KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Da haka ya samu tayi bacci bayan tayi ta mishi kukan shagwa6a,ya kwantar da ita ya mayar da abin ruwan zafin ya shiga toilet ya shanya tawul d’in tare da d’auro alwala yazo ya fara nafilfilin shi sai 3:30pm na koma bacci tare da rungume babyn shi,kai YARIMA akwai son yaji shi jikin mace hmm,

Da asuba ya kusa makara zuwa masallaci dan yana zuwa ana tayar da sallah,sakamakon a da kuwa yana can ake tayarwa,

Ko da ya dawo har yanxu tana bacci,da alama kuma taji sauqi,shiyasa ma bai tashe ta ba, tunda ba sallah take ba,zuwa yayi ya kwanta a bayanta har bacci yayi awon gaba dashi,sai 10am na safe IMAAN ta tashi,d’akinta taje daga nan ma toilet ta shige tayo wanka ta shirya,bata koma d’akin YARIMA ba,k’asa ta sauka,daga nan tayi kitchen dan yau tanaso tayi musu break fast da kanta,tea ta had’a Wanda yasha kayan k’amshi su citta da kanumfari ta duk ta had’a dasu,ta dawo ta sulala dankalin turawa ta fasa Kwaï tasa maggi, onga,da dai sauransu,sai da ta had’a komai ta shirya a dinning,ta hau sama,d’akin YARIMA ta nufa,da ta shiga bata ganshi ba,amma taji k’aran ruwa a toilet,wannan ya tabbatar mata cewa yana wa ka Kenan…

Tana zaune ya fito daga shi sai tawul,kauda fuskar ta tayi,dan bata son ganin shi ba kaya tsoro yake bata,hhhhh IMAAN Kenan,

Tace”the food is ready fa kai nake jira”,yace”banji ba,sai kin juyo kin kalleni sannan zanji”,tace”to sai ka sanya kaya tukun”,bata sani ba yayi sand’a yazo yace”to juyo ki kalleni na saka”,tana juyowa taga har yanxu bai sa kayan ba,ta saki ihu,saurin rufe mata bakinta yayi da nashi bakin sai da ya tsotse bakin tas sannan ya saketa,su duka suna maida numfashi,tashi tayi ta gudu dan ma kar yace zai sake mata,a falon ya isketa suka nufi wajen cin abinci, kallonta yayi ya ce”baby na kece da kanki kikayi mana break yau?”,tace”eh mana ni ce nayi”,yace”to ya ciwon cikin ya daina ko?”,tace”eh da sauk’i amma ina ji kad’an kad’an”,waya ya d’auka ya kira doctor mata ta gidansu,

Bayan ta d’auka ne yace”morning doctor ya kike?”,tace”morning YARIMA lafiya klau,ya madam”,yace”tana lafiya,plx magani nakeso ki aiko min na killer pain,ni babu a nan gida saboda na manta ne wlhy kuma sai gobe zanje asibiti”,tace”ok ba matsala ko ni da kaina zan iya kawo maka”,yace”ok thank u,sai kinzo d’in”,

Suna zaune a falo doctor tayi sallama ta shigo,bayan sun gaisa ne ta fiddo magani a jakar ta,ta bashi yace”nagode,wlhy jiya bamuyi bacci da wuri ba saboda ciwon cikin nata ne ya tashi,tace”ayya sorry madam,zai daina insha Allah daga ta haihu shikenan”,yace”insha Allah muna sa ran hakan,ai yanxu bai mata kamar na farko”,

Doctor bata jima ba tayi musu sallama ta tafi,ya kalli IMAAN yace”tashi d’auko ruwa kisha maganin,baki ta fiddo tace”nifa na warke”,yace”wane irin kin warke,to wlhy ko kisha ko inyi miki allura yanxun nan”,ai ba shiri ta tashi ta d’auko ruwan tasha”,dariya yayi yace”baby na akwai tsoron allura”,

Tace”akwai ciwo ne wlhy,ni ko sunanta banson ji”,janyota yayi ya rungume ya rad’a mata a kunne”kina tsoron allura idan kika zo haihuwa kuma fa?”,kanta ta cusa a k’irjinshi tace”banso ka daina”,to naji na daina idan time yayi kinyi min bayani ai,hhhh…….

‘YAR MUTAN KAZAY CE????

     *ANTY MAIMOUNATH*????

+22969164943

[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

       *STORY*
            *&*
           *WRITTEN BY:*✍????




     *ANTY MAIMOUNATH*????

DEDICATED TO:MY LUVLY FAMILY,I MISS U SO…SO MUCH…????????????????????

