KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Da isar su filin jirgin ba jimawa aka fara Kiran sunaye,imaan tana rungume jikin feenat suna kukan rabuwa da juna,

Mama ce take basu hak’uri ta kama imaan tace”’yata kiyi hak’uri kinji,ai kamar gobe ne zaku dawo,imaan dai sai ajiyar zuciya takeyi….

A daidai lokacin ne aka kirayi sunan su,ai fa kuka ya dawo sabo,da k’yar aka b’anb’are imaan a jikin feenat……

A cikin jirgin ma yarima yaci gaba da rarrashin ta,tayi lub a jikinshi…a d’ayan b’angaren ma wasu couple ne,amma su har da ‘yar su guda d’aya,suna kallon su imaan….

Matar ta kalli mijin nata tace”honey kalli wasu couple can sunyi matuk’ar birgeni,da alama amarya ce kuma ga ta k’arama da ita,

Dariya mijin nata yayi yace”dear kema ai yarinya ce,b’ata fuska tayi tace”haba honey nid’in ce yarinya,ni da har baby girl na haifa maka,

Yace”duk da haka,tunda har gobe kina tsorona,ta gane abinda yake nufi,

Kallon shi tayi a shagwabe tace”haka ma zaka ce koh,ai ina k’ok’ari ma,

Da suka isa malaysia imaan tana bacci a jikin yarima,sai da ya tashe ta….

A nan airport d’in sai da aymana tayi musu magana,tace”sannun ku dai”

Yarima ne ya amsa mata,sannan suka gaisa da mijinta,a nan yake ce ma yarima,ni sunana Mustapha matata kuma ummu aymana da ‘yar mu Haneefa,

Yarima yace”ok yayi kyau ni sunana shureim ana kirana da yarima,my nurul qalb kuma khadijatul imaan,

Nan ummu tazo kusan imaan tace”k’awata sannu ko,da alama kin gaji amma,

Nan dai suka shiga mota d’aya,hostel d’aya suka kama,sun zama friends,

Tunda suka zo imaan da tayi wanka ko abinci bata ci ba sai bacci…..babu yanda yarima bai yi da ita ba ta tashi taci abinci tace ita batajin yunwa…

Sai da lokacin sallar magrib tayi sannan ta tashi Dole badan bacci ya isheta ba..

Yarima kallon ta yake yana murmushi yace”my nurul qalb yadai nake ganinki wata iri Kodai….hmm

Tace”wallahi duk na gaji”,kin tabbata gajiya ce inji yarima,kai ta d’aga mishi,

Yace”zo nan in tambayeki wani abu,

Tasowa tayi daga abin sallah tazo kusa dashi ta zauna,jayota yayi ya rungumeta,a kunne ya rad’a mata yace”kodai nayi ajiyar baby ne yana magana yana shafa cikinta”,

Girgiza kanta tayi gami da cire hannun shi daga bisa cikinta tace”ni bani da komai,

Dariya yayi yana kallon ta yana wani tunani a ranshi….

Ko tunanin me? oho

Ku biyo ‘yar mutan kazay

          *Anty Maimounath*????

+22969164943
[16/10, 00:00] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

        *STORY*

                      *&*

                *WRITTEN BY*:✍????


       *ANTY MAIMOUNATH*????

PERFECT WRITERS FORUM
????P.W.F????

VOTRE SOUTIENT ÇA ME VA VRAIMENT AU CŒUR, MERCI BEAUCOUP JE VOUS AIMES TOUS????????????

DEDICATED TO:
MAMAN AHMAD(MARDIYYA KAO’JE)
RAHEENAT NIAMEY (NIGER)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page1⃣9⃣~2⃣0⃣

IMAAN sai da taji kunya dan ganin irin kallon da yake mata,yarima kuwa tunani yake a matsayin shi na kwararren likita yanaso ya gano abinda ke damunta,

Kamota yayi yace”fad’a min gaskiya bakijin wani canji a jikinki”girgiza kai tayi tace”kawai gajiya ce nakeji,

Ya lak’uce mata hanci yace”gajiyar nan fa kar ta hana min sakewa in anjima”,

6oye fuskar ta tayi a k’irjinshi dan ta gane nufin shi,hmm kai YARIMA akwai naci,

Ya d’ago ta ya kama fuskar ta yace”bud’e idon ai gaskiya ce na fad’a”,

Tashi, mu gabatar da sallah isha’i,ta shi tayi yaja musu jam’i sukayi yayi musu addu’a sosai…..

Ko da sukazo kwanciya bacci YARIMA fa yace sai ya d’an huta da IMAAN d’in tashi,ita kuma babu yanda ta iya haka dai ta daure ta bashi hakk’inshi….

Shi kanshi PRINCE bai son yana takura mata,amma haka kawai yakejin bazai iya jurewa ba,duk da gajiyar da sukayi….

Sai da yayi around biyu sannan ya kyaleta,Allah sarki IMAAN….

