KAWAR 'YATA CENOVELS

KAWAR ‘YATA CE COMPLETE

KAWAR 'YATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS

     🎐 ```G•W•A```🎐

GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼

Story & written
By
Sumy

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

Page1�0�

Hajiya Sa’a ta kasan ce yaya ce ga maza jin su Mummy ,Su takwas iyayin su suka haifa kuma ita kad’aya ce mace kuma ita ce babbarsu

Alhaji Muhammad shine mahaifinsu yana da rufin asiri dai dai gwargwado dan akwaishi da wadatar zuci shiyasa mutane da dama sukemishi kallon mai kud’i.

Matan shi biyu da Halima da maryam

Yaransu takwas Halima ita ce uwargida san nan Maryam ita ce amarya.

Mama Halima itake da yara shidda sa’adatu da Aliyu da Nura da Abdullahi da Ahamad da Mansur.

Ita koh Gwaggo Maryam tana da yara biyu da Sulaiman da Abbas.

Suna kiranta gwaggo saboda ita da Alhaji Muhammad auren zumunci ne sukayi dan d’iyar k’anin Baban shi ce.

Mama Halima da gwaggo maraya suna zaman lafiya sosai dan idan kagansu bazakace kiyoshi ba ne dan suna zaman mutunci kowacin su nada hakuri da kawai ci dan shi baza ka iya babbace yaran su ba.

Kuma Alhaji Muhammad baya nuna ma kowacin su babbanci haka ma yaran shi yana kulada su dai dai gwargwado kuma kowanin su yasan
yashi makarantar addini da ta zamani haka suka ciga da rawuwar su babu fada babu zagi.

Lokacin da Sa’adatu takammala secondary School,

Tasu ta cigaba da karatunta dan har baban a bukiyar ta Amina yasamu musu admission d’in usuman dan Fodiyo unversity Amma baban ta yace a’a”.

Sai intayi aure mijin ta yabar ta amma shikam bazai barta ta tacigaba ba.

Tayi kuka har ta gaji dan haka dole ta tsayda wanda zata aura
cikin samarin ta,

Wanda ta tsayad dayake shima dan boko ne kuma yace zai bar ta taci gaba da karatunta.

Ba ad’au lokaci ba akayi auren Sa’adatu da Umar inda suke cikin kwanciya hankali da k’aunar juna.

Kuma bata jima ba ta fara karatunta a Usuman dan Fodiyo .

Sukuma kannen ta maza suna Karatu Kuma suna zuwa kasuwa wanji mahaifinsu Nura da Sulaiman da Abdullahi suke zowa kasuwa.

Ahamad da Mansur da Aliyu suke gyaran mota .

Kuma da lokacin karatu islamiya yayi komai suke yi zasu barshi suje.

Haka mana boko kowane su ya nada tashi basara Dai dai gwargwado ,

Aliyu da Abdullahi da Sulaiman tari suka kammala secondary School,

Kuma cikin sa’a suka samu admission,

Haka karatunsu yaciga da tafiya har suka kammala digree d’in su nafarin cikin ikon Allah suna gamawa mijin yayar su Sa’adatu ya samar musu Aiki ,

Ita Kuma a lokacin Sa’adatu har ta kammala karatun ta tafara Aiki dan tana kammalawa mijin ta yanemu mata Aikin asbiti.

Alokacin tana da yara uku Mufida Khdija da Ammar.

Haka rayuwa taci gaba data fiya alokacin ne kuma Baban su yace Aliyu da Sulaiman da Abdullahi su fitar da matar aure dan yace bazasu joining masters ba sai saunyi aure,

Koda ma Aliyu yana da wadda yake so dan tunda yaje service wata makarkata secondary yahad’u Shafa’atu tun lokacin suka fara soyayya,

Shima Sulaiman yakawo tashi Fateema amma anfi kiran ta da Binta daya ke unguwar su daya malam Usuman shine mahaifinta matan shi biyu yana da kirki sosai kuma ko d’iyan shi ba laifi sunada tarbiya,

Shima Abdullahi yakawo tashi Lubabatu d’iya ce ga Alhaji ma’azu yana dakirki sosai harkar kasu wanci tahad’a su inda wani lokaci Alhaji ma’azu yakan aiki Abdullahi gidan sa acan ne ya had’u da Lubabatu.

Ba’a d’au lokace ba aka aikama iyayin yaran kuma kowanen su yayi na’am dajin d’an Alhaji Muhammad kesun ‘yar shi,

Bawani lokace aka d’auka ba akayi bikin su,

Inda kowane su yatare a sabon gidan da yagina ma kansa,

Idan alokacin Ahamad da Nura da Mansur suka samu admission,

Bajimawa suma suka fara karatu ,

Suma basujima da aureba suka joining masters dinsu

Haka rayuwa taci gaba datafiya Kuma arzikin su na k’ara yawa .

