KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Tsawa ya daka matayace”ki tashi ki d’auko mayafinki nace,umarni nake baki ba za6i ba,nan da nan ta gudu d’aki dan d’auko mayafi,ta tsorata da ganin yanayin shi,hmm yau fa abin ya motsa wato sarautar,ya koma mata YARIMA shi na da,gaba yayi ta bishi a baya….
Suna isa asibitin kai tsaye office d’in doctor MAHMOUD yaje,knocking yayi akace”yes come in”,tura k’ofar yayi suka shiga,Dr.MAHMOUD yana ganin shi yace”ah friend kune warhaka,sannunku da zuwa da fatan dai ba kan naka bane ko?”,hannu YARIMA ya bashi suka gaisa yace”a a doctor ni yanxu normal nake jina,magam ce batajin dad’in jikinta”,ya kalleshi yace”ok bari in kira nos sai suje ta dubata ko”,YARIMA yace”ok,please ce mata tayi Sauri”,waya doctor MAHMOUD ya d’auka ya kira nos d’in,ba jimawa ta shigo bayan ta gaishe su tace”gani doctor”,kallon ta yayi yace”kuje da madam ki dubata sai ta fad’a miki abinda takeji ok”,nos tace”ok to ba matsala tashi mu tafi…bayan sun fita ne doctor MAHMOUD ya kalli YARIMA yace”me yake damunta ne?”,YARIMA ya kalleshi yace”wlhy yanxu muna zaune take cewa cikinta da marar ta suke ciwo,shine nace bari muzo a dubata, doctor yace”ya haka friend,ya mukayi da kai sai da nace kabi komai a sannu amma baka d’auki shawara ta ba dan na tabbata baka bi da ita a hankali ba,kuma a matsayin ka na babban doctor ya kamata ace ka kiyaye wannan”,YARIMA yace”wallahi in ina kusan ta ban iya control kaina ne,amma ko ni nasan tayi k’ok’ari ma,kasan fa yanda nake,wlhy ina cikin buqatuwar ne shiyasa amma zanyi k’ok’arin gyarawa”,doctor yace”da yafi dai”,….an dubata akayi mata allurai biyu amma basu rubuta magani ba….sai kusan azahar suka bar asibitin,suka biya wani restaurant ya saya musu abinci sannan sukayi gida,da isar su lokacin sallah yayi,sai da sukayi sallah sannan suka ci abincin…suna zaune su MUSTAPHA sukayi sallama suka shigo bayan sun gaisa ne IMAAN ta amshi HANEEFAH daga hannun UMMU AYMANA,sannan suka zauna aka ci gaba da hira,suna cikin hirar ne wayar YARIMA tayi k’ara,yana dubawa yaga sarki ne mai Kiran wato mahaifin shi Kenan, ina zuwa yace dasu ya shige d’aki inda IMAAN ta bishi da kallon tuhuma,idan ka kalli idonta zaka gane cewa kishi takeji,a can d’aki kuma Sarki ne yake ma YARIMA fad’an cewa su dawo gida ya kawo IMAAN inda za’a kula da ita sosai”,YARIMA ya marairaice murya yace”sorry abba wlhy nima ina kula da ita a nan,kuma so nake mu wuce saudiya daga nan ma”,sarki yace”kai banson shirme son,yarinya da k’aramin ciki zaka d’auka ka rink’a yawo da ita,ku dawo in ta haihu kunje,kuma aikin naka fa,kazo ka kama aiki maza,kaji abinda nace ko?”,yace”to abba zamu dawo gida nan da two weeks ”,bayan sun gama wayar ne ya koma falon aka ci gaba da hira kuma ana kallo,inda YARIMA yake fd’awa MUSTAPHA cewa suma sun kusa komawa gida nan da two weeks, MUSTAPHA ya kalli YARIMA yace”kai haba dai”,yace”eh wlhy yanxu sarki ya kirani wai mu dawo na bar aikina nazo na zauna a nan,tunda na samu lafiya ya kamata mu koma yace”,ah to mai martaba yanada gaskiya saboda aikin likita aiki ne Wanda ya kamata ace ka tsaya sosai a kanshi saboda ceton ran mutane”,hakane gaskiya inji YARIMA,juyawa yayi ya kalli IMAAN yace”nurul qalbi na kinga kuwa yanda babyn ta miki kyau kamar taki,ko su bamu in kinaso”,tace”eh wlhy inaso su bani”,dariya sukayi mata UMMU AYMANA yace”to na baki ita tunda kinaso,”hhhh IMAAN Kenan jira kema kina hanya….
