KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Sarki ya sake kallon shi yace””ya kamata ka fito da wacce kakeso ayi maka aure zai dan kore maka zaman kad’aici,yarima yayi murmushi yace “” haba abba duka ma yaushe na dawo ne da har zanyi aure,kuma fa abba shekaru na basu kai ba ma.dak’uwa abban yayi mishi yace””ungo nan saï yaushe kakeso kayi auren mû da mukeson ganin ‘yan jikokin mû kuma kasan fa kaine babba a gidan nan ko.
To abba ayi hak’uri za’a nemo insha Allah.
Da kyau Allah yayi maka albarka,kaje ka huta.to abba a tashi lafiya good night.
Washe gari yarima yana kwance a gadon shi na alfarma da yasha ado,yana tunanin ina zai k’ara ganin wannan yarinya,hmm ni kuma nace su yarima an fada kogin soyayya????
Kai ina me zanyi da wannan yar mitsitsiyar yarinyar mai shegen fi’ilin tsiya yarima ne ke fadin haka kuma a zuciyarshi…
Da misalin karfe 8:00am na safiyar litinin khadijatul Imaan ce ta fito bakin titi tana jiran mai keke nepep tana sanye da uniform din ta na school bata yi wani kwalliya ba saboda ita ba ma’abociyar kwalliya bace,da hijab din ta har k’asa..
Batayi aune ba saï ganin motoci sun tsaya a gabanta tayi ta k’are musu kallo sai da gabanta ya fada ganin mamallakin motar….
Kuyi min hakuri wallahi i’m sick need ur prayers????
Ku biyoni danjin yadda zata kasance.
Yar mutan kazay ce????
Anty Maimounath????
[10/9, 01:44] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:????
*Anty Maimounath*????
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
(D.B.W.A)
Dedicating to:
Maman Ahmad(mardiyya ka’oje)
Maryam Ishaq
Maman Fairuza
Meemah Sadiq
Khaleesert
Da sauran masoyana dan sunada yawa luv u all????
Bismillahi Rahmanir Rahim
Page
Yarima ne na gani yana kallona daga cikin motar, da mukayi ido biyu saï na kauda kaina,a raina ina cewa shi wannan kullum a mota baya gajiya ma uhm saï wani girman kan tsiya wai shi dan sarki mtsw…ina cikin tunanin ne da ta d’ago saï bata ga motocin ba,
Nayi mamaki sosai ko yaushe har suka fice ban sani ba?
Kar dai ace yaga kallon da nake mishi ai da kuwa saï ya rainani duk ita kad’ai ke maganar ta har dai ta samu dan adaidaita sahu ta shiga.
Haka dai had’uwar tasu take kasancewa kusan kullum saï sun hadu,shi miskilanci da isa sun hanashi yi mata magana kuma idan yaje gida bashi da aiki saï tunanin ta Wanda ba a son ranshi ba yakeyi inji shi..wannan Kenan
Abinda yarima bai sani ba shine har fadawan shi sun gano shi daya gada cikin su yaje ya fada ma sarki halin da yarima yake ciki.
Yace ma sarki yarima fa wata yarinya ce yakeso amma yak’i ya furta mata.
Da jin wannan magana sarki yayi murna yace””alhmdllh indai maganar nan ta tabbata gaskiya to zanfi kowa jin dadi,
Sarki ya kalle shi yace””‘yar gidan waye haka da har d’ana ya kasa sukuni?
Yace””ranka ya dade wallahi ban sani ba, mû ma a bakin titi muke ganinta in zataje makaranta.
To a bincika min nan da kwana biyu inaso a kawo min labarin ko ‘yar waye.
To to ranka ya dade an gama.
Ya tashi ya fice.
Anyi haka da kwana biyu,Imaan tana zaune a tsakar gidan su tana taya umman su aiki saï sukaji anyi sallama,wani yaro ne ya shigo yace””ana sallama da maigidan””umma ta dubeshi tace””wanene?
Saï yaron yace””dogarin sarki ne
Umma ta zaro ido tace””
dogari kuma?lafiya?
Yace””nima dai ban sani ba saï ya fice
Umma ta tashi ta lek’a,bayan sun gaisa ya fada mata saqon sarki na son ganin malam a fadar shi.
Tace to idan ya dawo zan fada masa.
Bayan abba ya amsa Kiran sarki ya dawo saï ya tara mû a tsakar gida.yayi shiru na d’an lokaci sannan yayi gyaran murya,
Yace””kunsan dalilin Kiran da sarki yayi min?
Umma tace””a,a”” yace””sarki ne yake son in ba danshi yarima auren khadija,bansan lokacin da na mik’e tsaye ba na zaro ido nace” abba ni kuma?”
