KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Komai bata ce masa ba,dan haka da sauri yaje yakira Doctor.

Tare suka shigo Dactor ya cire mata ƙarin ruwan kana ya fara duba ta.

Sai da ya duba ta sosai sa’anan ya ruÉ“uta mata magani kana ya rubuta musu ta kardar sallama.

Sai da Daddy yasai magani kana suka shaga mota driver yaja suka wuci gida.

Sunayi parking Daddy da hannuta ya riƙo saboda jirin da bai gama sakin ta ba.

Ahankali suke tafiya har suka ƙarasu paulour dai-dai lokacin da Zainab ta fito a ɗakin su.

Da sauri ta Æ™arasu garesu tana faÉ—in,”Daddy ya jikin ta?”.

Yace, “da sauki Zainab”yana mai Æ™arasawa da ita part É—in ta.

Zainab taje ta gayawa Momy sun dawo.

Sai da tayi mata wani kallo kana tace, “to meya dameni aciki da dawo warsu da rashin da wowar su da zaki zo ki gaya min eh?”.

Tace, “Mumy kiyi hak’ur idan nayi laifi” tana mai ficewa daga É—akin.

Sai da Zainab tajima da fita Momy tashi tayi ta fito bata tsaya ko ina ba sai part É—in Fatima.

Koda ta shiga bata same su paulour ba dan haka kai tsaye ta wuce bedroom É—in ta.

Sai da ta shiga tayi sallam gaban ta ne ya faÉ—i irin yadda taga Daddy rungume da Fatima lokaci É—aya fuskar ta ta sauya amma sai ta wayin ce tayi kamar abun bai dame ta ba.

Bayan Daddy ya amsa sallama ta ƙarasa gabansu tana faɗin,

“Ashe kun dawo gashi har na shirya nasa drivir ya kaini sai Zainab ke cemin kun dawo”..tana magana tana ya mutsar fuska kamar da gaske.

Daddy yace, “koda ma aman ne ya wahal da ita amma yanzu da sauki”.

Tace, “masha’Allah,Allah ya Æ™ara sauÆ™i,taÆ™ara da cewa to Daddy su zainab meke damun ta?”.

Yace, “ba komai bane sai matsalar ciki ce”.

Ganban momy ne yayi mum-munar faÉ—uwa amma ta dage tace,

Tace, “kamar ya?ko ciki ne da ita?” ta faÉ—i haka muryar ta na rawa amma sai ka natsu za ka gane haka.

Cikin rashin damuwa Daddy yace, “ciki ne da ita har na tsawon wata uku”.

Gaban mumy ne yayi dummmmm amma da yake Æ´ar duniya ce tace, “amma shine baka gaya mun nasamu Æ™aruwa ba sai yanzu ” tafaÉ—a aÉ—an shagwaÉ“an ce.

Hakuri Daddy ya bata da ƙyar ta hakura kana tace, bari taje ta haɗa ma Fatima koda tea ne ta sha.

Godiya Daddy yayi mata kana ta fice.

Da ƙyar ta ƙarasa part ɗin ta dan gabaki ɗaya tafiya gagarar ta tayi.

Tana isa ciki da ta shin hankali ta É—au waya takira É—iyar ta Maram ta faÉ—a mata abunda ke faruwa.

Sai da tagama faÉ—a mata kana tace, “amma yanzu zan haÉ—a mata tea sai na zuba wani magani wanda ko cikin ya zube baza a gane meyesa cikin zubewa ba.

Maram tace, “haka yayi Momy kiyi sauri kiyi”.

Suna yin sallama bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ruwan tea ta haÉ—a da madara kana ta É—auko wani magani ta zuba a ciki sai da ta juya shi sosai ya haÉ—e da madara kana ta É—auko ta kawo musu.

Sallama tayi kana ta shigo ko yanzu yadda ta barsu haka ta same su.

Ƙarasuwa tayi gaban su tace, “gashi ta tashi tasha sai ta sha magani zata ji daÉ—in jikin ta.

KarÉ“a Daddy yayi tare da yima Mumy godiya yace, “Fatima tashi ki sha”.

Ba musu ta tashi dan koda ma yunwa take ji kofin yami Æ™a mata ta Æ™arÉ“a yace, “ta sha”.

Kofin ta É—auka zata kai bakin ta tare da faÉ—in bismillah….

