
A hankali take tura ƙufar shiga,koda ta ƙarasa Parlour baya nan dan haka ta ƙarasa bedroom ɗinsa.
Kwace ta same sa yayi nisa cikin bacci,a hankali ta ƙarasu har ta kawo wajan da yake kwance.
Kallon sa tayi da kyau,cikin ranta tace ƙila ko sallah Daddy bai yiba.
Dan haka a hakali ta zauna saman gadon da yake kwance.
Tunanin yadda zata tadashi ta fara yi domin yatashi yayi sallah.
Hannuta ta ɗura saman ƙirjin sa tafara shafawa a hankali,a hankali ya fara ware idon sa,itako tana ganin haka duk da a tsorace take tafara sakar masa wani ƙayataccin murmushi.
Ido ya kife ta daso, tunani yafara ina yasan ta?aikuwa lokaci É—aya ya tashi zaune.
Kallon ta yakeyi kamar bai taɓa ganin ta ba.ita ko duk tsoro ya rufeta dan haka tayun ƙura dumin ta tashi.
Cikin hanzari yajawo ta jikin sa yana cewa.
“Zainab ina kikaje na daina ganinki,me namiki kike guduna,wallah da gaske sonki nake yi bazan iya rabuwa dake ba”.
Ajiyar zuciya ta sanya mai sauta kana ta farawa Allah Kirari. kana tace,”Daddy yanzu katashi kayi sallah daga baya mayi magana”.
Tana mai tashi ta bar part É—insa.
Da ido ya bita har taɓa ce ma ganin sa kana ya tashi domin yayi sallah.
Alwala yayi yafice zuwa masallaci.
Ita ko tana ƙarasawa part ɗinta ta faɗa saman gado ta fara kukan.
Dan ita bata san kukan me zatayi ba,amma tayi godiya ga Allah sosai da ya fara karkatu mata da hankalin mijin ta gare ta.
Ƙuma ta ɗau ɗanmar yaƙi da duk wani wand ke son rabata da mijin ta.kuma zata tayi masa biyayya kamar yadda tasan zatawa wanda ta keso idan ta aure shi,dan haka duk wata kunya da tsoro zata ajesu waje ɗaya ta yima mijin ta biyayya kamar yadda ya kama ta.
Dan haka ta shi tayi taje tayi wanka tayi sallah isha’i.
Bayan ta kammala,tashi tayi tayi taje wajan mirro ta fara shefe jikin ta da mayuka masu Æ™amshi,bata tsaya wata kwalliya ba,gown ta atamfa ta saka tayi mata kyau sosai dan haka ta É—an zauna ta idar karatun addu’ao in ta,sai ta sauka Æ™asa.
Shiko Daddy tunda ya fita bai dawo gida ba saida akayi sallah isha’i,kana ya dawo.
Ana gama sallah ko gasai wa da mutane bai tsaya yiba ya fice domin burin shi ya dawo gida ko zai ganta.
Cikin sauri yake tafiya har kawo gida .
Yana ƙarasu wa falo tsaye yayi dan Momy ita da yaran ta yanzu sun dawo nan falo suna fira.
Afra da Affa ne suka zu da gudu wajan Daddy suna faÉ—in,oyoyo “Daddy Aunty Kulsum”.
Hannu sa ya ware suka shiga yana mai jin daÉ—in ganin su.
Zama yayi yana mai dura afra aciyar sa.
Maram ta tasu har wajan da yake ta duƙa ta gaidashi,amsawa yayi yana mai farin cikin ganin su.
Ya tambaye ta gida lafiya tace eh duk lafiya suke.
Fira suka fara yaushe gamo,amma rabin hankalin sa yana kan Fatyn shi.
Har sha biyu saura bai samu tashi yaje wajan ta ba, kuma gashi bacci yaji dan yau ya kwaso gajiya a wajan aiki,dan haka part É—insa ya wuce yaje yayi wanka kana ya kwanta bacci ciki da tunanin ta.
Ita ko tunda taga bai zoba har tasu taje wajan sa kuma ta fasa dan haka tayi shirin kwanciya ta kwanta bacci.
Itama Momy da yaran ta suka tashi wukaje ma kwancin su kana ita ko ta wace part na Daddy.
Ba wani bacci kirki tayi ba dan ƙarfi biyun dare ta farka ta fara na filfili,tana kai kukan ta ga Allah.
Sai da akayi sallah asuba kana tayi sallah ta É—an kwanta.
Shiko Daddy yau koda ya tashi ya makara shiyasa bai samu yaje ya tasu taba.
Amma yana dawowa gida bai tsaya ko inaba sai part É—inta.
Ita koma lokacin ta samu ta kwan ta, a hankali yake tafiya har ya kwao part nata,ko knocking ba tsaya yi ba, key ɗinsa yasa ya buɗe ƙofa ya shiga.
Tundan ya kama hanyar part ɗinta wani ƙamshi turare mai daɗi ya fara ziyar tar sa,uwa uba bare yanzu da ya shigo parlour ta .
