KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Cigaban labarin…..
Ko da suka dawo har lokacin sallah azahar yayi,sai da suka gabatar da sallah sannan suka ci abincin da UMMU AYMANA ta kawo musu,sai dai IMAAN tana ci ta amayar da shi,YARIMA yace ta fad’i abinda ranta yakeso yaje ya kawo mata,wai ita d’an wake takeso hhhh ina zaki samu d’an wake a nan,ido ya zaro yace”baby na a ina zan samo shi ai ba’a sayarwa a nan k’asar,please canza wani abun,ai kuwa ta fara mishi kukan shagwa6a ita shi kawai takeso,da k’yar ya rarrashe ta ya bata kaza da yagot yace taci wannan kafin ya kawo mata d’an waken,ba laifi ta dan ci tasha magani daga nan sai bacci abinka da mai yaron ciki….
Ajiyar zuciya yayi yace”ai kuma na shiga uku,dan ya lura cikin zai dan bata wahala kuma irin mai laulayi ne da sa mutum tsirfa da Saurin fushi kuma”,wai lallai YARIMA anji jiki kam..
waya ya d’auka ya kira gida yake fad’a ma mama cewa IMAAN ba lafiya,maman ta rikice tace”what?to maza ku dawo gida kasa ‘yar mutane gaba kana kallo ciwo ya shigeta,to wai me ya sameta ne?”,YARIMA ya Sosa kai kamar yana gabanta yace”mama munje asibitin da nake zuwa…uhm sai kuma yayi shiru”,maman tace”to me akace muku?ya Kayi shiru,fad’a min mana”,YARIMA yace”uhm doctor yace tana da juna biyu amma yana d’an wahalar da ita ne”,
Haba me mama zatayi in ba murna ba,kamar anyi mata da busharar shiga aljannah,fad’i take alhmdllh Allah na gode maka, ina ita IMAAN d’in bata mu gaisa”,
YARIMA yace”a a mama rufa min asiri kar taji cewa tanada ciki wlhy rigima zaki jayomin,yanxu ma da ya na k’are,yanxu ta gama kukan ita sai na samo mata d’an wake,da k’yar na samu tayi bacci,
Mama tace”to ku dawo gida ya isa haka nan honeymoon ya k’are kuma tunda an samo min jika”,duk da ba a gabanta yake ba,amma sai da yaji kunya”,yace”mama doctor yace cikin yazo da ‘yar matsala ne ba’ason abinda zatayi wani Abu na k’arfi kinga Kenan zancen zuwa bai taso ba,kiyi hak’uri ta samu ko one month ne”,
Mama ta nisa tace”to shikenan Allah ya nuna mana,yanxu cikin satin shi nawa ne?”kai mama da son sa mutum kunya take,YARIMA ne yake fad’in haka cikin ranshi,sannan yace”just two weeks ne”,
Nan dai suka ta6a hirar su ta tsakanin uwa d’anta sukayi sallama…haka dai YARIMA yayi ta kiran Wanda yasan yanada kusanci dashi ya fad’a musu abin farin cikin da ya same shi,ciki kuwa har da su anty khaleesert da Jamila tare da cewa bayason IMAAN ta sani kar su fad’a mata,suka ce ba damuwa kowa yayi murna,amma uwar gayyar batasan wainar da ake toyawa ba,hmm lallai YARIMA sarkin zumud’i,cikin two weeks har ya fad’awa jama’a,hhhh….
Sai da lokacin sallah la’asar yayi sannan ya tasheta shima ba dan yaso ba,sai dan tayi sallah ne,ai kuwa tana gama sallah ta dasa mishi kuka ita kawai a nemo mata d’an wake,YARIMA dafe kai yayi a ranshi yana cewa Ashe bata manta ba,hmm to ya zata manta abinda takeso,malam tashi la nemo kawai tunda ka had’ata da aiki..
Kamota yayi ya rungume yace”baby na yi hak’uri mana,na zagaya ko’ina ban samu ba a nan basu sayarwa ne,yi shiru ki daina kukan ya isa haka zai sa miki ciwon kai”,cikin shagwa6a tace”to mu koma gida ai a can akwai”,
Yace”to naji amma ba yanxu ba,bari inje b’angarensu MUSTAPHA ko zan samu abinda zakici”,nan ma tace sai dai su tafi tare,yace”to tashi mu tafi”,
Da sallamar su suka shiga falon nasu,sun taddasu suna zaune suna kallo,YARIMA ya mik’awa MUSTAPHA hannu suka gaisa,sai ya kalli UMMU AYMANA yace”ki taimakeni ki rabani da rigimar nan”,ta kalleshi kamar ya,me ya faru?,yace”IMAAN d’ina takeson d’an wake tun d’azu take min rigima,ki taimaka ko na fulawa ne kiyi mata”,
Dariya tayi tace”to shikenan ba matsala, anyi sa’a ma nazo dashi daga gida har da yajin,YARIMA yace”dan Allah fa?kai amma yau kin fanshe ni,ai da babu ni babu baccin dare”,a kunyace IMAAN tace”to anty muje muyi d’an waken”,nan suka tashi suka nufi Kitchen d’in…..hmm su IMAAN fa an samu abinda akeso,d’an wake da mai da yaji,hhhh
Cikin bacci YARIMA ya lalubo ta,ya rungume ta,ta bayanta ya tura hannunshi cikin ‘yar yaloluwar rigar baccin ta,ya fara wasa da k’irjinta,a cewar shi ko zai rage zafi????