Da asuba,Bayan sunyi sallah sun koma bisa gado nan YARIMA yake sunsunar ta,nan fa tayi rau rau da ido dan ba k’aramar gajiya takeji ba,amma shi YARIMA ya dage sai ya k’ara,cabb..

Hannu yasa cikin rigar ta yana wasa da k’irjinta,ita dai saurare takeyi,a kunne ya rad’a mata cewa”bakiso ko nurul qalb,kiyi hak’uri,bazan yi miki ba tunda bakiso amma plx ki barni inyi wasa da ke dan in samu nutsuwa…

Duk yabi ya takura ta da shafe shafe,da kuma kiss,hannu yasa ya fidda mata rigar,ganin dukiyar fulanin ta ya saka shi cikin wani hali,baki ya dasa a k’irjin ta,tsotsa yake cikin kwarewa a soyayya,ita kanta IMAAN abin sai yayi mata dad’i????

Sai miqa takeyi alamar saqonnin YARIMA suna isar mata,hannu yasa a marar ta cikin wata irin voice yace”you know i can’t endure it,plx ki yarda inyi ko da kad’an ne”,

Nan dai yayi ta mata kalamai masu ratsa zuciya har ya samu kanta,shawo kanta ba wuya kasancewar ta yarinya da bata san komai ba..

YARIMA albarka yake ta sa mata har bacci ya daukesu…

~~~

Ranar da suka cika sati d’aya a malaysia,YARIMA ne ya shirya dan zuwa clinic d’in da ya saba zuwa tun yana nan k’asar,IMAAN ce ta marairaice mishi tace sai ta bishi,hak’uri yake bata yace zai kaita b’angarensu UMMU AYMANA ta zauna can har ya dawo,

Hakan kuwa akayi,da ya gama shirin shi itama tasa kayanta ta saka hijab,suka fice zuwa can,yace musu yana son IMAAN ta zauna har ya dawo……

Ba YARIMA ne ya dawo ba sai kusan sallah azahar,a lokacin su IMAAN suna ta hirar su ita da UMMU AYMANA…ko da ya zo su tafi banza tayi dashi daman ta kumbura kamar ta fashe,wai ita a dole fushi takeyi saboda ya tafi ya barta,ni kuma nace toh su IMAAN ke da baki sonshi ina ruwanki da inda zaije,hmm muje zuwa dai….

Da suka isa b’angaren su,ya kalleta yace”nurl qalbi na yadai nake ganinki haka?,fushi ne kikeyi dani ko?”d’agowa tayi suka had’a ido tayi saurin kauda idon ta,

Yace”kiyi hak’uri ai daga asibitin banje ko ina ba”,bari inyi wanka muyi sallah in na huta zuwa anjima zamu fita in zaga dake kiga gari kinji koh?”

IMAAN kanta kawai ta d’aga mishi,yaja hannunta suka shiga d’akin baccin su…

Da yamma ne suka fita yawon shak’atawa,sun zaga gari sosai inda suka je wani had’add’en super market yace ta d’auki abinda takeso,kayan zaqi ne kawai ta kwana shi dai kallon ta kawai yakeyi ko me zatayi da wannan kayan zaqin,hmm

Daga nan kuwa wani shago na sayar da kayan mata ya kaita,nan ma yace ta zab’i kayan bacci masu kyau dan ya lura bata kawo nata dayawa bâ…kunyar za6e taji,yazo kusanta a hankali yace mata”ya kika tsaya?”

Rufe fuskar ta tayi da hannu,murmushi yayi yace”hmm su baby sarkin kunya,to bari ni in za6a miki,

Kayan da ya kwasar mata mamakin shi ta shigayi,kamar ba da kud’i ake sayen su ba ko ciwon fiddasu bai yi,hmm IMAAN kenan karki manta shi fa ba irin k’ananun mutane bane,tasu daban ce ba irin…

Ko da suka dawo masaukin su,wanka sukayi suka gabatar da sallah magrib,suna zaune suna kallo akayi musu knocking YARIMA ne ya amsa da”yes come in”su MUSTAPHA ne da ‘yarsu suka shigo,

Waje suka nema suka zauna aka ci gaba da kallo suna hirar su kuma,a nan ne YARIMA yake fad’a ma MUSTAPHA cewa d’azun yaje ganin doctor ne saboda matsalar kanshi yacekwana hud’u aka bashi ya koma ,nan yayi mishi fatan alkhairi yace”Allah ya bada sa’ar aikin”,ameen inji YARIMA,

UMMU AYMANA kuwa jan hannun IMAAN tayi tace”k’awata muje mu barsu suyi hirar su,b’angarensu ummu suka nufa….

A cikin hirar tasu ne UMMU ta kalli IMAAN tace”k’awata da alama mun samu k’aruwa ko?”kallonta IMAAN tayi dan bata gane nufinta ba,tace”anty kamar ya?ban gane ba,dariya UMMU AYMANA tayi sannan tace”ina nufin anya ba ciki bane gareki?”IMAAN ta zaro ido tace”ciki kuma anty,a a ni bani da komai”,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button