
Idonsa ya kifeta dasu nan take yaga ta koma mishi wata irin kyakyawa, aikuwa bashiri yataso zuwa gareta.
A hankali yake tafiya har yazo wajan da take tsaye kamar wanda aka dasa waje É—aya tana aika masa da shu’umin murmushi mai birkita Æ™waÆ™walwa.
Yana ƙarasowa gareta jikinsa ya sanyata aikuwa tanajin ta jikinsa ta sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfin gaskiya, dan rabonta data jita jikinsa tun lokacin da ya fara neman auren Fatima.
Shiyasa duk duniya yanzu ba abinda ta tsana kamar Fatima, dan taso ya aureta amma yace a’a Fatima yakeso dan haka ita zai aura.
Hajiya kulu ba inda bataje ba dan kada ya auri Fatima amma da yake Allah ya ƙaddara ba wanda ya isa ya hana, dan haka taci alwashi duk yadda zatayi sai taraba shi da Fatimar shi. Ko yanzu atunanin ta abinda akayi mata ne yafara aiki dan haka tayi ƙudurin sai ta rabashi da duk wani wanda ke raɓarsa. Badan komai yasa tasa bokanta yayi mata aiki ba sai dan yazama mallakinta ita kadai.
Tunda taga yanayin da yashiga tafara jin wani sanyin daÉ—i ya rufeta.
Aikuwa tana gani haka ta janye shi daga jikinta cikin murya mai jan hankali da iya bariki tace, “sakeni koda ma nazo ne mu gaisa kawai, kuma gashi natarar aiki kakeyi”.
Cikin muryarsa data fara dushewa yace, “kiyi hakura zan ajiye aikin har kitafi, kibarni mu gaisa please “.
Kamar baza tayi magana ba tace, “a’a bazan tsaya ba sai dai kazo muje gidana”.
Ba musu yace, “muje to”.
Wani farin cikine ya lubeta bata san lokacin da takai masa kiss a lips ba, shiko kamar jira yake yafara mayar mata da martani da ƙyar tasamu ya barta.
ÆŠaya daga cikin ma’aikatan shi kira yace zaifita. adawo lafiya sukayi masa kana suka wuce shida ita.
Tunda suka shiga gidan ta tafara rikitar dashi gabaki É—aya ya manta da kowa bare wata mai suna Fatima.
Dan koda ta kirashi bai masan a ina wayar take ba.
Bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita, dan ko dama har barci akwai acikinta.
12:pm dai-dai motocin group7,suka fara shigowa gida kowanin su cikin shiga ta alfarma suka fara shigowa, inda aka tanadar musu Momy ta nuna musu suka zauna d’aya bayan d’aya suka fara zuwa har suka kai su bakwai.
Ko wacce daga cikin su idan zata shigo sai ta rangwaÉ—a guÉ—a, Hajiya Hafsa ta dubi Momy tace, Hajiya Hadiza naga har Æ™iba kinya fah mi yabaki daga jiya zuwa yau”tana mai sanya dariya.
Saida suka tafa kana tace, “komai ma yabani tunda yanzu sai yadda nace”.
Aikuwa gabaki d’ayansu suka tafa sukayi wa kansu kirari suna faÉ—in, sai mu group7 bamu ba kishiya duk wanda yace zai ja damu yayi k’arya. amma idan zaka iya kazo ka gwada.
Haka dai sukayi tayiwa kansu kirari, daga baya sukaci suka sha har da taka rawa sannan sukace akira musu Fatima su ganta.
Momy Kulsum takira tace taje takira Fatima.
Koda Kulsum taje kwance ta sameta tana bacci dagani ba barcin daÉ—i ne takeyi ba.
Sai data Æ™araso gabanta tafara faÉ—in, “Aunty, Aunty, kitashi Momy na nemanki”.
A firgece ta farka tana faÉ—in, Kulsum ina Momy take?”.
Kulsum tace, “tana parlour tana jiranki”.
Fatima tace, “to je yanzu zanzo”.
Har Kulsum zata tafi sai kuma tadawo tace, “Aunty hala baki da lafiya ne”?
Har taso tace eh kuma tafasa tace, “lafiya ta Æ™alau bacci daine bai ishe niba”.
Kulsum tace, “to Aunty idan kika dawo sai kiyi ta barcin ki”.
Gajiya tayi da maganar kulsum dan haka tace, Kulsum je kice mata gani nan zuwa kinji”.
Aikuwa da gudunta tafice.
Itama Fatima tana ganin tafita tashi tayi da ƙyar ta saka hijab nata kana ta safko, tun bata karasa ba tafara jin hayaniya aikuwa ba shiri gabanta yafara duka uku-uku.
