KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

Koda ya ƙarasu bai tsaya komai ba ya ɗaukesu hankali ta she ya kai su hospatal ɗin dake kusa da su.

Taimakun gwagawa likitoci suka fara basu.

Shiko Daddy sai safa da marwa yakeyi a hospatal.

Ita ko Fatima na zaune kamar ba abunda ke damun ta, amma azuciyar ta tafima Daddy shiga tashin hankali.


Ita ko Hajiya Kulu tunda Daddy ya dai na kulata taje wajan Malamin ta akace sai ya rabu da Fatima zai dawo dai-dai,to tayi yawo wajan Malamai har tagaji amma bata samu nasara ba acan ne garin yawon ta tahaÉ—u da wani Alhaji tundaga wannan lokaci suke tare ko ina zaije da ita yake zowa.

Bayan wata uku da haÉ—uwar ta da shi har tafara tunanin yadda zata dawo wajan Daddy sai ciyo ya kamata ba sauki har sai da akaje hospatal.

Ana mata gwajin farin sai aka gano tana dauke da cuta mai karye gargowar jiki ajikin ta.

Tashiga tashin hankali sosai kuma taneme wannan Alhajin ƙasa ko sama amma bata ganshi ba tayi kuka har ta gaji ba dan son ranta ba ta fara shan magani dan lokaci ɗaya jikin ta ya sauya kowa ya san halin da ta ke ciki har yaran ta sunyi kuka har sun gaji sunyi tir da hali irin na mahaifitar su.

Daga baya da suka ga yadda ta koma lokaci É—aya dan haka suka sauko daga fushin da sukeyi da ita suka fara bata kulawa.

Amma lokaci-lokaci take zuwa kaɓar magani amma kamar bata sha dan har yanzu jikin nata bashi da kyau gani.

Sunfi awa biyu kafin likitoci su fito.

ÆŠaya daga cikin Doctors É—in da suka fito yace ma Daddy ya sameshi office dan haka ba musu suka biyu bayan shi har ita Fatima.

Bayan sun zauna dactor kewa Daddy bayani kan yaran yace, “ba komai aka basu suka sha ba sai guba mai illah acikin É—an adam yace amma sunyi Æ™oÆ™ari wajan dawo da lafiyar su amma yanzu muna jiran farfaÉ—owar su lokaci kaÉ—an amma kuyi addu’a dan koshi abune mai wuyar gaske”.

Hankalin Daddy sosai ya tashi lokaci É—aya ya dawo da kallon sa ga Fatima.

Tambayar ta ya farayi waya ba yaran sa guba.

Irin yadda yake mata magana yasa ta rikice tama rasa me zata ce masa.

Magana yake mata amma takasa koda mutsa baki bare yasa ran zata ce wani abu.

Ai da zuciyar sa ta rufe basan lokacin da ya kai mata mari har biyu ba.

Itako tana can tana tunanin yadda zatace masa tasan komai basa sha inba nonoba sai madarar da Kulsum tace Mumy ta basu É—azo kuma tana gudun tace Mumy ta basu madara wata rigima ta tashi dan yace ko ruwa kada abasu sai sun kai wata bakwai.

Tana cikin wannan tunanin taji saukar mari har biyu alokaci É—aya.

#Vote
Comment
Shere

Summy M Na’ige🌸
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

ƘAWAR ƳATA CE
1441H/2019M.

