KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

UMMU AYMANA tace”to bari inada abin gwajin ciki zamuyi sai mu gani,
IMAAN tace”in ciki ne na shiga uku,ina Zani da ciki ina ‘yar k’arama dani,
UMMU tace”to meye dan kinyi ciki,ai ba shege bane da ubansa kuma ko YARIMA zaiji dad’i sosai,ta kalleta tace”anty karatu na fa?”
Tace mata”ciki bazai hanaki karatunki ba,to wai ma yanxu bakijin wani chanji ne a jikinki?”
IMAAN ta kalleta sannan tace”a a inajin gajiya dai kawai,ita d’in ma nasan saboda tafiyar da mukayi ne….
Sunayin test d’in kuwa ya nuna alamar shigar ciki,haba me IMAAN zatayi in ba kuka ba,tanayi UMMU tana bata hak’uri cewa”haba k’awata bakison ki haihu kema kamar na kowa,karki manta YARIMA dan sarauta ne kuma kince min shi kad’ai ne d’a namiji a gidansu,to kinsan ma meye hik’imar turo ku honeymoon kuwa?to irin wannan rana sukeso tazo kuma na tabbatar zasuyi murna sosai fiye da yanda baki zato,
Ta tsagaita kukan sai sharar hawaye take…
Su MUSTAPHA ne sukayi sallama suka shigo,IMAAN tayi saurin goge idon ta,
MUSTAPHA ya kalli UMMU yace”ke haka akeyi kin rik’e mishi amaryar shi,in kuka samu hira baku leqa lokaci,
Sai a lokacin ta kalli wayar da take hannunta taga wajen 10pm,tace”kai ashe dare ya fara,ango kaina bisa wuyana,
Dariya YARIMA yayi sai yace”ba komai madam,ya juyo yace ma IMAAN baby na tashi mu tafi sashen mu,
IMAAN sai da taji kunya,shi kuwa YARIMA ba ruwanshi a gaban kowa ma soyayyar shi yake nunawa…
Suna shiga ya kalleta cikin ido yace”baby na Meya sameki naga idon ki kamar kinyi kuka?”
Ai daman kamar jira takeyi,nan da nan sai ta fara kuka,YARIMA ya rikice yana tambayarta ko sunyi wani abu ne ita da UMMU, girgiza mishi kai tayi,kamata yayi suka zauna a kujera yana share mata hawaye..
Tashi yayi ya d’auko yagot a firij(frigo) ya dawo yace ta bud’e bakinta ya bata tasha,tana kauda kai ma tad’an sha kad’an,amma me ai tana sha ta sai amai yazo mata da gudu ta shiga d’akin baccin su ta wuce toilet….
Amai take ta kwarawa kamar zata amayar da hancin cikinta,YARIMA yana dafe sa ita yana cewa”sannu baby na,sannu kinji,d’aga mishi kai takeyi sai nishi take yi kuma dan wahala,Allah sarki nima na tausaya ma IMAAN,
Da ta gama ta wanke bakinta da fuskar ta suka dawo d’aki,YARIMA ne yake ce mata”me ya saki amai, ko yagot d’in ne bakiso?”Eh tace dashi,
To yanxu fad’a min abinda ya saki kuka d’azu,
A shagwa6e tace”ba anty ce ba tace min wai ciki gareni,ta k’arashe maganar cikin zubda hawaye”,
Murmushi yayi yace”to shine abin kuka wasa take miki ai”,shi kuwa ya fad’i hakan ne dan ta kwantar da hankalinta dan shi kanshi yana zargin haka,dadi cike cikinshi amma bai nuna ba,
Tace”ai har da gwajin fitsari tayi min tace shine”,YARIMA yayi jim kad’an yace”likita ce kenan?”eh ta amsa mai,
Yace mata”to kiyi hak’uri muje kici abinci gobe zamuje clinic a duba ki kinji?”tace”to gami da share hawayen ta…
Cikin dare zaxxa6i yace ma IMAAN gani gareki,karkarwar sanyi takeyi har sai da YARIMA ya kashe a.c ya lullu6e ta da bargo….
Basuyi wani baccin kirki ba har aka kira sallar asuba,ya tashi yayi sallah sannan ya tashe ta tayi sallah d’à k’yar shima a zaune,toh fa abin karau ya samu wai anyi wa makauniya wacila????
