
Duk abunda suka ce ko kallon su bata yiba, bare har su sa ran zata tanka musu.
Suna fita taci gaba da aikin ta,ƙarfi biyar,ta kammala,sai da ta haɗa komai ta koma part ɗinta,wanka tayi kana tazo gaban mirrow ta fara ɗan-ɗasa kwaliya tayi kyau sosai bayan ta shirya ta kashe ɗauri ba shakka tayi kyau sosai,turaruka masu kamshi ta ɗauko ta feshe jikin ta dasu,kana ta ije ta zauna jiran dawo warsa.
Oyoyo, dataji Kulsum nayi yasa tasan Daddy ne ya dawo dan haka,takalma masu tudu ta sanya kana tafara saukowa ƙasa.
Ahankali take tafya har ta kawo setop ɗin ƙar she,lokacin ita ma Momy tafito cikin shirin ta dan ko ita ba laifi tayi kyau.
Yana ƙara suwa parlour da Momy yafara cin karo,sannu da zuwa ta masa kana ta ƙarɓe jikar dake hannusa,yana mai ƙarasuwa cikin parlour.
Su Zainab gaisheshe suka farayi,ya amsa ciki da sakin fuska.
Momy ta dube shi tace,”mu Æ™arasa daga ciki sai ka É—an huta”.
Ba musu yace, to muje”.
part ɗin Fatima ya kalla,aikuwa tsaye ya ganta tana sakar masa murmushi mai ƙara mata kyau.
Alama yayi mata da hannu tazo.
Bamu ta fara tako ahankali har ta ƙarasu wajan da yake.
Durkusawa tayi, tayi masa sannu da zowa.
Amsawa yayi ciki da fara’a afuskar sa, tari da faÉ—in, “ya jikin naki”.
Sai da tayi Æ™asa da kanta kana tace, “Ahmdllh”.
Tashi tayi domin ta koma part É—inta.
Kallon ta yayi yace,”Fatima ki kawomin ruwa na sha”.
Ahankali tace, “to Daddy”.
Wani kallo ne Momy ke aika mata wanda bana ko mai bane sai na tsana.wanda ita ko Fatima bata masan tanayi ba.
Fatima tafiya tayi, ta dauko masa ruwa masu sanyi da lemun kwa-kwa,ta kawo masa,yana zaune a parlour shi shi da Momy.
Ajewa tayi domin ta tayi fiyar ta, amma yace ta zuba masa ya sha.
Ba musu ta zuba masa ta bashi ya karɓa.
Lura da kallon da Momy keje far ta dashi ne yasa ta tashi domin ta koma.
Har ta kai Æ™ofa fita daga parlour Daddy yace,Fatima ina zakije ki tsaye muyi fira mana”.
Tace,”a’a Daddy idan kayi wanka zan dawo”.
Yace,”to yanzu ko zanyi”.
Tana fita Daddy ya kalle Momy yace,”ki haÉ—amin ruwan wanka”.
tashi tayi ta haÉ—a masa ta dawo tace masa ta haÉ—a tashi yayi yaje yayi wanka ya fito.
Sai da ya kammala shirin sa sannan ya fito parlour inda ya bar Momy anan yazo ya sameta.
Zama yayi ta haÉ—a masa abinci ya É—an ci bada yawa ba, tashi yayi yana faÉ—in,”Alhmdullah”.
Momy tace, “ba dai har ka kushi ba yace,na kushi Hajiya,fita ma nakeson nayi dan jira na akeyi”.
Momy tace,”haba Alhaji yaushe ka dawo da har zaka fita”.
Yace,kiyi hakuri ba jimawa zanyi ba”.
Adawo lafiya tayi masa kana yasa kai ya fice.
Da fitar sa part ɗin Fatima ya ƙarasa zaune ya sameta,riƙi da lattafi tana karan tawa.
Sallama yayi yana mai ƙarasuwa gab da ita.
Amsawa tayi ta mai ƙara gaida shi.
Kallon ta yayi yace,”kin ci abinci kowa?”.
Kasa tayi da kanta kana tace,”a’a yanzu zanci”.
Yace,”to zo muje kici sai kasha magani, dan doctor ya kawa maganin ki”.
Rau-rau tayi da ido kana tace,ni fah nawarke Daddy”.
Jikinsa ya jawo ta sai da ya kai bakinsa dai-dai kunne ta kana yace,baki son kije ki gada Ummah da Gwaggo,ko?”.
Kallon sa tayi cikin muryar shagoÉ“a kana tace,”Daddy kai fa kace zaka kaini”tana matsar hawan shagoÉ“a.
Yace,”eh zan kai ki amma saikin ci abinci kin sha magani da”.
Da hanzari ta yunkura zata tashi saman jikin sa sai ya riÆ™ita kana yace,”so kike kiman É“arna ko”. Yana mai lalubar cikin ta.
Bata bi ta kan magar da yayi ba dan burita yanzu taje gida.
Kamar zatayi kuka tace, “Daddy sakeni naje naci sai mutafi”.