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍�
{Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata burin mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da lahira}

 ```🎐G•W•A🎐```

GASKIYA DOKIN ƘARFE�

Story & Written
By
SUMMY M NA’IGE✍ðŸ?

Didicated to..
All Gaskiya writers😘

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

A RAYUWA ILIMI NA DA DAƊI IDAN KASAMU ƘARAN CIN ƊAYA DAGA CIKIN BIYU NAN RAYUWA BAZATAYI DAƊI BA, AllAH KABAMU IKON NEMAN ILIMIN DUNIYA DA LAFIRA
AMEEN YA AllAH.🙏

Page 49

_📖 Kanta ta É—ago ta kalleshi shiko inba huci ba ba’abunda ya keyi.

Nunin ta ya keyi da É—an yatsa kana yace “kigaya min me kika ba yarana wanda ke neman ya ka shesu”.

Komai bata ce masa ba dan irin yadda taga yana magana ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba.

Tashi tayi taje nesa kaÉ—an dashi ta kira Hajiya Sa’a ta faÉ—a mata abunda ke faru.

Bata jima da kiran taba sai gata tazo .

Yadda taga Daddy ko ita hankalin ta ya tashi amma ta dake ta fara bashi haƙuri da nuna masa cewa yaran zasu ta shi.

Cikin ikon Allah yaran na cika awa uku suka fara mutsawa.

Doctor suka kira ya ƙara duba yaran ya tabbatar musu da lafiyar su sannan Daddy ya samu natsowa.

Daddy ko ya nace sai Fatima ta gaya masa me taba yaran shi.

Badan taso ba tayi masa bayani tace bata basu komai ba inba Kulsum da tace Mumy ta basu madara ba.
.

Ai tun bata Æ™arasa faÉ—a ba ya kama hanyar fita Hajiya Sa’a na kiran sa amma bai san tanayi ba.

Sosai yasa direba gudu basu ɗau wani lokaci ba suka ƙarasu gidan.

Kafin driver yayi packing Daddy ya buÉ—e murfin mota yafito.

Ba kowa a parlour dan haka da sauri ya ƙarasa part ɗin Mumy .

Koda yaje har zai ƙwalamata kira sai yaji tana waya haɗe da wata irin dariya .

Bai ce komai ba dan abun mamaki ya bashi na wannan dariyar da takeyi.

Wayar ta taci gaba da yi ita da Hajiya Shafa tana bata labarin yadda akayi taba yaran poisen suka sha har yadda taje wajan wani Malami wanda yace a cikin satin nan Daddy sai ya sake Fatima kome suke ta ƙama da shi .

Firar su suka cigaba dayi sai da suka gama kana suka aje wayar Mumy tayi haka ta É—ago kanta suka haÉ—a ido da Daddy aikuwa ba shiri ta tashi zaune tana burin kunya.

Shiko Daddy gaba ki É—aya yarasa me zai ce mata abun duniya ya taru yayi masa tsaye azuciya .

Mumy ko gaba ki É—aya jikin ta yafara karkarwa harda kukan munafurci ta farayi.

Har ta buÉ—e baki dumin tayi masa magana amma ya daka mata tsawa yace “duk abunda zaki faÉ—a bana son ji,dan haka kitashi kibarmin gidana na sakeki saki biyu, kuma kisani komai kikayi min na barki da Allah kuma kanki kika cuta bani ba”.

Yana kaiwa anan ya ficewar sa zuciyar sa na ƙuna dan ji yake kamar ya faɗi, ikon Allah ne ya kaishi ɗakin sa ya samu ya zauna kana ya ɗauko magani ya sha sannan ya ɗan kwanta.

Ita ko Mumy ba Æ™aramin tashin hankali ta shiga ba dan bata taÉ“a tunanin akwai lokacin da Daddy zai’ayi furta kalmar saki agare ta ba.

Sosai ta shiga tashin hankali waya ta É—auko dan ta kira Hajiya Shafa ta gaya mata abunda ake ciki.

Kiran ta tayi amma har ta tsinke bata ɗauka ba har sau biyar ta kira batayi picking ba sosai hankalin ta ya ƙara tashi.

Itako Hajiya Shafa koda Mumy ta kira itama tana cikin nata tashin hankali dan Alhajin Aliyu yazu wucewa yaji tana waya tana dariya abunda ta faɗi ne yayi matuƙar bashi tsoro da mamaki hankalin sa ya tashi dan haka bai san lokacin da yaki feta da mariba har sau uku lokaci ɗaya, sai da yaci mata mutunci sosai kana ya bata takardar sakin ta itama biyu yace ko minti ɗaya kada ta ƙara ta bar masa gida sa.

Tana kuka tana bashi hakuri amma kamar cemasa takeyi ya kara,da taga yana nema ya illata ta bata san lokacin da tafito daga gidan ba.

Gidan Mumy ta nufa dan ta faÉ—a mata abunda ake ciki tana bisa hanyar tafiya ne Mumy ta kira ta.

Koda ta isa gidan Mumy itama har ta fara haÉ—a kayan ta dan ta tafi gidan.

Tanaa cikin haka taga Hajiya Shafa hankali ta she Mumy tambayar ta ta farayi lafiya, nan Hajiya Shafa ke faÉ—a ma Mumy abun da ake ciki.

Itama Mumy gaya mata nata tayi nan suka haÉ—e suna kuka gwanin ban tausai.

Shiko Daddy sai da yasamu kwanan awa É—aya yaji zuciyar sa ta É—an rage yimasa zafi.

Dan haka wanka yayi ya dawo hospatal.

Koda ya dawo fuskar sa bawani annashawa dan daka gansa kasan yana cikin damuwa .

Kiran Hajiya Sa’a yayi gyafe É—aya ya faÉ—a mata abunda yake ciki yana faÉ—a kamar yayi kuka.

Duk da taji daÉ—in hukunci da yayanke amma sai ta nuna masa ba ayanke hukunci cikin fushi sosai taÉ—an jamasa kunne haÉ—e da bashi kuri har ya É—an sauko.

Suna cikin haka Alhaji Aliyu shima yakira ta ya faÉ—a mata abunda ake ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button