Sai lokacin sallah magrib suka watse,su MUSTAPHA sukace zasuje su shirya kayan su ne…bayan sallah YARIMA zai shiga wanka yace”baby na kizo muyi wanka”,tace”ni sanyi nakeji bazan yi ba,zuwa yayi kusanta ta ya kamo ta ya rad’a mata cewa”,in bakiyi yanxu ba ai kinyi na asuba”,a shagwa6e tace”ni dai a,a na gaji,banso”,yace”ni kuma inaso baby na kinsan yanda kike kuwa,bazan jure bane”,ta basar da zancen da cewa”ka kira min jamila mu gaisa,tunda nazo banyi magana da ita ba,yace”ok ga wayar can d’auko ta,a hankali take tafiya har ta kai bakin gadon ta d’auko,tana juyowa taga YARIMA ya kura mata ido,sai da taji kunya,zuwa tayi ta mik’a mishi ya kira ya bata daga nan ya shige toilet ita kuma ta koma falo…sun sha hirar su irin ta k’awaye inda IMAAN take ce mata”k’awata ya skull?”,jamila tace”alhmdllh,munyi missing d’inki a skull kowa ya tambayata wai ko kin daina skull ne,nace musu kina nan zuwa kinyi tafiya ne”,IMAAN tace”ku tayani da addu’a ya bar ni in koma skull dan ko hirar ta bai yi min”,jamila a ranta tace hmm lallai kam sai dai addu’ar dan YARIMA da wuya ya barki kiyi skull da yaron ciki,amma a zahiri sai yace”to insha Allah zamu tayaki,ke zan barki haka nan,naseer d’ina yazo”,hmm,IMAAN tace”ke na manta ma wlhy to ya ake ciki ne ? “,jamila tace”yace zai turo ayi tambaya da sadaki duka,nace mishi a bari sai kunzo,bazai yiwu ba ayi min sadaki k’awata bata nan ba”,hmm ok to shikenan ai mun kusa zuwa,nan da sati biyu naji yana cewa,wlhy duk nayi missing d’in gida”,jamila tace”ok to Allah ya kaimu na barki lafiya ki gaishe min da YARIMA bye”,ok bye….
Cikin dare YARIMA ya lalubo ta,ta rink’a nok’ewa tace”please ni bacci nakeji”,yace”baby na ai cikin da sauk’i ko?”, tace”eh,yace”kad’an zanyi baby na kinji”,tace”haba dai wai baka gajiya ne kullum kullum”,yace”haba baby na ai indai kece bazan ta6a gajiya ba,saboda Allah yayi miki wata baiwa da ke baki sani ba,hhhhh YARIMA mai wayo,uh uh sis ke ina ruwanki ne wai,tsakaninsu ne????ai in tak’aice muku labari sai da YARIMA ya samu kanta ta amince mishi,hmm,amma yau so d’aya kawai yayi saboda yana tsoron kar a kuma gidan jiya….ana gobe tafiyar su gida Nigeria,suka je shop,IMAAN kallon YARIMA take yana ta kwasar kayan jinjirai,kasa jurewa tayi sai da ta tambayeshi tace”naga kana sayen kayan yara,me zakayi dasu?”,murmushi yayi gami da shafar fuskar ta yace”ajiyesu zanyi har mu samu baby sai mu rink’a sa mata ko?”,baki ta fiddo tace”uh nidai ba yanxu ba”,hhhhh IMAAN Kenan trop tard, dariya yayi yace”to shikenan sai in bayar tunda bakiso”,nan dai sukayi sayayyar su dayawa ita IMAAN mamakin shi takeyi yanda Yake fidda kud’i ko ciwon kashe su bayayi,hmm to akwai su ne mana…
****
Yau ne su YARIMA suka dira gida Nigeria inda motoci wajen hud’u sukaje tarben su,sai kace wani gomna ne ya zo,hmm lallai,cikin su har da nafeesat,da naseer shima yazo,jamila taso zuwa amma tanada lecture a time d’in…
Da saukar su feenat taje da gudu ta rungume IMAAN,inda naseer shima ya rungume YARIMA,dogarai kowa ya kawo gaisuwa,nan da nan YARIMA ya rikid’e ya koma ya dan shi saboda yaga dogarai,manyan kayane a jikinshi da bak’in glass manne a kyakkyawar fuskar shi,
Feenat ta kalli IMAAN tace”wow!anty na wai kinga yanda kika canza kikayi kyau kuwa?”,IMAAN ta kai mata dukan wasa tace”banson zolaya fa feenat”,feenat tace”i’m serious wlhy kinyi kyau masha Allah”,yace”to naji dai”,daga nan kowa ya shiga mota suka kama hanyar gida inda a can d’in ma an shirya musu tarba ta musamman…..
please manej,wlhy sai da nyi typing har na gama ya goge duka,na gaji,kuyi hak’uri da wannan,i’m buzy.tnx
‘YAR MUTAN KAZAY CE????
ANTY MAIMOUNATH????
+22969164943