KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

[10/9, 01:44] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

   Written by:✍????

         Anty Maimounath????

  Page1⃣

Dedicated to:Maman Ahmad

Imaan! Imaan! Imaan kina ina ne wai?na’am umma gani nan zuwa,

Wai bazaki fito kije wajen da na aike ki bane saï dare yayi ko,kuma kinsan halin abban ku idan ya dawo bai ganki ba fada zai yi ga yamma tanayi.

“” umma gani kayane nake sawa na gama.kaya kodai kwalliya ba,saï tayi dariya tace a a umma yanxu har wata kwalliya nayi

“” to naji dai yi maza kije ki dawo kafin abban naku ya dawo kinga lokacin dawowarshi ya kusa kin tsaya wani shafe shafe.murmushi ta sakeyi sannan ta fice tana cewa to umma saï na dawo.tace to a dawo lafiya ki gaishe min su.to umma.

“”Tafe take tana Sauri saboda ta dawo kafin magrub tayi kuma gashi bata samu abin hawa ba.kirrrrrrrr batai aune ba taji k’aran mota a bayan ta,saura k’iris motar Maimounath….waiwayawar da zatayi saï taga wasu dogarai a bayan ta.daya daga cikin su ne ya fara mata bala’i,” ke mahaukaciyar ina ce kina tafiya baki kallon hanya,wai

ku talakkawan nan me yake damun….bai karasa ba naji wani yayi magana ta bayana,yana cewa ke zo oga yana miki magana,na juya nace mishi wanene kuma oga kaje kace bazan zo ba.

Saï dayan dogarin yace ke hattara dai yarinya kinsan waye shi kuwa?tace ko ma waye bazan je…tsawa ya daka min keee fice muje kina bata masa lokaci.sum sum na fice daman karfin hali ne dan mugun tsoro ne dani????.

Da isar mû saï naga glass din motar yana zugewa har yayi kasa.subhanallahi na furta a cikin raina don ganin mutumen dake ciki.zan iya kiranshi da balarabe ma dan tsananin kyawun shi d’à farin shi,ga gashin kanshi nn baqi wulik irin na larabawa.

Hmm ba kowa bane face PRINCE SHUREIM……

da k’yar yake motsi dan tsananin mulki ni haushi ma ya bani,ina maganar zuci naji yace”hope u are fine babu abinda ya sameki ko?na kalleshi nace”eh.yace gud kina iya tafiya.hmm wani tsanar shi ma naji ta kamani wato iya abinda zai fada min Kenan ko,ni da aka kusa a kade bazai ban haquri ba.ni kuma nace yaushe zai iya baki haquri mutumen da magana ma wahala take mishi.nan daya daga cikin su ya biyoni y’a mik’omin bandir din kudi nace bana buqata ka mayar mishi.yace”ke rufamin asiri wa yake maida ma yarima kudi ai yanxu zan karb’i hukunci kuma ke sa’a ma kikayi da har ya tsaya don ke…

Wanene prince shureim?

Ku biyoni shafi na gaba danjin wanene.

Yar mutan kazay ce????
Anty Maimounath????
[10/9, 01:44] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

   Written by:✍????

        Anty Maimounath????

Decicated to:Maman Ahmad
(Mardiyya ka’oje)

Page2⃣

Prince shureim d’a ne ga sarkin garin yayi karatun shi ne a k’asar malaysia dan bai jima da dawowa ba.tun da ya gama primary school sarki ya kai shi can da zama.

Misk’iline na gaske dan bai cika son hayaniya ba dan shiyasa baya zama cikin mutane sosai.idan kaga yana hira da dariya to da abban sa ne wato sarki Kenan.

Su biyu kacal aka haifa a gidan su,shi da kanwar sa Nafeesat,ana kiranta da feenah.sarki yana matuk’ar ji dasu ba ma kamar yarima ba dan shi d’a ne mai biyayya…..


Cigaban labarin….

Imaan dai ta dage ita bazata karb’i kudin da yarima ya bata ba,shi kuma dan aike yana tsoron ya mayar masa ya kwashi hukuncin sa a hannu dan idan ya mayar shi ma yasan sauran..

Muna nan tsaye naga motar ta tsaya kusana,glass din motar ya zuge saï naga ya fidda glass din idonsa yy min magana a hankali,

“”Ni ba’a musu dani bare gaddama ke wacece da har ana baki abu kina yiwa mutane yanga””

“” dagowa nayi na kalleshi na murgud’a masa baki nace to ai bani nace ka bani ba,ko Dole ne saï na amsa””ina fadin haka nayi Sauri na fice daga wajen saboda magrub ta gabato kuma ina tsoron in iske abban mû ya dawo.

