
Suma su Hajiya Sa’a da Kaka Amo bin su sukayi É—akin da Fatima take.
Kuda suka shiga tana zaune saman gado kamar ba ita ce Daddy ya É—auko ba rai a hannun Allah.
Ƙarasuwa sukayi wajan ta suka fara yimata yajiki .
Bayan ta amsa suka bata yaran da ta haifa tagani amma saboda kunya cemusu tayi ta gansu.
Da ƙyar suka samu ta karɓa yaran.
Bayan awa biyar aka sallame ta dan ba abunda ke damun ta sai rashi ƙarfin jikin da bata da, koshi sunce zowa wani lokaci zataji ta dai-dai.
Gaba ki É—aya Daddy ya manta bai kira Mumy ya faÉ—a mata ba.
Hajiya Shafa ce ta kira ta dan suma har sunji labarin haihuwar Fatima ransu baiyi daÉ—e ba dan ba haka suka so ba.
Dan kishayar ta Nafisa har rawa sai da tayi ita da sauran amaren saboda murna.
Sai da takira har sau biyu kana Mumy ta É—auka dan tana É—aki tana bakin cikin zowan Daddy gida dan son tayi abar ta har ta gama shan woya kafin akai ta hospatal kafi wani lokaci komeye acinkin ya mutu.
Tana cikin haka wayar ta ta fara rura har taso taƙi ɗagawa amma data ga andame ta dakira dan haka ta ɗauka.
Sunan Hajiya Shafa tagani dan haka tayi sauri ta kara akunnen ta.
Bayan sun gaisa sai Hajiya Shafa tace “ko har dake kuna hospatal?”.
Sai Mumy tace “warin me?”.
Sai Hajiya Shafa tace, “au baki masan ki shiyarki ta haihuba kenan dan naga ko kiran mu bakiyi ba”.
Tana cewa haka sai da gaban Mumy ya faÉ— baki na karkarwa Mumy tace “yaushe ta haihu kuma me ta haifa, taÆ™ara da cewa nasan kome ta haifa ya mutu”.
Sai da tagama jerama Hajiya Shafa tambayoye kana ta buÉ—e baki tace “ko É—aya dan niman yanzu naji mutumi yar ta ta fito tana guÉ—a tana rawa wai anhaifar musu Æ´an biyu kuma gaba É—ayan su maza ne”.
Ai tun Hajiya Shafa bata kai Æ™arshin zancin ba Mumy ta sake waya ta faÉ—i Æ™asa tace tas…
Tan gaɗi ta farayi kamar zata faɗi,kujerar dake kusa da ita tariƙe kana ta fara magana cikin wata muryar kamar ta ƙatti.
Tana faÉ—in wallahi Æ™arya ne ba wata wadda zata haife É—a namiji a wannan gidan ta zauna lafiya matuÆ™ar ina raye”.
Hauka Mumy ta farayi har da cewa ba jinin Daddy ne ba in ma da gaske anhaihu É—in.
Tana cikin wannan haukar Daddy ya shigo da sauri ta Æ™arasa gareshi tace “Daddy Zainab ina Fatima É—in? tunda har zaka É—auke ta amma baka sanar dani ba”.
Yace “albishirin ki
kin samu yara biyu dukan su maza”.
Wannan karun Mumy ta sauya ba kamar da ba dan Æ™iri-Æ™iri tace “da gaske ko É—iyan kane? kodai wani wajan tasa musu ta Æ™aÆ™abamaka kai ko ido rufe zaka karÉ“a”…..bai bari ta kai Æ™arshin zancin ba ya wanke ta da mari har bayu.
Yana huci yana nunin ta da É—an ya tsa kana yace “kin san me kika faÉ—a kowa, yaran nawa zaki fara sheganta su kuma ina raye”.
Ba’abun da bai ce mata ba itama haka daga bisani yaga abun nata kamar da taÉ“in hankali dan haka yafice yabar mata gidan gabaki É—aya.
Duk abunda akeyina hidamar suna Mumy bataje taga yaran nan ba kuma ta hana yaran ta zowa Zainab ka dai ce taje amma batare da sanin Mumy ba dan tace duk wanda yayi mata maganar Fatima sai ta illatashi.
Mumy takoma kamar sabon kamun hauka dan bataji bata gani ko ina zowa takeyi dan akashe yaran ita dai burin ta su bar numfashi.
“`(Allah sarki su yara mesuka sani ko me suka yamata.
Dan Allah ƴan uwana mu daina ƙazamin kishi dan bashida anfani wallahi wani kishi illah ne ga remu.
Kowa na dakishe amma kada kishi yasa muhaÉ—a Allah dawani,dan haka mukeyaye Æ´an uwana.
Allah yasa mufi Æ™arfin zukatan mu kuma ya kare mu daga Æ™azamin kishi ameen. “`)
Inyi shagalin wajan sunan yaran inda Daddy yace ba zai sauya musu suna ba haka zai a barsu.
