocking tayi masa,aka bata damar shiga.
ahankali ta turo Æ™ofar ta shiga, cikin ta kunta mai jan hankalinsa ta Æ™arasa ciki, tun batayi sallama ba k’amshin ta yayi masa sallama,take yaÉ—ago kansa ya kalleta, aikowa wani shu’umin murmushi ta sakar masa wanda yayi sanadiyar kashe masa duk wani Æ™arfi dake jikinsa.