KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Page 3�5�

__📖 Wani kallo Momy ke binta da shi gabiki ɗaya tsoro ya bibiye ta, amma sai ta tuna maganar da matar Malamin su ta faɗa mata, dan haka ta dake zuciyar ta, ta fara ta fiya domin ta koma part nata.

Har zata wuce Momy tayi saurin cin gaban ta,kallon Æ™asa da sama tayi mata kana tace, “ni zakima rashin kunya?kice zaki raÉ“i mijina ko? to bari kiji, ba’ayi wata É—iya mace wadda zata raÉ“ar mijina ta zauna lafiya ba, dan haka sai naga wanda ya É—aure miki Æ™afa da har zaki É—au shegiyar Æ™afar ki kije part É—in mijin har da haÉ—a masa breakfast,kece tsowar munafuka É—iyar matsiya ta”.

sai da tayi mata tas kana ta kyale ta.

Ita ko Fatima ko É—aga kai batayi ta kalle ta ba bare tasa ran zata tanka mata.

sai da tabari tagama zubar ta kana ta raɓe ta gyafinta ta wuce war ta ba tari data kalle Momy ba.

Haka data yi ba ƙaramin ɓata ma Momy rai yayi ba dan haka da hanzari ta bi bayan ta.

Koda Fatima ta ƙarasa parlour duk sun nan zaune suna fira,amma tayi kamar bata ga wata halitta a wajan ba,dan haka ta kama hanyar da zata sada ta sa shen ta .

Aikuwa Nabila naga nin haka cikin É—aga war murya ta daga mata tsawa,tari da faÉ—in, “ke!”

Tafiyar ta taci gaba dayi kamar bata san da ita take ba.

Momy da taga Fatima batada alamun tsayowa, dan haka itama ta daka mata tsawa tari da faÉ—in,”marar mutuncin yarinya hala bakiji ana miki magana ba”.

Sai da Momy tayi magana yasa tayi tsaye cak, batari da ta juyu ta kalle suba,duk da atsora ce take amma tada sosai.

Abunda tayi ya ɓata musu rai sosai,dan haka cikin han zari Nabila ta zo ga banta hannu ta ɗaga dan ta mare ta, ita ko Fatima cikin da dakewar zuciya ta riƙi mata hannu kallon-kallon,suka fara yi tsaka nin su.

Ahankali Fatima ta buÉ—e baki tace,”Nabila me namiki zaki mareni?”.

Iya saÆ™owa Nabila tasaÆ™o dan haka hunnu ta ta fizge domin ta kai mata mari,sai Momy ta É—aga mata hannu tare da cewa, “Nabila bar ni da ita,kishi zatiyi dani,to kijira dan wallahi ko uwarki sai tayi kuka bare ke” Momy na faÉ—in haka tayi Æ™faci ta kama hanyar part É—inta da sauri batari da tace musu komai ba.

Itama Fatima ta raɓa ta gyafin Nabila ta koma part ɗinta.

Momy na shiga É—ikin É—inta wayar ta ta É—auko,kiran number Hajiya Shafa tasa.

ringing da ba wuce biyi ba akayi picking, sai da suka gaisa Momy ta Æ™ara da cewa,Hajiya inaga fah kamar aikin nan ya karya”.

Hajiya Shafa tace, “a’a gaskya aiki na nan,ta Æ™ara da cewa me kika gani da zaki ce haka”.

Momy tace,”komai nagani Hajiya”.

Nan Momy ta shiga faÉ—ama Hajiya Shafa duk abunda ta gani har ma da wanda bata gani ba.

Sai da Hajiya Shafa ta numfasa kana tace,”kada kisa damuwa aranki,kinga jebi sai mukoma mugaya masa abunda ake ciki,dan kinga yau bara nar zuwane wajan saba sai jibi muyi samma ko sai muje wajan sa”.

Momy tace,”to Hajiya zanyi iya hakuri har jibi? dan wallahi ni ka dai nasan me nakeji a zuciya ta”.

Hakuri Hajiya Shafa ta shiga bata, da nuna mata wannan karun É“atar da ita za’ayi babu mai saki ganin ta kuma babu mai saki maganar ta har abada.

Aikuwa Momy ba ƙaramin daɗi tajiba dan haka tasaki jiki suka cigaba da fira har daga baya sukayi sallama.

Parlour tadawo ta sa mesu zaune.

sai da ta zauna Maram ta kalle ta kana tace,”Momy haka kuke fama da yarinya Æ™arama tana muku rashin mutun ci kuma baku É—au mataki ba?”.

sai da Momy ta numfasa kana tace,”Maram yarinyar nan shegiya ce, duk abuda kayi mata sai ta kwance shi,amma nasan wannan karun tayi Æ™aÉ—an ta kunce shi”.

Maram tace,”haka yafi dan na tsane na ganta agidan nan. Momy ni gani nake kamar ciki ne da ita”.