Sosai nera tayi kuka dan ba abunda Daddy bai yi mata ba, har sauyama iyayen ta gida yayi kuma yaba mahaifin ta mota har Æ™anwar ta sai da yaba mota itama Kaka Amo sai da yayi mata kyau ta mai girma Hajiya Sa’a ma tawa Kaka Amo, aikuwa Kaka Amo kamar tayi hauka dun daÉ—i.
Duk hidamar da akeyi ta sunan su alhasan bawan da group7 suka je kuma basuyi murna ba.
Watan Fatima É—aya da haihuwa akayi auren su Zainab da Nabila,anyi shagalin biki sosai anka kashe nera Mumy ma ta narke nara sosai.
Bayan bikin su Zainab da sati uku Daddy yama tsama Hajiya Sa’a amaidam masa da Fatima.
Ba yadda ta iya tashirya taje gidan iyayen ta ta faÉ—a musu saÆ™on Daddy kafi kowa yayi magana Kaka Amo tace wani sati da kanta zata maida Fatima ita kam Ummah bata so haka ba, dan taso abar Fatima har tayi arba’in biyu amma ga yadda Kaka Amo tace kuma yadda tace haka za’ayi dan haka bata ce komai ba tayi shuru dan bata iyawa da yayyaÆ™ar da zata mata.
#Vote
Comment
Shere
Summy M Na’ige🌸
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦
ƘAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.
®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONâœðŸ?
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}
```ðŸŽG•W•AðŸŽ```
GASKIYA DOKIN ƘARFE�
Story & Written
By
SUMMY M NA’IGEâœðŸ?
Didicated to..
My lovely Aunty🥰🥰🥰🥰🥰â?
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
Godiya mai tarin yawa ga hasken gaskiya Writers,ina matuÆ™ar jinjina a gareku da godaya agareku sarakan haÆ™uri da kawaici da yafiya, ina Æ™ara godiya gareku na yadda kuka fara fitar da tauraruwa ta social media har take haskawa banda kamarku My Aunty nah (Mrs xerks) &Ummu Nabilâ?
Ina sonku
irin sosai ɗin nan Allah yabar min ku😘
Duk inda kuke inanan liÆ™e daku koda zakuyi min gore bazan barku ba bare nasan ba halinku bane yima mutum goreðŸ˜
Allah ya baku nasarar abunda kuke nema duniya da lafira Allah ya ƙaramuku basira mai yawa wadda zaku anfanar da dubban mutane da ita sabida Allah👌 Ameen ya Allah.
Ina ƙaunarku all gaskya writers😘
Masu iya magana sunce, da wasa da yaro gwanda kwana da yunwa👌
Page 48
_📖
Bayan sati ɗaya da dawowar Fatima Kulsum taje ta karɓo Husaini tazo da shi wajan Mumy aikuwa Mumy naganin tazu da shi ta karɓeshi cikin mutumci tace ma Kulsum taje ta karɓo ɗaya.
Da gudun ta taje dumin ta karɓo Alhasan.
Tana fita Mumy tayi sauri taje ta É—auko wani fauzin tahaÉ—a shi da madara ta fara bashi.
Suna cikin haka sai ga Kulsum ɗauke da ɗayan,da sauri Mumy ta karɓeshi tace mata ta ɗauke Husaini ta maida ita ko ta karɓi Alhasan.
Haka kowa akayi Kulsum ta É—auke shi ta maida tana fita Mumy ta É—auko Alhasan ta bashi wannan madarar mai haÉ—e da fauzin.
Ko da Kulsum ta dawo Mumy na bashi madara tace “Mumy ashe ya iya shan madara” tana faÉ—a tana dariya jin daÉ—i.
Mumy tace, “eh ya iya mana ba gashi yana sha ba”.
Mumy sai da taga ya sha madara sosai kana tace ma Kulsum ta maidashi wajan Mamar sa kuka yakeyi.
Kulsum ko ta dauka ta maida shi wajan Fatima.
Tana zuwa tace ma Fatima Mumy tace na maida shi kuka yakeyi dan har madara ta bashi yaki ya daina kuka.
Karɓar sa Fatima tayi tayi masa wanka ta kwantar da su.
Bayan minti ashirin da maida su sai ga yara sun fara fitar da kumfa abaki suna yin wata irin miƙa kamar zasu mutu.
Aikuwa Fatima na gani hak lokaci É—aya ta riki ce tama rasa me zatayi sai can dabara ta faÉ—u mata ta É—au waya ta kira Daddy tana kuka ta faÉ—a masa abunda ke faru.
Baƙara min ta shin hankali ya shiga ba lokacin da tafaɗa masa haka da sauri ya bar abunda yakeyi ya zo gida.