KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY*:✍????
*ANTY MAIMOUNATH*????
DEDICATED TO:
MAMAN AHMAD(MARDIYYA KAO’JE)
UMMU BASHEER(SIS FATEEMA)
MOM MUSADDIQ
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page2⃣5⃣~2⃣6⃣
Motocinsu a jere suke tafiya gwanin sha’awa kamar taryen gomna akayi,a hankali suke tafiya har suka isa gida,get aka bud’e musu suka shiga,k’ofar motar ma sai da aka bud’e min dan girmamawa,ah to ba dole ba,sarauta wasa ce…..da muka fito daga motar naga abin mamaki,saboda mutane ne cike da gidan ga barori,masu hidima suna tayi, da ganin mu sukazo suka kwashi gaisuwa YARIMA kuwa fuskar nan kamar bai ta6ayin dariya ba,hmm,feenat tana rik’e da hannuna muka shige bayan mun gaishe da mai martaba ,YARIMA kuwa zuwa yayi ya rungume shi,sarki yace”welcom my son,kunzo lafiya ko?”,YARIMA yace”tnx abba na,lafiya klau,mun sameku lafiya”,sarki ya amsa da”kowa lafiya sai missing d’inka da mukayi”,murmushi YARIMA yayi,sarki yace”ku shiga daga ciki anjima munyi hirar yaushe gamo ko?”,to abba mun bar ka lafiya,yana gama fad’in haka ya kama hannun NASEER sukayi ciki…ko da muka doshi 6angaren su maman su YARIMA nan ma abin mamaki, wai duk wannan abun dan mu aka shirya,dan har taron mata na gani,Wanda da alamu gayyatar su akayi walimar taryen mu…
Da sallama muka shiga,nan ma da mutane,mama tana ganin mu, da kanta ta tashi tazo ta rik’eni ni kuwa kaina a k’asa dan kunya,hmm ai bakisan ma tasan kinada ciki ba ai da sai yaya Kenan, hhhh…mama ta rik’eni har muka isa cikin d’akin ta zaunar dani,itama ta zauna,zamowa nayi k’asa ina zan iya zama a kujera kusa da ita ai bazan iya ba,duk sai da na gaishe da matan, da alama k’awayen ta ne,kuma duk matan manya ne,hmm
Bamu jima da zama ba sai ga YARIMA sun shigo shi da Naseer,har kusan k’afar mama yazo ya zauna yana gaisheta”,tace”banso nayi fushi,sai da ka gama da mai martaba sannan kazo wurina,to nima ga ‘yata nan”,YARIMA marairaicewa yayi kamar k’aramin yaro yace”haba dear mom d’ina kiyi hak’uri ba gashi ba yanxu nazo”,Naseer ma ya gaisheta,sannan suka tashi suka fita…bayan sun fita ne mama ta kalli nafeesat tace”ku tashi ku shiga daga ciki tayi wanka a kawo mata abinci”,feenat tace”to mama”,sannan ta kama hannun IMAAN sukayi cikin d’akin ta…bayan tayi wanka ne feenat ta bata wasu kayan ta saka,saboda nata an wuce dasu 6angaren ta,ita dai feenat kallonta takeyi,yanda ta k’ara haske,IMAAN tace”lafiya wannan kallo haka sai kace kin samu T.V?”,dariya feenat tayi sannan tace”klau kawai gani nake kamar ba IMAAN d’in da na sani da bace,duk kin wani k’ara haske,kinyi k’iba kuma,ko ke baki lura bane?”,IMAAN ta kalleta tace”wallahi na gani,amma ni banson wannan jikin da na k’ara”,suna cikin yin hirar ne akayi sallama suka amsa masu hidimar abinci ne,’yan aikin IMAAN,sune suka shigo tare da abinci,suna murnar dawowar uwargidan tasu,sai da suka mata sannu da zuwa sannan suka fita bayan sun ajiye kulolin abincin….feenat ce ta zuba musu abincin suka fara ci,ai IMAAN tana d’aukan baki na biyu taji wani irin amai ya taso mata da gudu tayi cikin toilet ta fara kela amai har sai da feenat taji tsoro da gudu tayi falo dan ta fad’a ma mama…
Hankali tashe suka shigo ita da feenat a lokacin har ta gama aman tazo ta kwanta a gado,mama ce tazo kusan ta tace”sannu ‘yata kinji,yanxu me kikeso a kawo miki”,a kunyace IMAAN tace”ba komai ba”,mama tace”a,a bazai yiwu ba,ga tafiyar da kukayi ga yunwa,ai sai ki yiwa kanka illah,hmm mama kedai fad’i gaskiya ko in fasa kwan????
IMAAN tace”zogale nakeso”,kan ta a k’asa ta fad’a,mama ta kalli feenat tace”jeki kitchen ki fad’a musu su had’o zogale a kawo”,feenat tace”to bari inje,da kaina ma zan had’o mata”,mama tace”yauwa ‘yar albarka yi maza kinji”,to yanxu kuwa mama inji feenat”,sannan suka fice….
