KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Hajiya Sa’a ta juyu ta kalle ta tace, “Fatima lafiya meke damun ki?”.

Ai kamar kada tace haka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Kallon-kallon aka fara yi tsaka nin Hajiya Sa’a da Daddy.

Jikin shi amace yace, “wallahi ba abunda na mata Yaya”.

Komai bata ce mishi ba ta ƙarasa wajan Fatima,kan ta taɗago tare da kura mata ido.

Jikin ta aÉ—an sanyaye tace, “Fatima me akayi miki lafiya ki gaya min kinji?”.

Sautin kukan da takeyi ne ta rage kana tace,”ni zanbiki bani da lafiya”.

Sai da Hajiya Sa’a ta sauke ajiyar zuciya kana tace,”to dai na kuka da ke zanje kinji”.

Tace “to na daina tana mai ciki da farin ciki”.

Tashi Hajiya Sa’a tayi ta fara haÉ—a mata kayan ta.

Da sauri Daddy ya Æ™arasu gaban ta yana faÉ—in, “dan Allah Hajiya kada kitafi da ita wallahi komai ban mata ba kiyi haÆ™uri Hajiya.

Kallon sa tayi da kyau kana tace, “ai bance kayi mata wani abuba zan dai je da ita sai taji É—an sauÆ™i”.

Ruk’un ta ya ciga ba dayi ta bar masa matar sa amma tayi kamar bata ji shi ba.

Sai da tagama haɗa mata kayan ta kana ta bata hijab tasaka tari ƙi hannu ta suka tafi.

Haƙuri Daddy yaci gaba da bata amma taki saurarin sa har suka kawo babban paulour.

Mumy suka tarar zaune ita da yaran ta,gashe da Hajiya Sa’a sukayi kana tayi wa Mumy sallama taje hannu Fatima suka wuce.

Aikuwa Mumy naganin da Fatima za’aje wani tashin hankali ya Æ™ara ma-maye zuciyar ta kuma bata da halin maganar kada aje da Fatima dan tasan Hajiya Sa’a wuta ce idan aka taka ta akwai bila’i, kuma idan tayi niyar abu ba mai hanata sai Allah.

Aikuwa Daddy nagani da gaske Hajiya Sa’a keyi ya kama bakin sa yayi shiru dan yasan halin ta sarai,amma zuciyar shi ba daÉ—i.

Akuwa tunda ga wannan lokacin Daddy kulum yana hanyar gidan Hajiya Sa’a kuma ta hanashi ya ga Faty shi yayi magiya har ya gaji har Æ™ara ya kai ta ga Gwaggo amma suna magana da Gwaggo tace abar ta har taÆ™ara jin sauki.

Shi wallahi ya gaji matar sa yake buƙata dan yanzu ƴar nacin can ta dawo masa kuma baya sun yana biye mata kuma gashi sun riƙi masa matar shi.

Koda Mumy nanan amma ya fisun ya haÉ—a biyu bare ma teemar sa ta daban ce agun sa.

Dan haka yaje ya sanar da Hauwa ƙawar Fatima a yanzu.

Bayan kuwa biyu Hauwa Ta shirya taje gidan Hajiya Sa’a bayan sun gaisa take tambayar ta Fatima.

ÆŠakin da Fatima take Hajiya Sa’a ta kai ta.

Sai da Hajiya Sa’a ta fita kana Hauwa ta matso kusa da Fatima bayan sun gaisa Hauwa ta dube Fatima da kyau kana tace,

“Ke yanzu teema kina jin daÉ—in zama haka ba mijinki tari dake?”.

“Wai ma me kika gaya ma Yaya Babba da har zata hana masa ganinki?”

Fatima tace, “ba abunda nace mata kuma dakika ce bana jin daÉ—i zama haka to bari kiji wallah ni nafi jin daÉ—in zama haka dan ba mai ta kuramin shi kuma Daddy ya fiye ta kurama mutum dan shi ban wani da muba”.

Wani kallo Hauwa ta watsa mata kana tace,

“Sai kiyi ta zama wata rana sai akawo miki labarin zai aure Hajiya kulu”.

Gaban tane ya bada dumm! kana tace,

Waye Hajiya kulu kuma?”.

Komai bata ce mata mayafin ta ta yafa zata fice.

RiÆ™e mata maya fi Fatima tayi tace, “haba Aunty Hauwa kin san bama haka dake dan Allah ki gaya min” tana magana kamar zatayi kuka.

Kallon ta Hauwa tayi tace, “ni dai nafaÉ—a miki kiyi yadda nace dan inba haka ba hmmmmmm taÆ™ara da cewa yanzu mijin ki ko gida baya zama ya can…bari nayi shuru amma inkin tashi komawa gidan mijikin to ki kirani a waya” tana faÉ—in haka ta fice war ta batari da ji abunda Fatima zata ce ba.

