
Gwaggo Maryam abu duk yadame ta, ta rame har ciyo sai da takwan ta dan ma Hajiya Sa’a koda yaushe tana leko ta, ita da yaran ta.
Dan ita gwaggo Maryam gani take ace yara bakwai duk, ba mai leko ta, data tunu haka sai ciyon ta yatashi, Hajiya “,sa’a tayi tayi mata magana ta tarage sa tuneni arain ta amma taki.
Tace “,Sa’adatu bazan iyaba ina dai rukon Allah sauki, kiduba kiga fah jiya zanje barka Ina fita nakawo gidan su Binta naga Sulaman yakawo yaranshi gidan kuma yagan ni amma sai yayi kamar bai sanni ba, tana mai fashewa da kuka.
Itama Sa’adatu abun yab’ata mata rai Amma tadake tana bata hakuri tace komai lokacene da shi tayi taba ta hakuri har ta d’an sauka.
Kiran Baban su Mufida tayi “,taneman ya bar Mufida da Khadija suzo wanjan gwaggo, dan kar abar ta bakowa kuma taga kamar ciyonta,, nasu tashi”.
Yace ,”bakumai yace “,takirasu tagaya musu dan baya gida , yakar dacewa , Allah ya bata lafiya sai nazo anjima”. Tace “,to”
Bayan su Mufida sunzo shima Baban su yazo tabishi suka koma gida.
Shigar su keda wuya tafad’a jikin shi tana kuka, mai cinrai.
Bai hanata ba sai datayi mai isar ta sannan yafara lallashin ta yanuna mata tace ,”gaba da hukuri komai mai wucewa ne, da k’ar yasamu tayi shuru, nan take itama zazzab’i yarufe ta, sai da tasha magani takwan ta, ya gyara Mata kwanciya sannan shima ya kwanta.
Haka, rayuwa taci gaba da tafiya.
Haka skacigaba daneman tai mako basusa gajiya ba.
Suma su Hajiya Safa ,”haka suka cigaba da kaima malamman su kud’i aiyi musu aiki lokaci lokaci.
Ance dai komai da lokacin shi duk abunda kasa Allah gaba zaka dace komai tsawun lokaci, mai hakuri natari da riba.
Komai kakeyi, arayuwa kasa naci da hakuri, dan shi _ko malamin arbiya yace “, duk , wanda yanacema bukun kufa wata rana za’a b’ud’e masa, koda kara tune kanace natabbatar, koda _k’wak’walwa_ka, bata d’auka wata rana zata d’auka, dan haka ko rok’un Allah ne ,kana ce kada kasa gajiya .
Aikowa ranar gwaggo Maryam tana zaune ita da Mufida suna fira, sallama taji anayi ,sun d’auka ma Ammar ne, gwaggo Maryam tace ,”bazaka shigo ba?”.
Wanda taga yashigo yasata mikewa tsaye bata kara Ida mikewaba biyu suka, yashigo
Kallon, kallon, suka farayi tsakanin su, kowanisu yara sa bak’in magana, hamdale tafariyi ma Allah da kirari ,kana tayi k’arfan halin tace wa “,miya kawo ku gidana ?”.
Bawanda yasamu bak’in magana, tsawa ,tadaka musu,tace” ,Meya kawoku gida na?” kufitar min daga gida, ku akwai wanda yaginamin shi, acikin ko?”.
Konan bawanda yayi magana, gwaiwowi su ,”saka fara kaiwa kasa suna neman gafarar ta, da yafiyar ta”.
Amma tayi kamar bata tab’a sanan inda suka fitoba .
Tace ,”kubarmin gidana inba haka ba zan fad’i mumunar kalma akan ku, abunda ban tab’ayi akanku ba to yanzo, zanyi “.
Bashiri suka tashi suna masu fitar da hawaye, dan su basu tab’a gani tayi fushe ba, balema irin haka.
Jikin su a sanyaye haka suka fito a gidan, asuron gida suka tsaya, suka yanke shawara suje gidan Malam Usuman.
Aliyu yayi k’arfin halin, cewa “mukira sauran sai muje tare kumai nene ayi agabansu.
Haka kowa, sukayi sukara su, bajimawa suma suka k’arasu.
Bayan sun k’arasu, suka wuce gidan Malam Usuman.
Fitarasu keda wuya ciyon gwaggoj, Maryam yatashi, aikowa tarin da Mufida tajine ,da sauri tak’arasu wajan ta.
Waya, tad’au ka ,takira Mamar ta, tagayama ta, abunda kefaruwa, aibata k’arasa ba Hajiya Sa’a taci gatan zuwa.
Koda Hajiya Sa’a ta karasu, gwaggo Maryam tayi nisa kamar ma bazatayi rai ba, yadda Hajiya Sa’a ,taga gwaggo Maryam batasan lokacin da kuka yakufuce mata ba.
Jinta na karkarwa takira mijin ta, tashe damasa abunda kefaruwa,
Yace ,”gashinan zuwa” bai tsaya jin mizata ceba yayanke wayar.