Yana cikin yi ne ta motsa,sai taji hannun mutum bisa k’irjinta,ture hannun ta shiga yi,a shagwa6e ta ke cewa”ni banso karkayi min bacci nakeji”,a hankali YARIMA yace mata”haba baby na baki ko tausaya min,ba abinda kike nufi bane zanyi,kawai iya nan zan tsaya,a matse nake,kiyi hak’uri har un samu nutsuwa”,zata sake magana ya juyo ta ya dasa bakinshi kan…..
~ ~~~~
Yau ta kama ranar da YARIMA zai koma asibiti,ya kai IMAAN b’angarensu UMMU tare ma suka tafi da MUSTAPHA….da isar su ma ba wuya abinka da harkar kud’i,nan da nan aka shiga d’akin aiki da shi inda za’a duba mishi kwakwalwar shi,likitoci sun kai ruwa rana kafin su shawo kan matsalar,amma alhmdllh komai ya zama normal,sai dai za’a kwantar dashi yayi two dans(kwana biyu)a nan asibiti…..
*ONE HOUR LATER*
Ko da YARIMA ya farfad’o cewa yayi kawo mishi IMAAN d’inshi nan,MUSTAPHA ne ya koma yazo dasu duka,ai kuwa suna shiga ko da IMAAN taga YARIMA kwance sai ta fad’a jikinshi tana kuka,ta ma manta da cewa ita fa ba sonshi take ba,hhhh,IMAAN Kenan so na nawa kuma,bayan ga so k’arara ina gani a kwayar idonki,ai kema UMMU BASHEER kin gani koh?
Da k’yar suka lallashe ta tayi shiru….nan dai suka wuni sai dare suka fice,IMAAN tace ita a nan zata zauna,aka ce mata ba’a buqatar d’an jinya a nan,nan ma wata sabuwar rigimar ce sai da YARIMA yace”baby na,kiyi hak’uri ku tafi da safe sai a kawo ki kinji,karki damu zan samu lafiya ai,ba gashi ina hira ba,da haka aka samu kanta….
Da safe kuwa IMAAN tunda tayi sallah ko break fast kin yi tayi,tace ita dai a kaita wajen mijinta,toh fa IMAAN fa ta kamu da son YARIMA amma yarinta ta hana ta gane hakan….da k’yar ta bari k’arfe 8am tayi,yau d’in ma su dukansu suka tafi asibitin inda IMAAN take d’auke da HANEEFAH ‘yar UMMU AYMANA Kenan,inda ita kuma UMMU ke d’auke da breakfast d’in YARIMA,suka shiga d’akin da aka kwantar dashi tare da yin sallama….
Ko da suka shiga yana zaune yana danne danne a wayar shi,yana ganin su yayi murmushi yace”ai da yanxu zan kira ku ince a kawo min baby na”,dariya MUSTAPHA yayi yace”to kud’inka sun huta ba sai ka kira ba gatanan,hannu ya bude yace”zo nan baby na,takawa tayi a hankali taje wajenshi,amma kunya ta hana ta shige hannun shi,sai ta zauna a kusan shi ta gaishe shi tana mishi ya jiki,sun shagala…MUSTAPHA ne yayi gyaran murya yace”to in ka ida da madam ai sai ka juyo mû gaisa ko,IMAAN kunya taji,inda YARIMA ko a jikinshi dariya yayi yace”am srry abokina kasan in ina ganin ta ban ganin komai a gabana”,a nan suka gaisa tare da mishi ya jiki….,
~~ ~~
An sako da YARIMA sun dawo gida,su duka sun fita yawon shak’atawa,daga can suka wuce wani katafaren restaurant dan su ci abinci..
Kowa an kawo mishi abinda yake so banda IMAAN dan cewa tayi ko warin shi bataso,toh fa sai yaya
kenan?
YARIMA lalla6a ta yayi har ya samu ta d’an ci ferfesun kayan ciki,bayan sun gama ne suka tashi dan magrib ta gabato,daidai zasu fita sukayi kicibus da wata budurwa,kallon kallo suka shiga yi da YARIMA,ita ma shi take kallo tanson ta tuno sunan shi sai can tace”wa nake gani kamar prince shureim?”YARIMA yace”yes shi ne sa’adiya uzaifa koh?”eh kwarai Ashe baka manta sunan ba,so ya kake naji ance Kayi aure”,yace”eh ga matata nan sunan ta KHADIJATUL IMAAN she is my life”,YARIMA yayi hakan ne saboda kar ta sake nace mishi irin na baya…