A hankali take tafiya har takawo cikin falon.
Tunda ta tunkaro su suka fara antaya mata harara,nesa dasu ta durÆ™usa tace, “Momy gani”.
saida ta aikamata kallon banza sannan tace, “hala jakar uwarki bata koya miki yadda ake gaida mutane ba? “.
Idon ta tap da hawaye tafara girgiza kai hawaye na zuba a idonta.
Gaishe su ta farayi amma ba wanda ya ƙarɓa mata.
Hajiya Binta cikin tsawa tace, “kitashi kibamu wuri dan ni ko ganinki bana sonyi”.
Jikinta na karkarwa ta miÆ™e zata bar wurin cikin sauri Hajiya Hafsa tace, “ke zonan nagani naga kamar cikine da ita”.
A firgice Momy ta mik’e tsaye tana faÉ—in, “ciki kuma?????”
Sai Hajiya Shafa tace, “ina wadda ko kusantar ta bai ta bayiba ina wani zancen ciki sai dai in wani taje yayi mata amma ba Alhaji ba, dan Malam yace bazai iya kusantar taba har su rabu kunga ko ba wani ciki bakin ciki ne dai zai kasheta”.
Sai a lokacin Momy ta saki wata ajiyar zuciya mai Æ™arfi kana tace, wallah yau dana ci ubanta kuma da yanzu zanje a zubar dashi, dubanta ta kai ga Fatima da jikinta ke karkarwa tace bazaki bar wurin nan ba ko sai na ci ubanki”.
Aikuwa bata bari ta ƙarasa zancen ba ta tashi da gudunta tabar wajan.
Haka dai sukayi ta k’ullawa da warwarewa har dai suka samu mafita sannan kowa cikinsu ta kama gabanta.
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, dan Fatima kullum sai abunda yayi gaba ga ciyo ga wahala gashi rabon da taga Daddy har ta manta.
Kuma ko wayar da take kiransa da ita tunda Nabila ta ganta ta ƙarɓeta shiyasa yanzu kowa batada labarinshi.
Dan shima Daddy yanzu yana kwana biyu bai kwana gida ba, yana can ya tare gidan Hajiya Kulu.
Ita ko Momy ko ajikinta dan yanzu taga ko maganar Fatima ba yayi gaba d’aya ya manta da ita……
By Sumy�
Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
typingâœðŸ?.
ƘAWAR ƳA TA CE
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION.�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}
```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
GASKIYA DOKIN K’ARFE•ðŸ‡ðŸ?
Story & wrtten
By
Sumy�
Dedicated to
KhausarðŸ˜
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.
BISMILLAH
RAHAMANIR
RAHIM
*Page* 3�1�
_📖 Yau ma kamar kullum tana gama sallah asuba ta maga azkar ɗin da takeyi, tashi tayi taje kitchen domin ta fara haɗa musu breakfast.
Tana fitowa falo taga gabaki É—aya ya yamutsa kamar ba jiya da yamma tayi gyara shiba.
Dan haka sai da ta gama gyaran shi sannan ta wuce kitchen ta haÉ—a musu breakfast takai dinning ta jera.
Tana cikin jera abinci saman dinnig, sai ga Daddy ya shigo falon, dan sai yanzu ya dawo daga masallace.
Tunda ya fara shigowa parlour ya kejin wani ƙamshi mai daɗi ya fara ziyar hancinsa.
Ta kunsa ya ƙara domin ya ƙarasa parlour ya zauna ko new ɗin safe ya kalla.
A hankali yake tafiya har ya kawo cikin falon, har zai zama bisa É—ayan kujerun da ke falon, sai idon shi ya kai gareta tana tsaye tana jera abinci saman darning.
Ido ya zuba mata yana kallonta, tunani ya shiga yi ina yasan wannan?har yaso ya tuni nan take zuciyar sa ta fara yi masa zafi sosai, bashiri ya kauda wannan tunanin.
Parlour ma ga baki É—aya yaji bazai iya zama ba, dan haka ya tashi domin ya koma part É—insa ya kwanta koda zai ji damar zuciyar sa dake masa zafi.
Mutsen da taji ne yasa ta É—ago kai ta kalle taga ko Momy ce dan tunda ya shigo bata ma sani ba dan gabaki É—aya ta maida hankalinta ga aikin data keyi.
Aikuwa tana É—ago kanta suka haÉ—a ido dashi gabanta ne ya faÉ—i, dan rabun da ta sanya shi a ido tun lokacin da yace zai kaita gidan su.
Gaba d’ayan su kowane kallon É—an wun sa yake, ita tana mishi kallon, Daddy mena maka,shiko yana yi mata kallon ina ya santa.