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page3⃣9⃣~4⃣0⃣

Wuni sukayi suna shan soyayyar su kasancewar babu aiki,da wannan ne yarima yake amfani wajen cusa ma IMAAN son shi,dan yanxu ta fara sakewa dashi ba kamar da ba,hmm yarima na daban ne cikin maza…

Tun k’arfe 7:00am na safe yarima ya tafi asibiti sakamakon aikin da gareshi sosai a can…yana zaune a office a lokacin k’arfe 11am ne,wata nos ce tayi knocking ta shigo office d’in,zuwa tayi ta tsaya batayi magana ba,yarima ya d’ago kanshi ya cire glass d’in da ke fuskar shi,yace mata”ya dai,lafiya kikazo kika tsare ni da idanu?”,kanta a k’asa tace”uhm…daman..ina neman wata alfarma ne”,fuska d’aure yace”alfarmar me?”,tace”daman kirana akayi daga gida mahaifiyata ce ba lafiya inaso in tafi gida”,yace”ok no problem kina iya zuwa,Allah ya bata lafiya”,tace”ameen na gode sir,ficewa tayi tanajin dad’i yau sunyi magana da yarima,kasancewar sun sani bai basu fuska ko kad’an,

Yarima kuwa binta yayi da ido,ya girgiza kai,yace wai me yake damun matan nan ne,dan ya tabbata ba wannan kawai ne ya kawo ta ba,tsoron fad’a ne tayi,murmushi yayi da ya tuna IMAAN d’inshi,yace my sweet baby kenan, ai ni ita kad’ai ta isheni rayuwa,she is my life,i can’t survive without her,hhhhh ni kuwa nace yarima ya zauce kan imaan, abinda bai tab’a tunani ba,wai shine yau yake nunawa mace so,hmm rayuwar Kenan ai…

Ba yarima ne ya koma gida ba saï wajen 8:00pm na dare,a lokacin kuma ‘yar rigimar tashi ta cika dan ganin bai dawo gida da wuri ba,hmm su imaan an san dad’in soyayya Kenan,ko da ya shigo da sallama da k’yar ta amsa gami da tashi tayi d’akin ta,hmm,murmushi yarima yayi dan ya gano laifin shi,binta yayi har d’akin nata,ya isketa a zaune bakin gado tana danna wayar ta,game takeyi,zuwa yayi ya zauna kusan ta yace”baby na yau babu sannu da zuwa ne?”,tace”ka koma inda ka fito saï ayi maka a can”,yarima rungumo ta yayi yace”haba baby na kinsan fa daga asibiti nake,ina kuma zanje?”,tace”oho wa ya sani dai”,yace”is ok,am so sorry baby na wlhy aiki ne yau nasha duk na gaji tashi mu tafi ki taimaka min inyi wanka saï muci abinci dan har yunwa na kawo”,zatayi magana ya d’ora hannunshi a bakinta yace”ya isa haka tashi mu tafi ko kuma inyi miki allura dan yau da kayan aiki nazo ban manta komai ba”,tace”ai na warke ban tsoro”,yace”are u serious kin warke,kina nufin bak’on ki ya tafi?”,tace”wane bak’o kuma?”,yace”bak’o mai hanani sakewa da baby na man,saï a nan ne ta gane nufinshi,rufe fuska tayi tace”a,a fa ban warke ba gaskiya”,yace”ok muje to”,

Tana zaune har ya gama wanka yasa k’ananan kaya sannan suka nufi k’asa dan cin abinci,bayan sun gama ne suna zaune a falo suna kallon t.v,wayar imaan tayi k’ara,tana dubawa saï taga ashe k’awarta jamila ce,d’auka tayi bayan sun gaisa jamila tace”yarima ya fad’a miki an sanya ranar auren mû?”,ihu imaan tayi Wanda saï da yarima yace”ke lafiya kike ihi?”,tace”ba komai,sannan ta cigaba da cewa”wai dan Allah da gaske kike an sanya ranar biki?”,jamila tace”ke wallahi da gaske nake miki nan da two weeks aka sa”,imaan tace”wayyo Ashe zamu sha biki budiri,to yaushe zakizo mû shirya yanda za’ayi dan kinga ba isasshen lokaci”,jamila tace”gobe ina nan zuwa insha Allah”,tace”OK Allah ya kaimu saï kinzo bye,bayan sun gama wayar ne ta juyo ta kalli yarima Wanda shi hankalin shi ma yana kan t.v,tace”shine baka fad’a min an sanya ranar bikin su naseer ba”,ya janyota ta fad’a k’irjinshi,yace”sorry mantawa nayi d’azu naseer ya kirani a waya ya fad’a min,kuma daga zuwa na kin tarbeni da fushi shiyasa na manta ai”,hmm su baby har an iya kishi,tace”ni ba kishi nake ba”,yace”to meye, cewa fa kikayi in koma inda na fito”,kyalewa tayi,yace”tashi mu tafi mû kwanta yau bacci nakeji da wuri,na gaji sosai,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button