KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace”baby na tashi a sama na kina sani wani yanayi gashi ke kuma da nace zanyi sai ki fara min raki”,ai kuwa firgigit ta tashi,kauda kanta tayi sannan tace”ka tashi ka shirya muyi break fast rana fa tayi har 12 ta wuce”,a zolaye yace”to ba ke bace kika hanamu bacci jiya”,ta rufe fuska da hannayen ta tace”ni ba ruwana kai ne dai”,murmushi yayi bai ce komai ba ya yaye blanket d’in daga shi sai gajeren wando,IMAAN ido ta zaro,subhanallahi,gaskiya YARIMA irin sadaukan mazan nan ne jarumai kuma,jiki duk a murd’e,yes namiji Kenan,kallon ta yayi yace”lafiya meye?”,idonta a rufe ta nuna shi,ya gane ta,sai yayi murmushi yace”bud’e idon ki kalleni,meyasa kike kunya ta,nifa mijinki ne,yanxu babu zancen kunya,muje ma kiyi min wanka”,tace”a,a ni nayi in na shiga zan 6ata jikina”,yace”hmm baby na wayo ko?”,to jirani yanxu zan fito……bai jima ba ya fito ya saka k’ananan kaya,suka sauka k’asa,wajen dinning suka nufa,suna tsakar yin break d’in ne akayi knocking k’ofar falon,YARIMA ne ya tashi yaje ya bud’e,harira ce ta sunkuya ta gaishe shi yace”lafiya?”,tace”wasu ne suka zo suna k’ofar gida mai gadi yace sai an sanar daku zai barsu su shigo”,yace”ok gani nan zuwa da kaina”,tace”to ranka ya dad’e sannan ta shiga cikin falon ta iske IMAAN,shi kuma ya fice….da zuwan shi k’ofar gidan ya hango MUSTAPHA daga cikin motar,ya zaro ido ya isa da sauri yace”what?wa nake gani kamar abokina?”,MUSTAPHA yayi dariya yace”surprise ne muka muku”,UMMU AYMANA ta gaishe shi, sannan yace a bud’e get su shiga,shiga sukayi yayi parking d’in motar sannan suka fito mai gadi kam yasha fad’a a wajen YARIMA sai da Mustapha yace mishi ya barshi ai bai san mu bane kaga Kenan yanada gaskiya,fada suka fara zuwa YARIMA ya gabatar dasu wajen mai martaba aka gaggaisa sannan suka shiga ciki nan ma sai da ya kaisu wajen hajiyar shi,wato mama kenan, daga 6angarensu yayi dasu,ita dai UMMU AYMANA mamakin irin girman gidan take,gida ne cikin gida,Wanda bai san kanshi ba zai iya 6ata,sallama sukayi sannan suka shiga cikin falon ba kowa sai su harira suna kai kawo a falo zuwa kitchen,YARIMA yace bismillah ku zauna ke harira kawo musu abin sha,ya kallesu yace”i’m coming,sannan ya hau sama,zuwa yayi yace”baby na albishirinki”,tace”goro”yace”kinsan bak’in namu kuwa?”,tace”a,a”,yace”k’awarki ta malaysia UMMU AYMANA sune sukazo”,IMAAN tayi k’ara ai kuwa ta warci hijab tasa sai k’asa,YARIMA yana cewa kiyi a hankali fa karki fad’i,ina ta tafi,tana sauka taje da gudu ta rungume ummu aymana tace”kai anty na shine kuka yi mana surprise”,tace”kiyi a hankali irin wannan gudu haka ai sai ki jima kanki ciwo”,a kunyace ta koma ta zauna suka gaisa da Mustapha,sannan tace”anty ina haneefah kuma ban ganta ba?”,tace”na bar ta a gida wajen mai reno yanxu zamu wuce ai,saidai in mun dawo musha hirar mu”,daidai nan YARIMA ya iso ya zauna IMAAN ta kalleshi tace”kanajin anty wai tafiya zasuyi”,tace”haba dai tun yanxu”,

Mustapha yace”ai ba hira mukazo ba,mun fito daga wani wajen ne nace mu biyo,amma zamu kawo muku wuni wata rana,amma bani number wayar ka zan kiraka in zamu zo”,yace”ok to kawo in sa maka,nan dai sukayi musanyar number IMAAN ma ta d’auki ta ummu aymana,sun d’an ta6a hira sannan suka fice,har ummu take tambayar IMAAN ya ta ganta babu cikin,IMAAN ta zayyane mata komai,ummu tace”ayya srry bakomai Allah ya kawo mai albarka”,dukansu suka amsa da ameen…..

