KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Bayan kwana biyu
YARIMA fa an hana shi matar shi dan mama ta kasa ta tsare ko zuwa yayi a gaban ta zai ga IMAAN d’in sannan ya fita,gashi kuma ya kusa kama aiki,duk a matse yake,hhhh lallai mama kin harbo jirgin YARIMA????
Sai da tayi sati daya a 6angaren su mama kafin a rakata gidan ta,amma sai da mama taja mishi kunne sosai,hhhh,yau dai nasan mai kwatar IMAAN a hannun YARIMA sai Allah,ita kanta tasan da hakan dan a tsorace take dashi,ta ga take taken shi,
Bayan sallah isha’i aka rakata gidan ta kamar sabuwar amarya dan har mai lalle aka kira tayi mata da kitso kuma,da isar su mamaki ya hanata magana komai an canza mata har yafi lokacin da take amarya,lallai akwai budiri a nan gaba kenan…sallama sukayi suka shiga,ko ina sai k’amshin turaren wuta yake,sun iske YARIMA yana zaune a falon yana danne danne a laptop d’inshi ga kuma T.V a kunne ko wanne yakeyi?kallon ne ko aiki a laptop,ya amsa musu,barorin sukayi baya dan ganin shi,ita kuma feenat biyota tayi suka shigo tare,har k’asa ta tsugunna ta gaishe shi, kallon da ya mata ne take ta gane nufinshi,kallon IMAAN tayi tace”a koma sai da safe”,IMAAN tace”daga zuwanki kizo muje ciki mana”,YARIMA yace”in kuka shiga me zatayi miki?”,ya jeho mata wannan tambayar fuskar shi ba fara’a kuma ba tare da ya kalleta ba,hmm tasan da yana cikin fushi ne,
Sukayi tsaye babu Wanda yayi magana,d’agowa yayi ya kalli Feenat wata tsawa da ya daka mata ni kaina sai da hanjin cikina ya kad’a,ai kuwa ta kwasa da gudu sai waje,
IMAAN kuwa takowa tayi a hankali tazo kusa dashi ta zauna duk da a tsorace take,tace mishi”barka da wuni”,ban buqata yace sa ita,tace”dan me?”,aje laptop yayi ya kalleta yace”ai kin fi kowa sani,kin damu dani ne da kike tambayar lafiya ta?”,tace”to kayi hak’uri nayi laifi ta k’arasa maganar a hankali”,hmm yace kawai,
Ya sake kallon ta yace”to wallahi karki ce zakiyi min raki ko kuka,dan ke kika jawa kanki,hmm tashi tayi zata wuce d’akin ta yace”in kin gama ina jiranki a d’akina”,gabanta ne yayi mummunar fad’uwa,dan tasan yau fa akeyin ta,hhhh
Har kusan 10pm na dare shiru IMAAN bata zo ba,tashi yayi ya iske sai yanxu ne ma ta fito daga wanka,d’aure da tawul ya iske ta,yace”sai yanxu kikayi wanka,tun d’azu aikin me kikeyi?”,tace”ba komai ba”,takowa yayi yazo kusan ta har suna gogar juna tanajin yanda iskar numfashin shi take sauka a kan fuskar ta,rufe ido tayi,ya kama hannun ya sauke su,zatayi magana ya hanata”shiiit,ba sai kin sa kata ba,nasan dai haka kike son fad’a ko?”,rad’a ya mata a kunne cewa”ko kin sa zaki ciresu kinga Kenan ba amfanin sawar koh?”,
Ita dai saurarenshi takeyi ta kasa cewa komai, d’aukan ta yayi ya nufi gado da ita…..
YAR MUTAN KAZAY CE????
*ANTY MAIMOUNATH*????
*+22969164943*
????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY*:✍????
*ANTY MAIMOUNATH*????
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page2⃣7⃣~2⃣8⃣
D’aukan ta yayi cak yayi kan gado da ita tana magiya,ko sauraren ta k’inyi yayi,ina ganin YARIMA ya saki hanya,na bazo a guje falo,amma ina fitowa ummu basheer ta tisa keyata wai in koma in samo labari,nidai ba ruwana itace????
IMAAN dai ido ya raina fata,dan sai kusan asuba ya saurara mata shima wai dan saboda d’an babyn shi ne,hmm,bayan ka gama Kenan,cabb….da asuba ya d’auketa cak saï toilet dan yasan yau ya ta6ota bazata iya tsinana komai ba,hmm…
A toilet d’in ma saï da suka 6ata lokaci dan cewa tayi bazai mata wanka ba wai kar ya kalle mata jiki,hhhh na nawa kuma wai ance da kuturu Allah ya la’ance ka,
Bayan tayi sallah a nan ta 6ingire tana baccin wahala????ah to na wahala ne mana,ko da YARIMA ya dawo daga masallaci,ya tadda ta bisa abin sallah tana ta sharar baccin ta,saï da ya tausaya mata dan yasan ta wahala,zuwa yayi ya d’auketa ya kaita bisa gado,ya cire mata hijab d’in duk tana bacci,lallai IMAAN an wahala,shima d’in tu6ewa yayi ya kwanta a bayanta suka cigaba da baccin su….
