KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Daga can YARIMA ya kashe Kiran sai ya kirata yace”baby na lafiya ko?”,eh daman inaso zan leqa gidansu jamila in ga shirin da akeyi in akwai aiki sai muyi tunda umma tace har da lefe baki d’aya zasu kawo”,yace”no baby na kije amma ban ce kiyi aiki ba ok”,tace”to dan me sai inje in zauna manya suna aiki ina kallonsu ai da kunya ko”,
Yace”to wallahi sai in ce ki zauna ma,nidai banso kuma kar in ji labarin kinyi aiki”,to shikenan”,sukayi sallama ta saka wayar a jakar ta tashi tsaye ta shiga d’aki ta aje jakar tace”umma yace inje na tafi sai kunzo,tace”to kin d’auki wayar ki ko?”,a,a umma in maryam tazo ta kai min can,tace”a,a dan me d’auki kayanki in aka kira ki fa”,IMAAN tace”to bari na d’auka, d’auka tayi ta fice,umma kallon ta takeyi a zuciyar tace Allah sarki khadija na,yarinta na damunki baki ma san kinada ciki ba,hmm in ta sani ko ya zatayi?oho
*
Bayan sallah magrib,IMAAN ce ta shigo da kuka umma ta rikice tace”ke lafiya kika shigowa mutane da kuka”,cikin kuka tace”umma wai da gaske ciki ne gareni?”,murmushi umma tayi tace”shine ya saki kuka wa yace miki ciki gareni?”,tace”ba a gidansu jamila bane suke cewa masha Allah IMAAN Allah ya raba lafiya,da farko ban gane nufinsu ba sai da wata a cikinsu tace muna nufin cikin da ke jikinki,tana kaiwa nan ta k’ara fashewa da kuka”,umma tace”ke banson hauka da shirme kinji ko,ciki ne gareki ai ba shege bane da ubanshi sai me”,ai fa IMAAN ta fara birgima kamar k’aramar yarinya ‘yar goye,
Umma tace”ai kuma sai kiyi,ki cigaba da kukan har abbanku yazo ya tardaki a haka,wallahi sai ranki ya 6ace na gaya miki”,
Tsagaita kukan tayi sakamakon muryar abba da taji a tsakar gida,yana cewa ina IMAAN d’in ta fito direban ya zo,ras gabanta ya fad’i a ranta tace babu inda Zani badai yaudara ta akayi ba,inada ciki ake 6oye min,hhhh IMAAN mai shirme kenan….. Maryam ce taje ta fad’a wa abba cewa IMAAN tak’i fitowa wuri ma ta samu tayi kwanciyar ta,hmm
Abban da kanshi yazo,tsawa ya daka mata yace”ki tashi maza ku tafi waye sa’an ki a nan,anayi miki magana kin nemi waje kin kwanta ba jiran ki akeyi ba a k’ofa”,tashi tayi sumi sumi ko jakar bata d’auka ba,sai maryam ce ta biyo mata da ita,ta shiga baya ta zauna,direba yaja suka tafi…
Da suka isa ma bata tsaya an 6ude mata k’ofar mota ba,ta 6ude ta fita,cikin gidan ta nufa,kai tsaya 6angaren su tayi,ko sallama batayi ba ta shiga,babu kowa a falo,amma taji motsin mutum a kitchen da alama su harira ne,bata bi ta kansu ba ta shige bedroom d’inta,jefar da jakar tayi ta fad’a bisa gado tayi rub da ciki ta bud’e sabon kuka…
Tana cikin kukan ne ta jiyo motsin mutum kamar an shigo d’akin,k’amshin turaren da taji ne ya bata tabbacin YARIMA ne,isowa yayi yace”baby na lafiya kike kuka,kuma kikayi irin kwanciyar da na hanaki”,tashi tayi zaune ta kalleshi tace”daman ciki gareni shine kuke 6oye min?”,YARIMA yayi shiru ya rasa abin fad’a…toh fa sai ka nemi hujjar ka ta 6oye mata,hhhh mudai ‘yan kallo ne…….
Ku biyoni dan jin yanda zata kasance????♀????♀????♀
*'YAR MUTAN KAZAY CE*????
ANTY MAIMOUNATH????
+22969164943
????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY*:✍????
ANTY MAIMOUNATH????
DEDICATED TO:
YAYA HASSAN ATK????
HUSSAIN ATK????
YAYA PRINCE ABDALLAH????
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page3⃣3⃣~3⃣4⃣
YARIMA fa an jima ba’a had’u ba dan wani zaxxafan wasa yake mata har dai ya kai ga cimma abinda yakeso,IMAAN ji tayi kamar ranar farkon su saboda anty khaleesert ta kira ta tace tasha maganin nan,hmm,ai kuwa IMAAN ta gurzu wajen YARIMA dan ba shi ya sarara mata ba sai wajen 3 na dare,cabb,IMAAN har da kukan ta wai ita yaji mata ciwo,rarrashi ya shiga yi,yana bata hak’uri,wai ya kasa control kan shi,hmm wayo ne yake miki kawai IMAAN,hhhh….