6angaren YARIMA kuwa yana can duk kewar matar shi yakeji,wunin da yayi bai ganta ba,mutane duk sun hanashi sakewa,sai bayan azahar ya d’auki waya ya kira ta,a lokacin har jamila da Maryam kanwar IMAAN sunzo suna hirar yaushe gamo,d’aukan wayar tayi ta d’ora a kunnenta tace”assalamu alaikum”,daga can YARIMA ya amsa mata sannan yace”baby na ya jikin naki,nasan dai yana ta miki ciwo ko?”,tace”a,a alhmdllh”,murmushi yayi yace”to kinci abinci dai ko?”,a shagwa6e tace”ba sai da na fara ci ba ya sani amai”,yace”oh sorry baby na kinji,to yanxu me zakici a kawo miki,ko inzo ne?”,girgiza mishi kai tayi kamar yana ganinta tace”ai naci zogale kuma ban yi amai ba”,ok to anjima zan shigo in dubaki duk nayi missing d’in ki,ke fa kinyi nawa kuwa?”,bata bashi amsar ba ta kashe tana murmushi,shima daga can murmushin yake,Naseer ya kalleshi yace”hmm kaji ‘yan soyayya nima dai gwara inyi auren nan ko zan huta da iskancin ka”,dariya YARIMA ya mishi yace”ah to ka zauna dai har matata ta haihu kuna nan…dukan wasa Naseer ya kai mishi yace”karka yi min baki mana”,dukansu sukayi dariya…hidima akayi tayi sai magrib aka watse kowa ya koma gidanshi…
Bayan anyi sallah isha’i su jamila suka tafi gida,ya rage daga IMAAN sai feenat a d’akin suna hirar su,aka kawo abinci IMAAN tace”ni ban ci feenat kici kawai”,feenat ta kalleta tace”meyasa?”,marairaice fuska tayi tace”baki ga d’azu ma da na fara ci ya sani amai”,feenat tace”to sai me kikeso?”,tace”ba komai ba,banjin yunwa ma sai dai bacci nakeji”,feenat tace”to ko dai sai yaya yazo ya rink’a baki a bakinki ne ta k’arasa maganar cikin zolaya”,IMAAN da ta gane ta cewa tayi”eh d’in shi zai bani ko haramun ne”,dariya feenat tayi tace”a,a ni na isa ince haka,Allah huci zuciyar Mr.SHUREIM,hmm feenat da a gaban YARIMA kika fad’a sai yayi tamaula(ball)dake,
IMAAN tace”oho miki dai kanki akeji ni ki kyaleni inyi bacci na,feenat ta kama baki tace”a ina zakiyi baccin?”,IMAAN tace”a nan ko an hana ne”,feenat tace”nidai ba ruwana yaya in yazo cewa zaiyi mu biyu muka kitsa wannan abu,please tashi ma in raka ki gidanki”,hmm IMAAN tace”eh saboda gani marar kunya,ni dad’i miji ko,sai in tashi ki rakani d’in”,dariya tayi tace”nidai tashi kawai in kaiki,yau fa tamkar amarya kike dan komai na gidanku ya canza,tashi muje ki gani ma”, IMAAN tace”ke bazan je ba karki dameni kinji ko,tana gama fad’ar haka ta juya mata baya tayi kwanciyar ta,
K’arfe 9:30pm na dare YARIMA ya shigo tare da yin sallama,mama da feenat ne a falon suna kallon T.V,inda feenat tayi matashin kai da cinyar mama,amma tana ganin shi tayi saurin tashi dan tasan halin shi yanxu zai mata tsawa,ya iso ya tsugunna ya gaishe da mama,feenat kuma ta gaishe shi,ya kalleta yace”ke ina IMAAN?feenat tace”tana d’akina bacci takeyi”,yace”je ki taso ta mu tafi”,hmm su YARIMA ko kunyar mama ba’a ji ne,feenat zata tashi mama tace”ke koma ki zauna bazaki je ba”,ta kalli YARIMA tace”me zata maka in aka taso ta”,sai a lokacin ne yaji kunya,sunkuyar da kai yayi yana sosar keya,
Mama tace”a matsayin ka na likita kuma doctor kasan illar da take tattare da tashin mai ciki daga bacci”,ta gaji tayi tafiya mai nisa sai ta huta ko da zata je”,
kalar tausayi yayi yace”mama in muka tafi ba sai ta kwanta ta huta ba a can d’in”,kallon shi tayi tace”kai ba fa zan baka yarinyar nan ba da yaron ciki tana fama da kanta,dan nasan halinka”,wata irin kunya ce ta kama YARIMA saboda ya gane inda mama ta nufa,hhhh…zai sake magana ta d’aga mishi hannu tace”na ida magana ta tashi ka tafi sai da safe Allah ya bamu alkhairi in kuma tsayawa zakayi mu rink’a ja in ja da kai to bismillah,Allah huci zuciyarki mama na tafi sai da safe inji YARIMA,amma fa sai da ya d’an bani tausayi ke fa ummu basheer ?