Komawa tayi ta kwanta a gado,YARIMA yazo ya dafa jikinta yaji har yanxu akwai zaxxa6in yace”sannu baby na,bari in had’a miki tea anjima mu tafi clinic d’in…fita yayi yaje ya had’o mata tea d’in ya dawo ya ce ta tashi tasha sai ya bata magani kafin suje asibitin,
Tashi tayi tasha kad’an ya bata maganin sannan ta koma ta kwanta,ya hayo gadon ya rungumeta yace”a samo miki wani abu mai d’an nauyi kinga asibiti zamu kuma allura zasu miki,tashi tayi daga jikinshi tace”ni banson allura kar ayi min”,yace”hak’uri zakiyi a miki ki samu sauk’i kinajin yanda jikinki yake da zafi,
Kukan shagwa6a ta fara mishi tana cewa”ni ba sai munje ba,na samu sauk’i,
~~ ~~
Karfe 9am a asibiti tayi musu,sai da YARIMA ya fara ganin doctor yayi mishi bayanin cewa yana zaton cikine da IMAAN amma in ya aunata kar ya fad’a a gabanta….hmm
Sai da suka jira result d’in ya fito,sai da doctor yayi ‘yan rubuce rubucen shi sannan ya kalli YARIMA yace”ba komai ne yake damunta ba sai gajiya da kuma sauyin wuri,IMAAN dad’i taji an ce bata da ciki,hhhh yarinta kenan,
Allura akayi mata saboda zaxxa6in,YARIMA ne yace da ita ta zauna a nan yana zuwa,
Fita sukayi shi da doctor,YARIMA ya kalli doctor yace”ya me ka gani?”hannu ya mik’a mishi yana cewa”congratulation friend ka kusa zama dady,she is pregnancy”,haba me YARIMA zaiyi in ba murna ba,shi daman yayi zargin hakan,yace”doctor na week nawa ne?”doctor yace”sorry ashe ban fad’a maka ba,two weeks,amma ka bi a hankali fa friend”,
YARIMA yace”ban gane nufinka ba?”dariya yayi mishi sannan yace”friend ina nufin karka kusance ta ka bari zuwa d’an wani lokaci”,
YARIMA yace”why doctor?”,yace”saboda akwai ‘yar matsala kad’an amma karka damu ba wani abu,wannan magungunan idan tana shan su komai zaiyi daidai kaga yarinya ce sosai”,YARIMA yace”to har zuwa wane lokaci kenan dan kaima kasan yanda nake fa,wlh yanxu haka a matse nake”,kafad’ar shi doctor ya bubbuga yace”karka damu ko zuwa 2 weeks ne,saboda a binciken da nayi cikin na iya zubewa in har kace zaka kusanceta”,kallon shi YARIMA yayi yace”ok ba matsala zan jure tunda larura ce”,doctor yace”ok,kuma karka manta cewa jibi ne aikin naka,ai bazan manta ba insha Allah..
Baku tambayeni wanene doctor nan ba,ya akayi ya iya hausa alhalin yana zaune a turai?
KU BIYO ‘YAR MUTAN KAZAY????
*ANTY MAIMOUNATH*????
+22969164943
[18/10, 01:53] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY*:✍????
*ANTY MAIMOUNATH*????
PERFECT WRITERS FORUM
????P.W.F????
KHADIJATUL IMAAN FAN’S INA MATUKAR GODIYA DA SOYAYYAR KU,MASU BINA PRVT IDAN BANYI MUKU REPLY BA PLX KUYI MIN UZIRI INA BUZY NE TNX,LUV U ALL????????????
YANXU NASAN CEWA BA SURBAJO KADAI AKE ZAGI BA,HAR DA SAURAN WRITERS,WANI YACE INA DAB DA FARA IRIN ABINDA SURBAJO KEYI,YA KUMA CE KOWA YA TASHI ISKANCIN SHI SAI YA FARA RUBUTUN NOVELS
TARBIYYA DAGA GIDA TAKE TASHI INDAI HAR MUTUM YANADA ITA BABU WANDA YA ISA YA SAUYA MISHI,BA’A CE DOLE MUTUM YA KARANTA BA,NOVELS DIN SURBAJO BAZAI BATA TARBIYAR MUTUM BA SAI DAI IN DAMAN CAN MUTUM BASHI DA ITA,PLX KU BAR MUTANE SUYI ABINDA SUKA GA DAMA,KOWA YAYI LIFE DINSHI,PLX,PLX ND PLX????????????
DEDICATED TO:
MAMAN AHMAD(mardiyya ka’oje)
MAMAN IMAAN(Elina)
MAMAN FAIRUZA
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page2⃣1⃣~2⃣2⃣
Doctor MAHMUD IBRAHIM,haifaffen d’an najeriya ne,an haifeshi a garin Gombe baban shi bahaushe ne mahaifiyarshi ce bafillatana,aiki ya kawo babanshi Gombe a nan ne yaga mahaifiyar shi har sukayi aure,suka haifi ‘ya’yansu biyar, MAHMUD ne babba a gidan su saï kannunshi,AYSHAT,FATEEMA,ANISA da kuma ALIYU dan autan su…MAHMUD fari ne kyakkyawan gaske da ka ganshi to kasan yanada alaqa da fulani,yana da matar shi d’aya BILKISSU da ‘yarsu kausar,aiki ne yakeyi a can k’asar ta malaysia,da ya gama karatu saï turawa suka rok’eshi da ya zauna yayi musu aiki saboda hazak’ar shi,shi ma YARIMA babu abinda basu yi ba ya zauna yace shi yana kishin k’asar shi bazai zauna bâ,a nan ne suka san juna da doctor MAHMUD,amma shi doctor yana gabansu YARIMA dan har ya fara aiki sannan su suka ida nasu karatun…wannan Kenan…