Da asuba ma taji taji ana shinshinar wuyanta,YARIMA ne wai tayi hak’uri yayi kad’an kuma,toh yau naga jaraba,tace”wlhy ni na gaji daman ban warke ba ka tashi duk kaji min ciwo ta karashe maganar cikin kuka”,yace”to naji shikenan i’m sorry nayi laifi ko?”,am so sorry baby na,wallahi ba laifi na bane in kina kusana ne ban iya wa saï na kusance ki,kuma kinsan fa na kwana biyu shiru”,batayi magana ba,zata tashi tsaya ta kasa,har da ‘yar k’ara tayi yace”sorry baby menene?”,tace”ka gani ko na kasa tashi ciwo nakeji”,yace”sannu bari in d’aukeki in kaiki toilet d’in,cak ya d’auketa saï toilet,tare sukayi wanka IMAAN dai idon ta a rufe wai dan kar ta ga YARIMA ba kaya,YARIMA kallon ta yayi yace”oh na manta baki shiga ruwan zafi sosai ba,gaskiya koma cikin ruwan ki gasu da kyau”,tace”wlhy zafi nakeji ni ya isa haka saï gobe kuma”,yace”naji karkiyi min kuka,ke mai arhar hawaye,
YARIMA ne ya fara fitowa saboda kar ya makara zuwa sallah,saï da taji ya fice sannan ta fito tana d’ingisawa,hmm kai IMAAN akwai son jiki,guduwa tayi d’akinta kafin ya dawo,hhh wa yaga amarya sabon kawo wa Kenan…..da ya dawo yaga bata d’akin,murmushi yayi a ranshi yace baby na Kenan ita dai akwai tsoro,bari in kyaleki ki kwanta ki huta,gado ya hau yayi kwanciyar shi,haka itama IMAAN kwanciya tayi….
Wayar shi ce tayi k’ara firgigit ya tashi zaune daga asibitin su ne,ya kalli agogon da ke manne a bangon d’akin yaga 8am ta gota yayi d’aukan Kiran yayi banji me aka ce musu ba,yace”ok gani nan zuwa”,tashi yayi a gurguje yayi wanka ya shirya cikin suit bak’ak’e sunyi matuk’ar k’arbar shi abinka ga farin mutum, gaskiya nima na yaba au????ba ruwana bakina ne ya fad’a
Zuwa yayi d’akin IMAAN ya iske tana bacci,ai Dole saboda jiya batayi sosai ba,kuma ga ciwo,zuwa yayi ya gyara mata kwanciyar ta yayi mata kiss a baki ya fice…da ya sauko k’asa ko break fast bai zaya yayi ba ya fice dan yana da patient dayawa a asibiti kuma an ce ana ta jiranshi,yau ko wajensu mama bai shiga ba,direba yana ganin shi ya zo da Sauri ya amshi kayan hannun shi gami da gaishe shi,sannan yaje ya bud’e ma YARIMA mota ya shiga shima ya shiga mazaunin direba ya tashi motar suka fice,YARIMA yace mishi kai yi sauri ana jirana,yace”to maigida an gama”,
Da isar su ma kai office d’in shi ya shiga ya kira wata nos yace”kice ma patient d’in su fara shigowa”,jiki na 6ari tace”to sir”,fita tayi ta fad’a musu sak’on shi,dad’i takeji wai yau YARIMA ya mata magana,dan bai basu fuska ko kad’an,hmm
** ****
Ba YARIMA bane ya samu kanshi ba sai 10am na safe ga yunwa duk ta addabeshi,waya ya d’auka ya kira mama suka gaisa yace mata yayi latti ne shiyasa ya fice bai shiga ba,haka ya kira abba ma,daga nan sai sahibar tashi wato IMAAN,Ashe bata tashi ba sai wayar ne ya tashe ta,d’auka tayi tace”hello”,daga can YARIMA yace”hey!baby na baki tashi ba kenan,nine ma na tasheki ko?”,i’m sorry,amma kinsha bacci”,tace”eh,”yace”duk gajiyar jiya ce baby na ya fad’ane dan ya tsokano ta,ta shagwa6e kamar tana gabanshi tace”ni ka daina banso”,yace”to na daina,so ya kike?”,tace”lafiya lau,kana asibiti ne?”,yace”yes”,tace”shine baka tashe ni ba”,yace”sorry na makara ne ko break fast banyi ba har yanxu duk yunwa ta addabeni,amma ai nayi bankwana da ke ko?”,tace”yaushe ni da nake bacci”,yace”nayi miki kiss a baki da zan fita”,kunya taji ta basar sannan tace”yanxu to me zakaci a can?”,yace”yanxu na aika za’a kawo min tea”,inaso kafin in dawo a sake min suna,in tashi daga YARIMA in koma wani matsayi,kuma yau abincin ki nkso ki dafa mana da kanki OK?”,yace”to naji amma me sunan naka yayi da za’a sauya shi?”,