Basu suka tashi ba sai 12am na rana,wanka suka sakeyi suka shirya tsab dasu sai k’amshin turare ne ke tashi a jikinsu,falo suka nufa,IMAAN kuwa sai kumburi takeyi,sai da suka zauna bisa dinning table ya kalleta yace”baby na yadai na ganki haka,lafiya dai ko?”,ta zumburo baki tace”ba kaine ba…kuma sai bata k’arasa maganar ba ta kyale”,murmushi yayi yace”nine nayi me?”,tace”ba kaine ka bani wahala ba,kuma sai na had’a ka da mama”,dariya yayi yace”to ai na fad’a miki daman,sai da nace miki muzo 6angaren mu,amma kika k’i Kenan duk yanda nayi miki banyi laifi ba,haba baby na kinsan fa yanda nake amma kika basar kamar baki gane ba,kikayi zamanki a wajen su mama”,shiru tayi tana sauraren shi sai da ya gama ta kalleshi ido cike da hawaye tace”cikina ya kulle kuma inajin amai”,
YARIMA yace”cikinki kuma,oh God,tashi to mu tafi kiyi aman sai kisha magani,ko in kira doctor ta duba ki”,ai fa da taji ance doctor sai cewa tayi”ni fa aman ma ya koma,kuma cikin yayi sauqi,hmm,kallon ta YARIMA yayi yace”kinsan banson musu da gaddama ko?”,zo ki kwanta tazo ta dubaki,hmm lallai ciki d’an gata tun kafin ya zo duniya Kenan,kwantar da ita yayi,ya d’auki waya ya kira doctor,ce mishi tayi kar ya damu ba wani abu da zai samu cikin,Dole ne mai ciki ta rink’a jin chanji a jikinta ba kamar da ba”,yace”ok to shikenan doctor nagode”,tace”ok ba komai aikina ne ai”,
* *
Yau ne za’a kawo sadakin jamila IMAAN tana ta magiyar YARIMA ya barta taje wajen sadaki,daga nan kuma ta lek’a gidansu tunda a unguwar ne su jamila suke,amma fir yak’i,ta marairaice tace”kai ma fa zuwa zakayi sai a bar ni ni kad’ai a gidan”,yace”to baby na me zakiyi a can?”,tace”hmm jamila ce fa,k’awata tun muna yara muke tare sai yanxu kace bazanje ba,kayi hak’kuri in tafi daman nayi missing su umma”,yace”ohk naji,amma da sharad’i”,tace”wane iri”,yace”banson kije ki shiga cikin k’awayen ku kuyi ta shirme da wani raye raye,karki manta ke matar aure ce,idan naji labari ranki zai 6ace kinji na fad’a miki,ki kula da kanki,saboda zuwa gida kawai zan barki”,ta kalleshi yace”to naji na yadda”,yace”ok jeki ki shirya har da ni zamuje in na gaishe su sai in wuce office akwai abinda zanyi a can,monday zan fara zuwa wajen aiki”,IMAAN kuwa sai zumud’in zuwa gida akeyi….
Sun fito a jere suke tafiya gwanin ban sha’awa,sunyi shar dasu sai k’amshin turare sukeyi,6angaren su mama suka nufa….shiga sukayi tare da yin sallama,mama bata falo YARIMA ne yaje har d’akin ta ya kira ta,da ta fito IMAAN ta durk’usa har k’asa ta gaishe ta,mama tace”tashi ‘yata kinji,ya kuka kwana da fatan jikin da sauqi ko?”,a kunyace IMAAN tace”eh mama naji sauqi”,yace”to alhmdllh”,YARIMA ya kalli mama yace”zamu fita mama,yau akeyin sadakin k’awar ta jamila,naseer ne angon ai ranar ma na fad’a miki ko?”,eh ka fad’a min,Allah sarki yau da yamma ne za’ayi Kenan?”,YARIMA yace”insha Allah,to zan kaita gida ta wuni da yamma bayan anyi sadakin sai a d’auko ta”,yace”to shikenan ku tafi Allah ya kiyaye hanya,’yata ki kula da kanki kinji”,to mama kawai tace”,amma a k’asan zuciyar ta tambaya take wai meyasa ake ta cewa ta kula da kanta?oho kema baki sani ba Bare kuma mû……
A gidan su IMAAN sai murnar zuwan ta akeyi,zuwa tayi ta kwanta a jikin umman su tace”umma nayi kewar ku sosai wallahi,kamar nayi shekara ban ganku ba,umma tace”to ai haka auren yake,ba gashi yanxu kinzo kin gan mû ba,ai YARIMA akwai k’ok’ari yazo ya kawo mana abin arziki wai tsaraba ce”,da Sauri ta tashi zaune tace”umma Kenan shi yazo,shine ni yak’i kawoni sai yau”,shima sai da na rok’eshi nace sadakin jamila ai Dole in zo sannan ne fa yace to muzo ta k’arashe maganar a shagwa6e”,ummu tace”ai ke da shi duk d’aya ne tunda yazo ba shikenan ba”,hmm to umma ina tsarabar da ya kawo muku, nima na kawo”,tace”bazan nuna miki ba ina ruwanki ne da abinda ya kawo”,uhum kawai IMAAN tace sannan ta basu na ta tsarabar,a gidan babu Wanda bai samu ba har abba shima anyi mishi tashi tsarabar,tace”umma bari inje in ga shirye shiryen me ake mana na tarben ‘yan kawo sadaki”,umma tace”duk ne ai za’ayi har lefe gaba d’aya”,IMAAN tace”shine jamila bata fad’a min ba?”,umma tace”a,a itama sai daga baya sunce suna son ayi gaba d’aya a huta kawai”,to umma bari dai inje gidan nasu ina zuwa”,umma tace”kin fad’a wa mijinki dai ko?”,to umma ai yasan zanje d’in,eh duk da haka dai ki fad’a mishi yafi,6ata fuska tayi ta 6ude jakar ta ta fiddo wayar ta,Kiran YARIMA tayi,umma tace”to ki saki ranki mana ko a haka zaki mishi magana,kai yau naga wata irin ‘ya,