KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

A hankali ta buÉ—e baki dan tayi masa magana, har zatayi taji mutsi kamar za ashigo dan haka da sauri ta koma kitchen.

Momy ce ta fito daga part ɗinta, Daddy ta gani tsaye da haka da hanzarinta ta ƙarasu gaban sa tana faɗin.

Alhaji ka dawo ne? Kallon ta yayi fuskar sa É—auke da murmushi yace, “eh yanzu na dawo kuma yanzu nake son nafita dan akwai wani meeting É—in da zamuyi yanzu, dan haka ki haÉ—a min breakfast ki kamin É—akina dan yanzu wanka zan shiga”.

Tace, “to Alhaji”.

Wanjan dinning ta Æ™arasa domin ta had’a masa abinda yace har ta fara haÉ—awa sai ga Fatima ta fito daga kitchen zata koma part É—inta.

Momy ce ta kalleta a ya tsane tace, “kizo ki had’a ma mijina breakfast dan waya nake so nayi dan haka kiyi sauri ki haÉ—a ki kai masa part É—inshi dan haka kiyi sauri bana son shiriri ta”.

Tana gama faÉ—in haka ta wuce zuwa parta É—inta.

T ajima tsaye kafin ta ƙaraso wajan dinnig, ta fara haɗa masa duk abinda tasan yana da buƙata, kana ta ɗauka zuwa part ɗinsa.

A hankali take ta fiya har takai falon sa, kuma shigar ta tayi dai-dai da fitowar sa bedroom É—insa.

ido ya kife ta dasu ya fara tunani ina yasanta? Kayan dake hannu ta ta aje kana tafara taku a hankali har ta kawo gabansa.

Durkusawa tayi hawaye na zuba a idon ta, kana tafar faÉ—in.

“Daddy dan Allah idan wani laifi nama maka dan Allah kaya feni please”. tana mai sanya masa kuka mai cin zuciya.

Shi dai sai kallon ta yake kamar ya santa amma ya kasa ganu ina ya santa, dan haka yace, “ke waya baki damar shigowa part É—ina a matsayiki na yar akin?”.

Kuka data takeyi tada kata kanta É—ago ta kalle shi tace.

“Daddy nice fah Fatima? Duba kagani ba tar aiki ceba”.

Ai bata kai da ƙarasawa ba ya daka mata tsawa mai ban firigi ta wanda tasa jikinta ya fara karkarwa lokaci daya.

Bashiri ta mike tsaya, Hanyar fita ya fara nuna mata dan ko magana baya son yayi mata dan haka da hannu yayi mata nuni da tafita.

Da gudu ta tabar É—akin tana mai zubda hawaye, part É—inta ta wuce ta faÉ—a kan gado tafara sabon kuka mai ciki da kunar zuciya.

Ta jima tana kuka, kukan da take taga ba shine mafita ba dan haka bashiri ta tashi, hijab É—inta ta tasaka tafito.

A hankali take tafiya har ta kawo parlour.

Tayi sa’a kowa babu dan haka cikin sauri tafit harbar gidan.

Tana kawo wa geta mai gida ya gaidata kana ya ɓuɗe mata tafice.

Tana fita ta fara tafiya har ta kawo bakin titi kuma kawo war ta yayi dai-dai da zowan mai adedeta, taran sa tayi sai da ta shiga take faÉ—a masa uguwar da zai kaita.

Kana yaja suka tafi……

   *Sumy*�

Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

typing✍�.

ƘAWAR ƳA TA CE

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION.�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    ```🎐G•W•A🎐```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•🏇ðŸ?

Story & written
By
Summy�

Dedicated to
My daughter🥰
(Zainab)

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.

BISMILLAH RAHAMANR RAHAM

       *Page* 3�2�  

_📖 Tafiya sukeyi basu tsaye ko ina ba sai wata ungowa mai Æ™arancin jama’a.

Bakin wani k’ofar gida tace ya sauke ta,fita tayi ta bashi É—ari biyar, ko canji bata tsaya karÉ“a ba ta Æ™arasa cikin gidan.

Da sallama tashiga gadan, matar gidan ta amsa mata, kana tace ta wuce ta zauna.

Sai da ta zauna kana ta gaishe ta tana cewa, “Fatima yau kece a gidan mu dafan dai lafiya kuke?”.

Fatima sai da tayi k’asa da kanta tace, “Lafiya Æ™alau muke mama, inasu Nafisa?”.

Tace, “duk sunje makaranta”.

Shuru ya biyo baya, sai da Fatima ta nunfasa kana tace, “Mama malam baya nan ne?”.

Sai da ta kalle Fatima tace, “wallahi bai jima da fita ba, amma bari na kira shi in bai yi nisa ba nace mishi gaki kinzo”.

