KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Glove É—in da ta kashe ya kunne Æ™arasuwa yayi saman gadon ya kwanta tare da kashe glove kana jawu ta jikin sa yana faÉ—in, “ba dai kinyi bacci ba”.

Komai bata ce masa ba tashi tayi ta ɗauko man habba ta zaba hannuta ta zo wajan sa ta fara shafa masa aƙirji.

To daga shafa man wasa ta sauya Dan Daddy ya Nuna mata yayi missing ďinta over.

Dan haka ba ƙaramar wuya ta sha ba awajan Daddy dan da ƙyar ta samu ya ƙyaleta amma ba dan ya gaji ba.

Tashi tayi tayi wanka dan bata sun kwana da janaba ajiki dan yana ba sheÉ—an damar shiga jikin ka domin ya cutar da kai.

Shiya sa ake sun mutum ko bai samu yayi wanka ba to yayi alwala idan yana tare da janaba kafin ya kwan ta barci.

Tana cikin wanka Daddy ya zo sukayi wanka tare.

Bayan sun kammala suka yi shirin bacci suka kwan ta.

Basu jima da kwanciya ba barci ma daÉ—i yayi awun gaba da su.

Ƙiran sallah farin ne ya tashe su da ita har Daddy.

Alwala sukay kana suka zo suka tada sallah na fila can daga baya Daddy ya tashi domin zuwa masallace.

Yana fita part É—in Momy yaje ya tashe ta kana ya wuce masallaci.

Tana gama sallah bayan ta gama azkar tayi kartun Æ™ur’ani tashi tayi taje kitchen agurgoje ta haÉ—a mishi breakfast tana kammala wa ta dawo part É—inta tayi wanka ta É—an-É—asa kwaliya ta sauÆ™o Æ™asa ta É—au breakfast ta je part É—insa ta zauna tana jiran dawo war sa.

Bata jima da zama ba Daddy ya dawo, dan yau so yake yafi ta da wuri dan yana da metting a office.

Kai tsaye part É—insa yaje domin yayi wanka.

Ƴana shiga yafar jin kamshin turare me daɗin shaƙa,zaune yagan ta riki da littafin husunil musulin tana karan tawa.

Sai da yayi sallam ta san ya shigo.

Kanta ta dako tari da sakar masa murmushi me Æ™ara mata kyau kana ta zo gare shi ahankali take tako har ta Æ™arasu jikin sa ta faÉ—a kana tace,”My Daddy nah antashi lafiya?”.

Sai da ya sauke ajiyar zuciya kana yaÆ™ara matse ta ajikin sa sannan yace,”lafiya Æ™alau,kema in fatar haka”.

Kanta ta girgi za masa alamun “eh”.

Ruwan waka yace ta haɗa masa saboda sauri yake dan metting ne da shi ƙarfi ta 8:.

Bari jikin sa tayi taje toilet ta haÉ—a masa ruwan wanka kana tafito.

Har zai shiga yace, “dear nah ba zaki tai makamin nayi wankan ba?”.

Kallon sa tayi a É—an marai ce kana tace, “a’a Daddy sauri kakiyi kaje kayi niko nafitar da kayan sa warka.

Ba musu yace, “to” tare da shiga toilet dan ya fara wanka.

Koda yafito tagama fitar masa da kayan sawar sa.

Taima kamasa tayi ya shirya ya fito domin yin breakfast .

sai da ta cika masa cikin sa kana itama yaci kama ta nata kana ya tashi domin ya tafi .

Jikarsa ta ɗauka domin ta rakashi,koda suka ƙarasa paulour lokacin ita ko Momy zata fito domin taje part ɗin sa.

Kallan- kallon saka farayi tsakanin su duk mugun kallon da Momy ke aikama Fatima yau bai sa taji tsoron ta a zuciyar taba dan haka tayi kamar bata san tanayi ba.

Sai da Momy ta gaishe da Daddy kana itama Fatima ta gaishe ta.

A ya tsane ta karÉ“a gaisuwar kana Momy taÆ™ara da cewa, “ba dai har zaka fitaba?”.

Yace, “yanzu zan fita saboda metting garemu yanzu”

yana mai takawa dan ya fita saida sukayi mishi rakiya har sai da motar shi ta É—aga suka dawo ciki.

Duk kallon da Momy kema Fatima baisa yau taji tsoron ta ba dan haka kai tsaye part É—inta ta koma ta kwanta da bacci ba wani isar ta yayi ba.

Momy ko tana ganin yara duk sun tafi school bata tsaya koma ba ta yafa mayafin ta ta fita domin zuwa wanjan bokan su.

Dan ko gayama Maram bata yi tafiba,dan sauri take taje ta dawo.