Da sauri yafigo muta yazo, baicemusu komai ba yad’auku ta yakai mota suma suka bi yonshi yasa ta mota bai tsaya da ita ko inaba sai wata babbar hospital dake kusa da unguwar su.
Dauri nurses suka zo da gadun da ak d’ura Mara lafiya aka d’ura ta suka wuce emergency da ita aka fara bata taimako cikin ikon Allah numfashin ta yadawo dai dai.
Hajiya Sa’a in ba ,”anbatun Allah ba ,ba abunda takeyi har sada taga Doctor yafito da sauri takarasu wajan Doctor dayake yasan ta yace ,”Doctor kwantar da hankalinki komai yadawo dai dai yanzo tasamu bacci fatarmu Allah yakiyaye gaba .
Da ,”Ameen ta amsa tanamai ajiyar zuciya ita da mijin ta Alhaji Umar.
Sai da yaga komai ya lafa yace ,”musu shi zaije yadawo, godiya tamishi kana ya wuce.
Suna kawowa k’ufar gidan Malam Usuman Kai tsaye suka wuce, da sallama suka k’arasa ciki falon sa,suka sameshi yana kallon labaru da sauri yamai da hankalinsa inda ake sallam.
Da kallo yabisu har suka Ida shigawa, bai cemusu komaiba.
Gasheshi ,”suka fara yi, bai cemusu komaiba.
Sai can,”yace yanzo damikoka zo?”.
“,Hak’uri suka fara bashi akan abunda sukayi mishi “.
Yace ,”nibakuyimin komai ba, wad’anda kukawa, su zakuba hakuri bani ba.
Amma ,”wallah ni kumban mamaki, wai da hankalin ku, da llimiku, aci kunzab’e matan ku, sama da iyayinku, Kuna sun ku gama da duniyan lafiya kowa,?”.
Fad’a da nasiha yayi musu sosai, kana yad’ura, dacewa ,kukara rik’i ibadar ku sakaci da ibada nasa shed’annu suyi galaba da mutum”.
Hanyoyi yayi tad’urasu akai, kana yace ,” yanzo kutashi kuje kuneme gafar mahaiyar ku”.
Suka ce “,daga cin muka fito wallahi ko saurarin muma taki”.
Yace “,nasan za’ayi haka ,wallahi tayi kukan, dare, tayi narana, har tausai takebani, shiyasa bako da yaushe nake zuwa ba.
Sa’adatu ce ke zuwa kuwani lokaci saboda yanzo bawata cikarkar lafiya ne da ita ba”.
Amma “,yanzo kutashi muje can wajanta”.
Suka ce “,to”.
Tashi sukayi suka shaga mota, har Malam Usuman, Basu tsaya ko inaba sai k’ufar gidan.
Malam Usuman yafara shiga da sallamar sa sannan Suma suka bibayanshi.
Mufida ta ,amsa musu, dan lokacin tadawo dan daukar musu, abunda zasu affani.
Gaida Malam Usuman tayi, yakarba, “yace Ina Maryam take?”.
Tace “,batada lafiya yanzo, haka muna asbiti ankwantashe ta”.
Yace
“,Yaushe abun yasame ta?”.
“,Tace yanzo”.
Aliyu “,yace bayan fitar mu?”.
Ta”,eh”.
Nan take hankalinsu ya Ida tashi, a tare suka tambayar ta ,”wace hospital?”.
Fad’i musu tayi suka ce “tatasu sutafi”.
Dasauri tahad’a kayan ta tabisu suka tafi.
Koda su k’arasa cikin d’akin, gwaggo Maryam bacci takeyi, ita ko Hajiya Sa’a tana sallah.
Wuri suka Samu suka zauna suna masu nadama da bikin cikin abunda sukayi.
Hajiya Sa’a tana gama sallah Malam Usuman yace ,”Ashe ciyon Maryam tashi yayi?”.
Tace “,eh” Baba amma yanzo, da sauk”.
Yace “,Allah Kara sauki”
Take “, ameen”.
Sarai tagan su amma tayi kamar bata gansu ba.
Da day daya, suka fara gasheta ,amsamu su tayi kamar, bawani abunda ke faruwa.
Aliyu Yace “,yaya dan Allah kigafarce mu wallahi sharin shiad’a ne da sun zucya” .
Batace musu komai ba har suka gama abunda suke fad’a.
Gwaggo Maryam ita abbata farka ba sai daf da magarib lokacin Hajiya Sa’a tana sallah .
Ahankali, take bud’e ido, har Saida tagama bud’e idonta , abunda yafaru ta tunu tace,” tasan mafarkin da tasabayine basuna suka zogare taba.” tana Mai zubar da hawaye.
Bayan takammala sallah, alamun farkawar ta taji, dasauri ta k’arasu, tana ,”cewa gwaggo kin farka?”.
Hawayin dataga na zuba aidon ta yasata cewa “,gwaggo ko akwai wurin da ke miki ciyo?”.