Wata sanyayar ajiyar zuciya ya saukar,zama yayi sama ɗaya daga cikin kujerun parlour ,sai da yayi ƴan secnds kana ya tashi ya ƙarasa bedroom nata.
Koda ya Æ™arasa kwance ya same ta, a hankali ya futa cewa,”kardai ace bata yi sallah ba”.
Dan haka da suri ya ƙarasu gare ta,zama yayi ƙusa da ita a hankali ya kai hannusa ga reta,ya fara tashinta.
Da yake bacci nata baiyi nisa sosai ba,dan haka a hakali ta fara buÉ—e idon ta,ta sauke su akan shi.
Yana ga ta buÉ—e ido cikin muryar mai kama da rarrashi yace,”tashi kiyi sallah har angama sallah baki tashi ba”.
A hankali ta buÉ—e baki ta fara magana tace, “nayi sallah yanzu ma na kwanta”.
Yace, “to shine zaki kwan ta baki san ba kyau ba”.
Bata ce da shi komai ba.jin shurun da tayi ne yasa ya Æ™arasu gareta,jikin sa ya sanya ta kana yasuma faÉ—in My teema na, ina kika je na daina ganin ki? kuma kinsan ba zan iya ruwa baki a tari dani ba ko?”.
Koma bata ce masa ba inba hawaye da ke zuba a idon taba,tunda ya fara magana.
Aikuwa gaba ki É—aya ya rikice yafara rarra shin ta,irin yadda taga ya rikice ne yasa ta daina kukan da takeyi.
A hankali ta É—ago ido ta kalle sa kana ta furta cewa,”Daddy da gaske kana sona?”.
Saida ya ƙara matseta ajikin sa kana yace.
“Fatima ko ban faÉ—a ba duk wanda ya kalleni yasan akwai sonki maitarin yawa atari dani”.
Tace,”to Daddy amma inson ka nemi tsarin jikin ka,kuma ka Æ™ara dagewa wajan tsayuwar dare,in har kana son muci gaba da zama cikin kwanciyar hankali,kuma da ka ke faÉ—in ina naje,niba inda naje ina nan dan kona je É—akin ka korata kakeyi shiya na dana dan naga yanzu ga daina sona”.
Bai bari ta kai Æ™arshin zancin ba ya rufe mata baki tare da faÉ—in,dan Allah kada ki faÉ—a haka wallahi ina meki son da baki bazai iya faÉ—a ba,kuma bam masan kin taÉ“a zowa na Æ™ureki ba.amma dan Allah kiyi hakuri kuma kada ki faÉ—ama yaya Sa’a,kuma insha Allah zan Æ™ara neman,anjima ma zanje wajan kawo Gwaggo”.
Tace,”kada kada mu Daddy kowa ma bazan gayama ba bare Hajiya”.
Idonsa yasa cikin nata yana mata kallon da gaske?kai ta girgizamasa alamar eh”.
Yace,”ya akayi naji jikinki da zafi ko baki da lafiya ne?”.
Idonta suka suma kawo ruwa a hankali ta buÉ—e baki tace. “na kwana biyu banda lafiya dan ko aiki da Æ™yar na keyin sa”.
A razane ya furta aiki! to waya saki aiki ne?,to bari kiji ban yadda ki sake É—aukar koda wani tsinke ba da sunan aiki, ni bari ma nakira doctor ya dubamin ke, dan inson naje gida Kowa Gwaggo”.
Tashi yayi domin yaje part É—insa ya d’auko wayar sa.
Har zafita ta kira shi tace, “Daddy ina zuwa” .
tsayowa yayi yana jiran ta,wata kwalbar zuma ce ta ɗauƙo ta ɓuɗe ta zuba a cokali ta fara bashi yana sha sai da ta bashi kosan cokali biyar kana ta aje.
Kallon ta yayi yace,”bata isan ba aÆ™a ramin”.
tace,”a’asai anjima zan Æ™arama Daddy”.
Yace,to abu biyu zaki bani anjima ko?”.
Tace, “meye É—aya?”.
Ido É—aya ya kanne mata.
Kuka taso mayi tana faÉ—in Allah ban yadda ba Daddy”.
Dariya ya sanya yana mai buɗe ƙofa yafita.
By Sumy�
Comment
Nd
Shere
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
*ƘAWAR ƳATA CE* *1441H/2019M.*
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION.�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}
```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
GASKIYA DOKIN K’ARFE•ðŸ‡ðŸ?
Story & Written
By
SUMYâœðŸ?
Dedicated
to..
Family🥰🥰🥰
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad~@
~GaskiyaWritersAss~.
Congratulations Mrs Basakkwace, ina tayaki murnar kammala novel É—ikin me suna Samha,faÉ—a karwa dakikayi akansa Allah yabaki lada,kuskure Allah yaya femiki.kuma ina tayaki murnar fara sabon novel É—inki mai suna WATA KISHIYA BATAYIBA
Allah yasa anfara asa’a