KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Imaan dai babu bakin magana jikinta kuwa yana k’arb’ar sak’on da yarima yake aikawa,toh fa jama’a yarima fa ya zauce har ya kasa controling kansa,kukan imaan ne ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi,hmm yarima Kenan ko ya manta a halin da imaan take ne…hak’uri ya shiga bata yana cewa”baby na sorry ba abinda kike nufi bane,ta yaya zan kusanceki kina rashin sallah,kawai nayi haka ne dan in samu nutsuwa”,imaan dai ba magana tayi lamo a k’irjin shi kunya takeji hmm,ya k’ara cewa”baby na kiyi hak’uri nasan ina takura miki,wallahi ban iya controling kaina idan ina kusanki so ki k’ara hak’uri dani kinji,ita dai ta kifa kanta a bisa pillow tana sauraren shi….yarima tashi yayi ya sake yin wani wankan????bayan ya fito yasa kananan kaya yazo ya zauna bisa bakin gadon yace”baby na tashi muyi magana”,tashi tayi zaune suka had’a ido sai ta kauda kan ta,murmishi yarima yayi yasan kunya ce takeji,yace”baby daman inaso in fad’a miki zamuyi tafiya ni da ke malaysia nan da two weeks,saurin d’ago kai imaan tayi tace”karatu na fa?”yace”xakiyi baby na amma ba yanxu ba”,tace”imaan tace”kamar ya nidai skull d’ina zanyi ka tafi kai kad’ai”,kallon ta yarima yakeyi yanda take maganar yace”zonan in biya wannan shagwab’ar yasa hannu ya janyo ta…….
‘yar mutan kazay ce????
*Anty Maimounath*????
[12/10, 19:24] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:✍????
*Anty Maimounath*????
PERFECT WRITERS FORUM
????P.W.F????
wannan shafin nakune ‘yan grp kwalliya adoce,ban manta daku ba,kuna a raina,grp mai hadin kai Allah kara mana kaunar junan mu.ameen!!!
Luv u all????????????
Dedicated to:
Mom Abdul
Mom khaleepha
Mom Ansar
jiddah santee
zeemom amarya
zee yakubu Dewu
Ayshat 2
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page1⃣4⃣
Hannu yasa ya janyo ta yana cewa”ya akayi ne,ai nace zakiyi meye kuma b’ata rai haka,imaan tace”ni yanxu nakeso saura one week mu koma fa,kowa yana zuwa skull ban da ni,yace”to me kika rasa a gidan nan uhm?”ta kyale,yace”inajinki fad’i abinda kika rasa,baki ta turo tace”ni ba wannan ba,inada burin zama likita ne,duk k’awayena suna zuwa skull sai ni kad’ai za’ace ba xani ba”,yarima kallon ta yake sai da ta gama sannan yace”to naji ya isa haka karkiyi min kuka,ke mai arhar hawaye,idan kika sake hawayen nan ya fito sai nasa baki na tsotse shi,tanajin haka tayi saurin goge hawayen,yarima dariya yayi yace”baby kin cika tsoro fa”,itadai batayi magana ba…tashi tayi tace”zanje d’aki”,yace”nan ma ai d’akina ne”,d’akina nake nufi,yauwa na manta ban tambayeki ba,kwana nawa kikeyi in kina menses(al’ada)din ki,shiru tayi,yace”ina tambayar ki kinyi shiru,i hate in ina magana a yi min shiru ya k’arasa maganar cikin tsuke fuska”,a hankali tace”kwana 5”,zaro ido yayi 5 baby duk ma yau ne kika fara,oh god ya fada gami da dafe kanshi,imaan dai kallon shi takeyi….