#Vote
Cmment
Shere

Sumy M Na’ige🌸
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

ƘAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍�
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}

 ```🎐G•W•A🎐```

GASKIYA DOKIN ƘARFE�

Story & Written
By
SUMMY M NA’IGE✍ðŸ?

Didicated to..
My Shemah🥰

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

Page 42

_📖 Har ta kai bakin ta sai taji ƙarnin madarar ya dake hancin ta aikuwa lokaci ɗaya ta fara kakarin amai.

Amayar da wanda ta kurɓa tayi tare da aje kofin dan jin take zuciyar ta na tashi sosai.

Shi ko Daddy duk rikicewa yayi yana ta faÉ—in,

“Sannu ,meke damunki Fatima?”.

Ita ko Mumy ranta ne ya ɓaci sosai gani tabbas Fatima bata sha tea ɗin da ta kawo mata ba.

Sai da aman ya lafa Daddy ya jawo ta jikin tari da faÉ—i,

“Mekike ji yanzu?”.

Ahankali tace, “komai banji Daddy”.

Momy ko cikin ranta faÉ—a takeyi yariyar nan munafukace fah ji yadda ta wani shige masa ajiki wai ita bata da lafiya wai me ciki.

Ƙaraso wa tayi gaban su kana tace ma Daddy, “tunda aman ya lafa kabata ta sha sai tasha magani kaga zata ji daÉ—in jikin ta”.

Ba musu Daddy ya É—auko kofin tea É—in ya miÆ™ata yace, ” “sha Fatima”.

Kai ta girgiza masa kana tafara magana a hankali tace, “Daddy bana son madara amai zanyi”.

Sai da Momy ta fake idon Daddy ta wanka mata hara-ra kana tace, “to me kike su sai akawa miki?”.

Sai da Daddy ya mai-mai ta mata kana tace,”fura nake su”.

Faɗima Momy yayi abunda tace dan ƙasa-ƙasa tayi maganar dan Mumy bata fahin ta ba sai da Daddy ya faɗa mata.

Momy tace, “to bari na kawo mata” tana faÉ—a tana aikama teema hara-ra.

Tana fita Daddy da kansa ya kai Fatima toilet ya taima ka mata ta gyara jikin ta kana ya fito.

Kuka ta sanya masa tace sai ya kai ta gida.

Da ƙyara ya samu ta haƙura zuwa ajima zai kaita kamar yadda yace.

Mumy ko kitchen ta koma ta É—auko fura ta sake zuba wannan maganin kana tafito domin ta kai mata.

Salamar da akayi ce ya da katar da ita daga saurin da take.

Kallon-kallon suka fara yi ma juna kana Mumy ta Æ™aÆ™alo murmushin karfin hali tace, “yau wa muke agani agida”.

Ita ma Hajiya Sa’a martanin murmushin da tayi mata ta mai da mata.

Gaisawa suka fara yi kana Hajiya Sa’a ta tambaye Mumy yara da kuma Fatima.

Sai da Mumy tayi ajiyar zuciya kana tace, “yara duk suna É—akin su,Fatima ko batada lafiya dan yanzu itace ma zan kai ma fura tashi”.

Hajiya Sa’a tace,”ash-sha meke damun ta?”.

Mumy tace, “lamarin ciki ne”.

Sai da Hajiya Sa’a ta dube Mumy da kyau kana tace, “tana ina yanzu?”.

Sai Mumy tace, “tana É—akin ta”.

Hajiya Sa’a bata sake yiwa Mumy magana ba ta haura sama,Mumy ita ma tana bin bayan ta har suka karasa ciki.

Ko yanzu kwance take shiko Daddy na gefe ta yana jera mata sannu.

Sallama sukayi kana suka shigo .

Aikuwa yana ganin Hajiya Sa’a ya faÉ—a-É—a murmushin sa kana yace,”Babbar Yaya kece agidan?”.

Tace, “nice tunda ku baku neman ba aigwara na zo na-nemeku naji ko lafiya”.

Sai da ya sosa kai kana yace, “Hajiya Babba hak’uri zaki Æ™ara yi damu yanzu ayuka sun muna yawa sasai”.

Tace,hmm “ko bada aiki ba haka kuke Allah dai ya kyau ta.

Fatima ko tana jin muryar Hajiya Sa’a taji wani daÉ—i sosai dan haka tayun Æ™ura ta tashi zaune dumin su gaisa.

Fatima gaida Hajiya Sa’a tayi itama ta amsa ciki da sakin fuska haÉ—e dayi tamata yajikin?”.

“Da sauÆ™i tace mata”.

Mumy ta miÆ™o mata fura tace, “gashi ta sha sai ta sha magani dan yau kome babu acikin ta”.

Hajiya Sa’a ta karÉ“e furar ta buÉ—e sai da tayi mata kallon tsaf kana ta rufe ta aje aÆ™asa batare da tace komai ba kuma bata ba Fatima ba.

.
Bata cema kowa komai ba suka cigaba da firar su game da yadda bikin zai kasan ce na sauran ƙannen ta.

Mumy na tsaye komai bata ce ba da taga alamun ba furar zata bata ba dan haka ta fice zuciyar ta na zafi dan a duniya bata ga abunda ta fi tsana ba irin Hajiya Sa’a,saboda tana mata shi-shige ga lamarin ta.

Sai da sukayi fira sosai kana Hajiya Sa’a tayi musu sallama dan tafiya zatayi.

Aikuwa Fatima nagani tafiya zatayi lokaci É—aya tayi rau-rau da ido ba shiri sai ga hawaye sun fara zuba sai tafara sha-shekar kuka .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button