Direba ta kira ta gaya mishi ida zai kai ta mota ya ja yakan ta gidan Hajiya Shafa.

Suna zowa ita ma Hajiya Shafa ta gama shirin ta dan haka taje mota suka tafi.

Koda suka je suka faÉ—a masa aikin ya karya shi kansa yayi mamaki sosai dan haka yace, “kada su damu komai zai dawo dai-dai dan wannan aikin mai tsaneni za’ayi”.

Godiya sukay mishi kana suka zuba mishi kuÉ—i masu tarin yawa,sukafice tare da zomar cewa su zuba idao suga me zai faro.

Tana cikin barci taje anta sallama dan haka ta tashi ta zo tagani wake sallama.

bakin part É—inta suke,aikuwa tana ganin su ta sakar musu murmushi tari da faÉ—i,”Aunty Maryam da Aunty Amina kone tafe?”.

Wato kishiyar Hajiya Shafa da Hajiya Binta.

Tace, “sannuku da zowa ku Æ™arasu ciki dan Allah”.

Ƙarasuwa sukayi suka zauna kana taje ta kawo musu kayan motsa baki ita ma ta zauna tace,ashe zaku zo?”.

Sai Maryam tace, “to mu irinki muke da bata sun shiga cikin mutane”.

Murmushi Fatima tayi kana tace,”wllahi Aunty ba haka ba kawai yanzu bana jin daÉ—in jiki nane?”.

Sai Amina tace, “aike Fatima kin more kina samu yana kulaki tunda gashi har rabu ya kuka,amma gamu muda babu duk É—aya dan nibada Hajiya Sa’a ba da tafiya ta zanyi wannan wahala har ina kai ne kome gaka ka koma kamar Æ´ar aikin gida”.

Sai da suka gama nasu kana Fatima tabasu labarin inda ta fito kuma tace suje wajan malamin isilamiyar su da ikon Allah zai basu taimako ko meye zai kwanci.

Godiya sukayi mata sosai kana ta basu number wayar sa.

Sai da suka yi fira sosai kana sukayi mata sallama akan sai sunyi waya.

Har suka fito Momy bata dawo ba.

Maryam ta dube Fatima tace,”Hajiyar ki da tawa yau fah tun safe suka fita gashi har yanzu basu dawo ba”.

Fatima tace,”ni bamma san bata gidan ba”.

Sai Amina tace,”Maryam zo muje firan ba zata Æ™araba gwara muje wurin malamin kafin wani lokaci mu koma gida”.

Sallama sukayi ma Fatima suka fice.

Ita ko bata koma É—aki ba kai tsaye kitchen ta wuce.

Bata jima da shaga kitchen ba taji hayani ya dan haka tasan da Æ´an boko sun dawo suda Momy.

Sai da ta kammala aikin ta ta fito.

Tana fitowa part É—in Daddy takama hanyar zuwa dan ta gyara shi, yi tayi kamar bata ga kowa a paulour ba.

Tafiya take bata masan da damai zuwa ba jitayi sunyi kara da wani abu kuma kafin ta ankara an wanke ta da kykyawan mare.

A razane ta É—ako kai ta kalle waya mare ta.

Nabila tagani dan haka itama cikin zafin nama ta wanke ta da mari har biyu tana huci kamar kumur cin macije.

Nabila ita ma hannu ta ɗauka dan ta ƙara kai ma Fatima mari amma sai Fatima ta riƙi hannu ta kana ta fara faɗin,

Haba Nabila da hankalinki da tunanin ki zaki É—au hannu ki ki mare matar ubanki?”tare da sakir mata wani murmushi me biÆ™ita Æ™waÆ™waliwa.

Aikuwa tana cewa haka ba Nabila ba har Momy da ke wuri zaune tana kallon su sai da ta miÆ™e tsaye har su Maram da Zainab Kalaon-kallon suka farayi tsakanin su….

#Vote
*Comment
Shere

Sumy M Na’ige ce✍ðŸ?
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

KAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍�
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}

 ```🎐G•W•A🎐```

GASKIYA DOKIN ƘARFE�

Story & Written
By
SUMY M NA’IGE✍ðŸ?

Didicated to..
Gaskiya writers

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

*Page* *38*

_📖 Ƙarasuwa sukayi har suka kawo wajan da suke.

Momy ce tayi magana ciki da É—aga murya.

Tace, “sannu matar uban su bari yanzu nasa ta mare ki sai naga uban da zai rama miki kuma wallah ki-kiya yeni kinji ko”.

Kallon Maram Momy tayi tace, “rama ma Æ´ar uwarki marin da tayi mata naga meza tayi”.

Cikin hanzari Maram ta É—au hannu zata kai ma Fatima mari taji an daka mata tsawa mai ban firgi ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button