Fatima tace “tau Mama nagode”.

Waya ta É—auko takira shi ta faÉ—a masa ga É—alibar shi Fatima tazo neman sa.

Yace ta jira shi gashi nan zuwa. Mama kallon Fatima tayi ta faÉ—amata yadda yace.

Tace, “tau mama nagode”.

Ba tajima da kiran sa ba sai gashi yazo cikin hanzarin sa.

Da sallama yashiga gidan. Sai da suka amsa kana ya shigo.

A hankali Fatima ta kai duban ta gare shi ido suka haÉ—a, yace, “Subuhanallah, Fatima hala baki da lafiya ne?”.

Aikuwa ba kai da rufe baki ba ta sanya mishi kuka mai tsoma zuciya.

Ido ya kifeta da su, dan ko magana ya kasa.

Mamace tayi ƙarfin halin ta fara rarrashi Fatima da ƙyar tasamu tayi shuru.

Sai da yaga tayi shuru kana yace.”Fatima meke damun ki?”.

A hankali ta fara buÉ—e baki ta faÉ—a masa duk abunda ke damun ta.

Aikuwa tana kai Æ™arshe Mama ta fara salati tana faÉ—in, “duniya ina zaki damu kalli ji har gani”.

Sai da malam ya numfasa kana yace. “Fatima kiyi hak’uri ko wane bawa da inda Allah ke jarbtarsa, dan haka ki kara hak’uri kinji, kuma sai kin tashi tsaye sosai wajan namen tsarin jikinki ki nutso sosai ki dage da addu’a, kuma insha Allahu muma zamu ta yaki kuma duk wanda ya shiga tsakanin ki da mijinki Allah ya fishi, dan Allah baya kwana dan hakk’in wani akan wani kici gaba da rok’on Allah sauki kuma ki nace da rok’on Allah, duk abinda yayi tsanank yana tare da sauki kinji”.

“Badan koma muka baki shawara kiyi wannan auren ba sai dan ki samu ki gama da iyayenki lafiya dan haka kiyi hak’uri, yanzu zan haÉ—a maki magani da zaki affani dasu insha’Allahu lokaci kaÉ—an ko meye zai sake shi amma fah, sakin dage da addu’a”.

Tashi yayi yaje É—akinsa.ya jima kafin yafito, sai da ya zauna, ya kalleta kana yace.

“ga wannan maganin keje ki fara aikin da shi muga abunda Allah zaiyi”.

Man zaitu da habbatus sauda ya fara bata kana yace, “kisan yadda zakiyi ki haÉ—e masa su cikin man da yake shafawa a jikin sa , ki Æ™oÆ™ar ta kada kisa wasa”.

Wani É—aurin magani ya bata yace. wannan ko ki samu lemu ki haÉ—a masa yasha kuma ki tabbatar da yasha kinji”.

Sannan ya koma bata wani yace, ga wannan turare ne sai ki haÉ—a shi da turare mai kamshi sai kirinÆ™a yima gidan hayaÆ™i da shi”.

Kuma kema idan zaki kwanta ki shafe kirjinki da man zantun dan yana kariya sosai”.

Yace,” insha’Allahu idan kin kiyaye abunda nace to komai zai dawo kamar ba’ayi ba”.

Dan haka ki tashi ki koma gidanki Allah yayi miki abarka ya k’ara baki hak’uri, Allah kasa adace kuma idan kena neman Æ™arin bayani sai ki gaya man”.

Godiya tayi masa sosai kana tasoma tashi, sai mama tace Fatima zonan kiji”.

Kallon ta malam yayi yace. “Dan Allah ki barta ta tafi kinga kilama bada izinin shi tazo ba”.

Mama tace, “malam kayi hak’uri ba jimawa zamuyi ba”.

Yace, “to kuyi sauri gani ina jiran ku”.

Tashi Fatima tayi ta same mama a É—aki, wajan zama ta nuna mata ta zauna, kana ta kalleta da kyau tace.

“Fatima ki buÉ—e kunneki da kyau kijini, dan naga ba ainkin sihiri kaÉ—ai ke cin kiba har da tsoro”.

Dan haka, bari kiji koda malam ya baki magani karya wannan sihiri bashi zai sa ya karye ba sai kin cire tsoron su a zuciyar ki. Dan haka kiyiwa mijinki biyayya, in har kina son kema ki zama mace kamar kowa ce a gidan mijin ta. Dan haka Tashi kije malam najiran ki a waje”.

Wani kullin abu ta É—auko ta bata tace, gashi duk lokacin da kika ga abun yayi sauki ga mijinki to kisa madara kisha, duk da naga alamun ba ke kaÉ—ai kike ba, amma zaki iya sha”.

Karɓa tayi tana godiya, dan ita bata san me take nufi da ba ita kaɗai take ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button