Da zuwa na gida kuwa nayi sa’a abba bai shigo ba.amma umma saï da tayi min fada,”’wai Imaan ina kika tsaya haka?

“” wallahi umma wasu ne suka kusa kad’eni da mota garin ina Sauri,
”’Umma ta zaro ido mota kuma su waye wannan?

“” baki ta fiddo,wai yarima ne dan sarkin garin nan dan naga har da dogarawa wai kamar shine sarkin kuma fa umma ko haquri basu bani ba saï kudi ne suka dauko suka bani ni kuma nak’i amsa na gudo gida.

Umma ta ce””yauwa y’ar albarka ai daman nasan bazaki amshi kudin su ba dan na yarda da tarbiyar da na baki.kici gaba da kare mutuncin ki na y’a mace kinji y’ata

Na ce””to umma insha Allahu zan kiyaye.

Khadijatul Imaan su hudu ne a gidansu.yaya Habeeb shi ne d’a babba a gidan mû,saï ni saï maryam da kuma dan autan mû khaleed…yaya habeeb ya gama makarantar shi yanxu haka yana Abuja can yake da zama tare da matar sa anty khaleesart da y’ay’ansu biyu ummi da fa’iz..
wannan Kenan.

Bangaren yarima kuwa suna isa gida kai tsaye bangaren shi ya fice yana shiga d’aki ya d’aga ma y’an bi bayanshi hannu alama yayi musu da su koma yana son ya huta ne.da shigar shi d’aki ya fada gado ya tsunduma kogin tunanin haduwarsu da imaan hmmm..lallai yau yarima ne da tunanin wata yarinya mutumen da y’an mata ke kawo mishi tallan kansu amma bai kulasu,yan mata masu aji ma,amma saï gashi ya fara tunanin wannan abar inji shi.oh god yarima ne yake fadin haka,wai meke shirin faruwa dani ne?

Ku biyo yar mutan kazay????

  Anty Maimounath????

[10/9, 01:44] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

Story & written by:✍????

    *Anty Maimounath*????

Da bazarmu writers association.

Happy birthday to u sister Maryam Ishaq. Allah ya albarkaci rayuwarki

Wannan shafin naki ne sister na.Allah ya barmu tare.

Page3⃣

Saï da aka kira sallah magrub sannan yarima ya tashi don gabatar da sallah,bayan ya gama yayi addu’o in shi a nan ya zauna bisa abin sallar yana karatun al’qur’ani mai girma har aka kira sallah isha’i.

Bayan ya gama ne yana zaune aka turo k’ofar d’akin aka shigo,yana dag’owa saï yaga umman shi ce,yayi murmushi yace””umma ke da kanki kika zo,ai da saï ki turo inje ko?

Tayi murmushi itama tace””a a ai ba komai ina son muyi magana ne shiyasa nazo nan din””.to umma da fatan dai ba laifi nayi ba ko dan naga duk maganar da zamuyi a b’angaren ki mukeyi.

Hmm d’ana Kenan karka damu bakayi laifin komai ba.

Yarima,umma ce ta kira sunan shi a hankali,ya d’ago yace””na’am umma””tace me yake faruwa ne naga yau sam baka da walwala tun da ka shigo ko wajena baka tsaya ba kai tsaye nan kazo,kuma ka kulle kanka a d’aki kai kad’ai meya sameka?fada min inji.babu komai umma yace da”ita”.

A a nasan halinka na misk’ilanci ko Abu yana damunka bakason fada,why?

Umma kaina ne kawai yake dan yimin ciwo amma nasha magani zai daina ma.a iya sanin da na maka yarima baka son shan magani.akwai dai wani abu kake boye min,to zan fada ma sarki shi ka fada masa ai.
Yarima yayi shiru bai yi magana ba.umma ma tashi tayi ta fice daga d’akin…

Misalin karfe 9:00pm na dare yarima ya amsa Kiran mai martaba wato mahaifinsa Kenan,

Bayan ya gaishe shi ya zauna kusa dashi,sarki yayi gyaran murya irin tasu ta manya yace””d’ana me ya sameka naji umman ku tace min tun da kuka dawo kake cikin d’aki?lafiya kuwa ?

Yarima yayi k’asa da kanshi yace””babu komai abba kawai ciwon kai ne kuma yanxu ya daina ma i’m fine.

To shikenan Allah ya kiyaye ka rinka shan maganin ka a kan lokaci kasan yanayin ciwon kai irin naka ko,

To abba zan kula

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button