Jikin Fatima ne yayi sanyi sosai kuma lokaci É—aya taji tana son ganin Daddy ko jinsa dan tunda tazo ko wayar sa bata É—auka ba bare ma taji wani hali yake…..

#Vote
Comment
Shere

Sumy M Na’ige🌸
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

ƘAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍�
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}

 ```🎐G•W•A🎐```

GASKIYA DOKIN ƘARFE�

Story & Written
By
SUMMY M NA’IGE✍ðŸ?

Didicated to..
My Hafsa😍

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

Page 43

_📖 Jikin ta a sanyaye ta jawo wayar da ke gaban ta ta dan na masa kira tana ringing ba’a ďauka ba, har sai data yi masa kusan miss call biyar amma ba’a É—auka ba.

Gabanta ne ya fara dukan uku-uku saki kira tayi ko nan ba’a É—auka ba.

Ai bata san lokacin da hawaye suka fara tsiyaya a idon ta ba.

Lokaci É—aya ta shiga rera kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Shi ko Daddy lokacin da ta kira bai ma san takira ba dan yanzu ba ita ba ko Mumy ta daina ganin shi kuma da Mumy ta tambaye shi sai yace mata aiki ne ke re ƙishi.

Dan yanzu ga baki É—aya ya tare gidan Hajiya Kulu sai yadda tayi dashi.

Ita ko Mumy ta ɗauka da gaske aikin ne ke riƙeshi dan haka bata sake maganar ba,bata san Hajiya Kulu ce ta sashi agaba ba.

Wace ce Hajiya Kulu?

Hajiya Kulu gogagayar Æ´ar duniya ce ta bugawa a jari da,tunda mijin ta yarasu bata sake aure ba sai taci gaba da harkokin ta na bariki, tana da yara biyu Salim, Naja’atu,naja tayi aure har da yara biyu shi ko Salim na Dubai yana karatu.

Ita ko Hajiya Kulu bata da wani aikin da ya wuce shiga cikin Æ´an siyasa da Æ´an kasuwa da manya mutane data ji za’ayi wani taro ko metting to babu abunda ke hana mata zuwa ko dan ta samu wanda ya kwan ta mata arai idan taga namiji ya kwan ta mata to fah duk yadda zatayi sai tasa ya kula ta ko baya so.

Haka tafaru haÉ—uwa su da Daddy wata rana sun yi metting suna fitowa shi kuma yana sauri ya tafi gida dan Mumy ta kirashi tace mishi Kulsum ba lafiya har sun kaita asibiti.

Karu yaji yayi da mutum dan bai masan da mutum ba.

Kansa ya É—ago ya kalle ta, hak’uri ya bata ba tare da ya tsaya ba ya wuce war sa.

Ita ko tunda ta ganshi taji ya kwanta mata arai aikuwa tunda ga lokaci tabi duk wata hanya da zata bi har ta samu ya fara kula ta.

Taso ya aure ta amma yaki amma wannan lokaci kuma tace dole sai ya aure ta kuma da alamu zai amince.

Hankalin Fatima ya tashi sosai,bata tsaya wani abu ba tafito falo zaune ta same Hajiya Sa’a tana kallo dan haka ta Æ™arasu wajan da take, zama tayi tare da gaishe ta.

Bayan sun gama gasaiwa Fatima tana son tayi mata magana kuma tana jin nauyi abunda zata faÉ—a É—in.

kula da haka É—in da Hajiya Sa’a tayi dan haka ta kalle Fatima da kyau kana tace,

“Fatima ko kina buÆ™atar wani abune?”.

Tana son tace eh kuma da kunya ta faÉ—a mata abunda take su.

Mai-mai tama ta Hajiya Sa’a ta koma yi,amma sai tayi Æ™arfin halin cewa “a’a ba komai Hajiya”.

Bata yadda da abunda tace ba dan haka tace,

“Fatima ni aganina ni dake ba wani abin boye-boye in har kin É—auke ni amatsayin Yaya kuma uwa ina son ki gayamin meke da munki?”.

Shuru Fatima tayi sai can ta numfasa kana tace,

“Dama ba komai ba ne Daddy ne naga ya bar zowa gidan nan kwana biyu”…tana faÉ—a tanayin Æ™asa da kanta muryar tana rawa.

Sai da Hajiya Sa’a tana numfasa kana tace, “kada ki damu anjima zan neme shi naji ko lafiya” daga haka bata sake magana ba dan ta kula Fatima tana son ta kuma gidan mijin ta kuma ita bata son ta koma yanzu sai taji sauÆ™i laulayin da take yi.

Ita ko Fatima duk kunya ta bi-biye ta saboda abunda ta faɗa gani take bata yi dai-dai ba da ƙyar ta tashi ta kuma ɗakin ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button