Yace, “naji amma kitafi ahankali”.
Tace, “to” dan ta Æ™agar yasake ta.
Tashi tayi taje ta É—auko abinci taci, kana ya bata magani ta sha, sannan yace taje ta canja kaya jikin ta waÉ—an da kejikin ta turare ne dasu,kuma tasan ba kyau saka turare ga macci idan zata fita.
Dan haka taje ta canza ta É—auku faya finta ta fito tasa meshi parlour zaune yana jiranran ta.
Sai da ya kalle shigar yaga tayi mai kana yace,”su tafi”.
Ahankali suke taka setop É—in har suka sauka.
Alokacin Momy na zaune ita da yaran ta Zainab ce kawai bata wajan.
Momy kallan Daddy tayi tace,”aw bakaje ba?na É—auka katafi”.
Yace,”aa yanzu zanje”yana mai takawo dan ya fita.
Momy kallon ta ta maida ga Fatima wada kebin sa a baya kana tace,”ke ina zaki ne?”.
Daddy ya juyu ya kalle Momy yace,”tare zamu fita”….bai tsaya jin me zata ceba suka Æ™ara gaba.
Suna kaiwa wajan da mota take driver ya buÉ—e musu suka shiga kana yaje suka wuce.
Momy ko har suka fita bata sani ba,dan sun barta da baki buÉ—e tana mamaki tare zasu fita…..
#Comment
#Vote
#Share
Sumy ce
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
ƘAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONâœðŸ?
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}
```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
GASKIYA DOKIN ƘARFE�
Story & Written
By
SumyâœðŸ?
Dedicated to..
Gaskiya writers
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
Page 26
_📖 Maram ce tadube Momy tace, ” wallah tun wuri ki ta kama yariyar nan birki dan inba haka ba kinaji kina gani komai na gidan nan zai dawo hannun ta”.
Nabila tace, “kema kya faÉ—a Aunty Momy ko naci zan yima yarinyar nan hukunci sai tace kada nayi amma wallahi wannan karun ko Momy ta hana sai nunci uban ta”.
Ita dai Momy ta kasa cewa komai dan ita kadai tasan me takeji a zuciyar ta.dan haka tashi tayi ta koma É—aki dan surutun su ya nasu ya hai far mata da matsale a zuciya.
Bin Momy da kallo sukayi kana Nabila tace, “Aunty ba zamu zuba ido akan wannan Æ™aramr yariya tayi yadda take so ba a gidan nan”.
Maram tace, “bani kwana biyi kafin natafi zan san abunyi”.
Basuyi nisa da tafiya ba Daddy ya kalle Fatima yace, “ina zamu fara zow gidan su Umma ko gidan Gwaggo?”.
Ahankali taÉ—ago kai ta kalle sa kana tace,”gidan Gwaggo zamu fara kaga ban taÉ“a zowa na gaishe taba”.
Sai da yaja hancin ta kana yace, “duk yadda kikace haka za’ayi” yana faÉ—a yana murmushi.
Driver Daddy ya faÉ—ama wurin da zai kai su.
Basu tsaya ko ina ba sai gidan Gwaggo.Daddy ya fara fita daga motar kana ya buÉ—e mata ta fito.
Hannusa ya sakala anata kana yace, “muje ko”.
Kallon sa tayi tare da saka masa kukan shagwaÉ“a kana tace, “Daddy sake min hannu kaga shiga zamuyi kuma ni kunya zanji idan muka shiga ahaka”.
Yace, “meye na kunya tunda mijinki ne ba kowa ba”.
Tace, “eh Daddy duk da haka kayi hakuri har mu fito”.
Yace, “to naji”…yana mai sakin hannun ta.
Ahankali suke tafiya har suka ƙarasu paulour Daddy na gaba tana biye.
Sallama sukayi ma Gwaggo.
Amsawa tayi tana mai tashi daga shingi É—in da take.
Yana shigowa Fatima ta shigo,aikuwa Gwaggo naganin Fatima ta fara murina tana faÉ—in,
“Yau baki ne damu agida? sanunku da zowa”.
Cikin na tsowa Fatima ta ƙarasu wajan da Gwaggo take ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da Gwaggo cikin mutunci.
Amsawa Gwaggo tayi tana mai faÉ—in ya gidan duk lafiya kuke?”.
Sai da tayi Æ™asa da kan ta kana tace, ” “lafiya Æ™alau muke Gwaggo”.
Bayan sun gama gaisawa Gwaggo ta dube shi tace, “Mansur kaje su Sa’adatu sun dawo kowa?”.
Da kamar mamaki ya É—ago kai ya dube ta kana yace, “yaushe suka dawo Gwaggo ?”.
Tace, “to baka ma sani ba ai na É—auka daga can kuka fito ashe baka masani ba,dan haka ku tashi tun yanzu kuje duk Æ´an uwa nata zuwa yi mata sannu dan haka ko tashi kuje can kuma kace ina gaishe ta da jikin mijin nata”.