~~~~~~
Yarima yana k’irge da kwanakin da imaan tayi tana al’ada,a kwana na shidda ne ya isko ta tana sallar azahar,zama yayi bakin gadon ta har ta gama ta shafa,amma sai tak’i tashi dan cike take da fargaba dan tasan halin yarima yanxu yace zai yi mata wani abin,haka kuwa akayi,da yaga tak’i tashi sai yazo har inda take ya rungumo ta ta bayanta yana cewa”har yanxu baki gama bane ai naga kin shafa fatiha,sai me kuma yayi saura,ai ya kamata azo a kula dani ko”,nan fa ta k’ara tsorata,zatayi magana ya hanata sakamakon bakinshi da ya dasa a nata,daga nan kuma ya sureta bai dire ta a ko ina ba sai bisa gado,soyayya mai wuyar fassarawa,kissing din ta yakeyi ba k’akk’autawa hannu yasa ya fidda mata riga shima ya fidda tashi,hannu ya d’ora bisa kan….nidai da gudu na fito,amma dan son jin gulma irin na ummu basheer ta turani d’akin wai in d’auko rahoto????ni dai ba ruwana…
Ko da na koma na tarda yarima ya kama komai,saboda bai son takura mata wannan ma dole ne saboda yana jin wani irin yanayi in yana tare da ita,imaan kuwa a ranta cewa take wannan wane irin mutum ne da baya gajiya kullum Abu d’aya dai ni dai gsky na gaji a haka zan bishi ya kasheni a k’asar mutane,tana wannan zancen zuccin har bacci ya d’auketa,basu tashi ba sai da aka kira sallar la’asar,ita ta fara tashi taje tayi wanka ta d’auro alwala ko da ta fito yarima bai farka ba,ta rasa yanda zatayi ta tashe shi itadai kunyar shi takeyi,hmm imaan Kenan,ta matso bakin gadon ta d’an bubbuga pillow da kanshi yake bisa,shiru dai da ta tab’ashi sannan ya d’an bude ido ya kalleta ta kauda kanta sannan tace”lokacin sallah yayi,(gareki yake ‘yar uwa ya kamata ki koyi yanda ake tashin maigida daga bacci ba wai zuwa xakiyi ki ta bubbuga mishi pillow ko kafafuwa ba,a a namiji bai son haka,zuwa zakiyi ki zauna bakin gadon daidai fuskar shi ki rink’a wasa da hannunki bisa fuskar shi….)
Kallonta yarima yakeyi yana murmushi shidai birgeshi takeyi idan tana magana cikin sanyin murya takeyi,wani lokacin shi yake tada mishi sha’awar ya kusance ta,toh fa…tashi yayi ya shiga toilet ita kuma ta fara sallar ta,tana sallamewa yana fitowa daga toilet, shi dai yanason fitowa ba kaya daga toilet inji imaan,sunkuyar da kanta tayi tana zaune tana ‘yan addu’o’in ta har ya gama shiryawa ya fita waje……..
Da dare ma yarima yace zai k’ara,imaan kuwa tace nan fa d’aya,har ya kai yarima ya fusata yana cewa”zaki haramta min abinda Allah ya halatta min ne,komai naki na kuka ne ni da hakk’i na ko so nawa zan nemeki a rana akwai mai tuhuma ta yace dan meyasa,sai anyi magana kice ciwo kikeji,yanxu na gane cewa ba ciwo ne kikeji ba….yana fad’a imaan kuma duk ta tsorata da yanayin shi sai kuka takeyi….ko kallon ta yarima bai yi ba ya tashi ya fice daga d’akin,toh fa ran maza ya b’aci kenan….imaan kuwa yana fita ta rasa yanda zatayi saboda tunowa da tayi a makarantar su ance musu duk matar da take gudun shimfid’ar mijinta to sai ta kwana mala’iku suna tsine mata(wa’iyazubillahi????)tashi tayi ta d’aura Zani bisa kan doguwar rigar baccin ta,ta sanya hijabi ta nufi d’akin yarima zuciyar ta cike da fargaba tana tsoron taje bashi hak’uri ya dake ta,a lokacin k’arfe 12pm na dare saura kwata,
Knocking tayi shiru ba magana,tura k’ofar tayi gabanta sai fad’uwa yake,bisa gado ta hangoshi yana danne danne a labtop(ordinateur, systèm)din shi,takowa tayi har kusan gadon ta durk’usa tana wasa da d’an yatsanta ta kasa mishi magana yarima ne ya waiwayo ya kalleta yace”lafiya me ya faru?”inda inda ta fara”uhm hmm…daman zuwa nayi in baka hak’uri dan Allah kayi hak’uri ka yafeni,bazan sake”,ya wuce kawai yace da ita,hmm yau k’asaitar ta tashi Kenan haka imaan ta fad’a a ranta,shiru sukayi na d’an wani lokaci,yarima ne ya juyo yace”da akwai wata matsalar ne?”girgiza kai tayi,sai kuma ta fara hawaye ya kalleta yace”tashi ki fita min a d’aki karki yi min kuka a nan”,tashi tayi ta fita da Sauri tana kuka….bin bayanta da ido yayi ya dafe kanshi yace”oh my god ita komai nata na kuka ne,yanajin kukan ta har cikin ranshi amma kuma miskilancin shi ya hana ya bita ya rarrashe ta………
manej plx need ur prayers????????????????????
*'yar mutan kazay ce*????
*Anty Maimounath*????
+22969164943
[14/10, 00:09] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:✍????