Momy tayi saurin faÉ—in, “a’a Maram bata da komai”.

Tace, “Allah Momy haka nake gani,amma zan sa ido akanta kafin na bar gidan nan”.

Sai Momy tace,”to kisa dan wallahi in shine sai naci ubanta kafin na zubar da shi”.

Haka dai suka cigaba da firar su,Zainab kam ko mai bata ce musuba duk abundan da suke iya kar ta kallon su.

Dan yanzu ta rage jin tsanar Fatima a ranta.

Ita ko tunda ta shiga ɗaki ta faɗa saman gado ta fara kuka mai tada hankalin mai sauraru kamar wadda aka niƙama duka.

Sai da tayi mai isar ta,kana ta tashi taje toilet tayo alwala ta zo ta fara sallar walha.

Bayan ta kammala tajima tana addu’a kafin ta shafa,ta É—auko husunl musulima ta fara karan tawa,har sai da akayi sallah azahar tayi sallah kana ta kwanta bacci.


Daddy ko tunda ya fita daga gida gida Kawo Gwaggo ya fara zuwa,bayan sun gaisa,Daddy ya faÉ—a masa abunda ya kawo shi.

Sai da yayi ma Daddy faɗa mai haɗi da nasiha kana ya haɗa masa magana ya bashi,man habba ya ɗauko ya bashi yace ya tabbatar duk zai kwanta barci ya shefe ƙirjin sa da shi,dan yana kariya sosai koda an jefeka acikin barci da ikon Allah ba abunda zaiyi ta siri akan kai.

Ya Æ™ara dace masa kuma ya dage da azkar safe da yamma insha’Allahu ba abunda zai same shi.

Godiya mai yawa yai masa,kana yayi mishi alhairi sannan ya wuce gidan Gwaggo ya gaisheta kana ya wace office É—insa.

Bai jima da zama office ba doctor ya kirasa yace, “gashi nan zuwa ya kawo saka makon abunda ke damun Fatima”.

Daddy yace, “sai dai kasameni office dan yanzu nafita daga gida”.

Doctor yace, “oky ganinan zuwa”.

Daddy yace, “tom yana mai aje wayar.

Bai sujima da yin wayar ba.doctor ya ƙarasu.

Damar shiga ya bashi sannan ya shigo.

Sai da suka ƙara gaisawa sannan doctor ya fara yiwa Daddy bayani.

Yace, “da farko dai congratulations,ina tayaka murnar matar ka na dauke da cikin wata biyu da sati uku”.

Daddy ba abunda yake faÉ—a sai “Almhdullah”lokaci É—aya farin ciki ya mamaye fuskar sa.

Doctor ya Æ™ara da cewa, kuma abar barin ta tana shiga damuwa saboda haka kan iya haifar da illa sosai ga abunda ke cikin ta”.

Ta kardar magani ya ba Daddy yace, “sai ta rinÆ™a sha insha’Allahu zata samu Æ™arfin jiki,kuma zata daina zazzafin da takeyi akai-akai.

Godiya Daddy yayi masa sosai kana yayi masa alhairi mai tarin yawa.

Shima doctar godiya yawa Daddy kana yayi masa sallama ya wuce.

Tunda doctor yatafi Daddy yasu ya koma gida amma aiki ya riƙi shi,dan ko kiran da Hajiya Kulu kema sa baibi ta kan saba,daga ƙarshe ma da yaga ta dameshi da kira kashe wayar yayi yaci gaba da aikin sa.

Itace bata farka ba sai da akayi sallah la’asar, tashi tayi tayi sallah kana ta sauka Æ™asa domin ta shiga kitchen.

Har ta É—ura sanwa tana cikin yin blending É—in kayam miya,sai ga Nabila ta shigo ita da yayar su Maram.

Ko kallon inda suke batayi ba taci gaba da aikin ta.

Tunda Maram ta shigo takefe Fatima da ido tana su ta gane gaskiyar lamarin.

Itako bata ma kula dasu ba dan aikin ta takeyi.

Tana cikin haka Nabila ta zo har wajan da take tana leƙin me take girka wa.

Kallon ta tamaida ga Fatima kana tace,ke idan kin gama ki haÉ—a mana kun aya dan yau shi muke son shi”.

Kamar bata san da halitta awajan ba haka tayi musu.

Maram ce ta daga mata tsawa tana faÉ—in, “ke bakiji ana miki magana kinyi banza da mutane”.

Sai alokaci ta É—ago ta kalle su,kana tace,”kuyi hakuri ban É—auka dani kuke ba”.

Har Maram zatayi magana Momy ta shigo tace,”wai me kukeyi ne naji kamar hayani ya”.

Nabila ce tagaya mata ƙarya da gaskiyar abunda ya faru.

Momy tace, “ku kyale ta, bana son kuna haÉ—a baki da É—iyar ta lakawar nan,dan haka kuje idan tagama girki dole ta ta kawo kuci”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button