Ya kalleni yace”kwantar da hankalinki ‘yata
Bari in tambayeki,a ina kuka had’u da yarima har ya ganki yace yana sonki?
Na dag’o idona cike da hawaye nace wallahi abba ni a bakin titi ne kawai nake ganin su in zasu wuce nima in zanje school.
Abba ya kalli umman mû yace””saratu wallahi bansan ya zanyi da buk’atar sarki ba,kuma a gaskiya bazan iya hana mishi auren khadija ba,saboda sarki mutum ne mai adalci wa al’ummar k’asar shi.gashi inaso yarinyar nan tayi karatun ta.
Umma ta nisa tace”to ya zamuyi Kenan?in shi yariman ya yadda saï ta cigaba da karatun ta a can,
Abba yace”Anya a gidan sarauta ana haka kuwa?
Nidai daga nan tashi nayi na fad’a d’aki da gudu ina kuka…
Muna zaune bayan sallar isha’i muna hira ni na manta ma da wani yarima saï kwatsam mukaji sallama,auta da ya lek’a saï ya dawo da gudu yace”umma su yarima ne sukazo gasu can suna gaisawa da abba a k’ofar gida,
Gabana ya yanke ya fad’i nace na shiga uku me ya kawo shi?
An shigar dashi d’akin saukar bak’i.umma tace min inje amma banda rashin kunya in nutsu inji abinda zai ce min,
Na fiddo baki nace”ni fa umma ban son shi nawa ma nake d’à za’a min wani aure,umma tace”ni fice ki bani waje.
Da sallama ta na shiga d’akin,aka amsa min yana zaune bisa kujera,yau sanye take cikin k’ananan kaya,sunyi matuk’ar yi mishi kyau,fadawa suna ta fadanci.ni haushi ma suke bani wai saï kace shine sarkin hmm..tashi sukayi suka fice suna ta kirarinsu..
Na samu waje nesa dashi na zauna sannan nace”ina wuni”bai d’ago ba yace”lafiya”ita kawai ya fada,
Saï can ya d’ago ya kalleni yace”kin samu sak’ona ko ai basai na maimaita miki ba,
Na d’ago mukayi ido biyu ni dashi na kauda kaina nace”naji amma ni karatu na nikeyi ban isa aure ba,kaje ka nemi wata,
Yayi murmushi irin na k’asaita yace”ba yardar ki nake nema ba,kuma ba zab’i na baki ba,umarni ne kuma Dole ki zamo matata nan ba da jimawa ba.
Nace”to saï in gani in ana aure Dole”.
Yayi ‘yar dariya yace”ok ki jira lokaci kuma ki bini a sannu ba’a musu dani,idan kikayi wasa zaki zamo amarya nan da one week.
Na kalleshi nace”ba dai ni ba”
Bayan sati daya da faruwar haka,ina gidansu jamila kawata dan unguwar mû daya da ita,saï ga khaleed yazo kira na wai inzo yarima ne ya zo,
Na kalleshi nace” da yamman nan me ya zo yi”?
Jamila tace”ki tashi kije kiji mana,
Nace”sarkin naci kawai,shikenan baza’a bar mutum ya huta ba.
Da shigar mû gida umma ta fara fad’a tana cewa “kinsan zai zo amma kikaje kikayi zamanki,nace” ni fa umma bansan zai zo ba a ina zan Ganshi bare ya fada min
Na shiga d’akin da sallama yau kam fadawa suna k’ofar gida,sanye Yake cikin manyan kaya,na gaishe shi ya amsa,
Ya kalleni yace”daga ina kike”
Kallon mamaki na mishi ko ina ruwanshi oho..
Nace”gidan su k’awata mana”
Yace”banson yawo dan haka ki kiyaye,banda kawaye na banza,
Na kalleshi nace”da k’afata za’a hanani yawo tabb saï nayi.
Ya tashi ya tako har inda nake yasa hannu ya kama fuskata yace”maimaita abin da kikace,na fusge nace”ni ka daina tab’ani”
Ya sakeni sannan yace”tsoron me kikeyi?i’m ur husband to ne,so ki daina jin tsorona.
Nace”waye zaiji tsoron ka?ni ba tsoronka nakeji ba, a makarantar mû ta islamiyya an ce mana babu kyau namiji Yake tab’a mace.
Yace”ok ni zan tafi gobe za’a zo a kaiki school,saura idan dreba yazo kiyi mishi gaddama
Yana fadin haka ya fice..
Yau anMaimi garin kaduna ruwa akeyi,yarima ne kwance a d’akin shi saboda yau asabar ce,waya ya d’auka ya kira abokin shi doctor naseer”,hello ranka ya dade likita bokan turai”Yarima yayi dariya yace”ya kake ?”lafiya lau naseer yace dashi”,