Inda alokacin sun kammala masters d’insu sukuma su Nura da Ahamad da Mansur sun kammala digree su .

Kuma alokacin har sun kawo matan da zasu aura.

Idan Nura yakawo kanwar abukin shi Suwaiba wadda suka dai dai ta da ita .

Shima Ahamad yakawo tashi Sha’awa tana da kiri dan ranr yaje wani shago dake kusa da unguwar su bayan ya saye abunda zai saya yabi ya yafito Ashe wajan bayan kud’i wayar shi ta fad’i bai sani ba,

Ita Kuma bayan ta gama sayayyar da zatayi fitowa dazata yi taga waya yashe ak’asa tasa hannu ta d’aka tace kowaye ai zay Kira ,

Sai da yakoma gida yaga ba waya kira yayi tad’auka tayi mishi kwatancin gidansu yazo yakar ba.

Tunda ga lokaci suka fara soyayya

Shiko mansur wani Alhaji Abubakar dan siyasane sosai gyara mota ya had’a shi da Mansur yana son Mansur har yaka sance wani Abu idan zaiyi sai shawar ce Mansur yasan ya Mansur jikin shi yad’auke shi kamar d’a.

Dan haka gidan Alhaji Abubakar yakoma kamar gidansu Mansur.

Alhaji Abubakar matar shi d’aya sunan ta Hajiya Asuma’u yana da yara biyar macci hud’u namiji d’aya.

Hadiza da Rukayya da Shamsiya da Hauwa wadda akifi sani da jidda sai autan su Marwan.

Tunda Hadiza taga Mansur tafara shige ma sa shikoma baya su yayi ta kauce mata yana daure mata Amma taki dainawa har yagaji yafara sake mata .

Shikoma Alhaji Abubakar yad’auka soyayya suke yaji dad’i sosai dan haka yasame mahaifin Mansur yasheda mishi yaba Mansur d’iyar shi Hadiza koma nan badaji mawaba za’a yi biki Baban su Mansur yayi mishi godiya sosai.

Bayan Alhaji Abubakar ya wuce Alhaji Muhammad yashiga gidansa yana fad’ama matan sa Suma sunyi murna sosai .

Shikuma Munsur koda yaji hankalinshi inyayi dubu yatashi….

Yace shi fah ba sonta yakeyiba yana dai kulata ne saboda Baban ta,

Mahaifinsu yace ko baya son ta sai aure ta tunda mahaifinta yabashi ita.

Hakan akayi aure ba dan rashi yasu ba.

Akowa Hadiza tana ganin Mansur da gaske ba son ta yake ba hankalin ta yatashi har tagaya mamar ta mamar ta ce takwantar da hakalinta tace mama dan baki yadda yakemin ba.

Mama tace naji dok zai daina anjima zan Aiko Rukayya takawo miki wani abu kuma duk yadda akace kiyi kiyi inhar kina son yadai na yin abunda yakemiki.

Tace tau mama zanyi inajiran ta sai tazo tace “to yayi .

Aikowa tunda ga wan’nan lokaci Mansur yakauda zancin wani rashin so,

Dan yariga yafad’a hannu su Hajiya Asuma’u .

Haka rayuwa takasan ce musu kowanin nakula da iyalinshi kuma da iyayinsu dan yanzo har Aikin Haji sunkai iyayin su suma sunje har matan sun je .

Inda a lokacin kowanin su nada yara Abdullahi .yaran shi biyar
Aysha Saudat Nasir Safuwan da Alamin.

Inda Sulaiman ma haka Halima suna cemata (Mimi) saboda sunan mahaifiyar su sai Walid sai Usuman sai Mubarak sai Yusuf .

Sai Aliyu yana da yara uku Jawad da Muhammad amma suna kirinshi (baffa) saboda sunan mahaifinsu ne dashi sai Hafsa.

Muje zuwa

Commet
Nd
Share
1/23/20, 11:48 AM – +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

 *KAWAR* *'YATA* *CE* 

®�
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION�
{ Gaskiya É—aya ce daga Æ™inta sai É“ata, burinmu mu faÉ—akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     🎐 ```G•W•A```🎐

GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼

Story & written
By
Sumy�

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

     *Page11* 1�1�

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da dad’i ba dad’i.

Su Nura nada yara d’aya, Allah yayima Alhaji Muhammad rasuwa mutuwar da ta girgiza family dinshi, dan ankwanta dashi ba’a tashi dashi ba.

Allah yak’ar b’e abun sa, sunyi kuka har sungaji.

Itama Mama Halima wata biyu da rasuwar Alhaji itama tabashi tace ga garinku.

Sosai suka shiga tashin hankali dan cikin su bama iya lallashi dan uwansa haka suka kasance babu mai iya wani abun kirki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button