****

Bayan sallah magrib ne IMAAN taje 6angaren su mama,wajen nafeesat,ta iske su a falo suna zaune ta shiga tare da yin sallama,zuwa tayi har k’asa ta durk’usa ta gaishe da mama,mama ta kalleta tace”yata lafiya naga kin rame kinyi fari haka?”,IMAAN ta sunkuyar da kai tace”lafiya lau mama”,

Mama tace”a,a fad’a min gaskiya kodai baki da lafiya ne,ko shureim yana miki wani abin ne?”,girgiza kai tayi tace”ba komai mama”,tace”a,a ban yadda ba akwai wani Abu”,bari in kira mijin naki,d’aukan waya tayi ta kira YARIMA yana d’auka tace”kazo ina kiranka…….

    *'YAR MUTAN KAZAY CE*????

ANTY MAIMOUNATH????
+22969164943
[27/10, 21:45] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

       *STORY*
             *&*
          *WRITTEN BY*:✍????



    *ANTY MAIMOUNATH*????

Wannan shafi na sadaukar dashi ne ga ‘yan grp din:
Alk’awari fan’s,khadijatul Imaan fan’s,nuriyya fan’s,inajin dadin addu’o’inku,mi yenty……

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page3⃣7⃣~3⃣8⃣

YARIMA ne ya shigo tare da yin sallama, yazo kusa da k’afafuwan mama ya zauna,mama ta kalleshi tace”shureim”,yace”na’am mama”,tace”me yake damun yarinyar nan naga duk ta rame,kalleta ka gani da kyau kamar marar lafiya ko bata cin abinci ne da kyau?”,ya d’ago yace”mama lafiyar ta lau,kuma tana cin abinci”,tace”yanxu mai lafiya haka yake,ita tak’i ta fad’a min abinda yake damunta,kaima gashi nan kana 6oye min”,

Yace”wly mama ba komai”,mama tace”to bakomai amma ta rame haka,kodai damunta kakeyi ne?”,nan take kunya ta lullu6e YARIMA dan ya gane tambayar inda ta dosa,Sosa keya yayi yace”a,a mama”,tace”haba d’an nan me ka d’aukeni na tabbata haka ne,kunyar fad’a min takeyi shiyasa tace ba komai, to bari kaji ba haka ake zaman aure ba,ya kamata ka rink’a kyale musu yarinya tana hutawa,in duk mazan duniya kamar kai suke da ba kowace mace bace zata jure zaman auren,itama hak’uri ne da ita,amma nasan abinyi duk laifin mai martaba ne da yasa waziri yake baka abinda bai kamata ba,IMAAN da YARIMA dai kansu a k’asa dan kunya,tace”ku tashi ku tafi zanga wazirin gobe insha Allah,

Tashi sukayi suka nufi 6angaren su,da shigar su ya janyota ya rungume ture shi tayi tace”ka manta akwai su harira ne”,yace”ban manta ba,dan suna nan saï in k’i rungume my wife”,tace”nidai ka daina salon su fito su gan mu ko”,yace”so what dan sun gani,mu da gidan mu sai a hana mu shak’atawa,suzo ma su fice tunda sun gama girkin”,

Kiransu yayi sukazo yace”kun gama aikin ko?”,harira tace”eh har mun kai dinning”,yace”good,to ku fice ku tafi sai da safe kuma”,tashi sukayi suka d’auki abincin su suka fice….

Zuwa yayi ya kulle k’ofar falon ya dawo,suka nufi dinning table,da kanshi ya zuba mata abincin,ta kalleshi tace”wannan duka ina zan iya cinye shi gaskiya yayi min yawa”,yace”bakiji abinda mama tace bane yanxu,cewa tayi kin rame kamar marar lafiya, nima sai yanxu naga hakan so ki cinyeshi duk ko inyi miki dura”,

Baki ta zumburo amma batace komai ba ta fara cin abincin,suna tsakar cin ne ya kalleta yace”baby na kinsan me mama take nufi da ina damunki?”,tace”a,a”,ido d’aya ya kashe mata yace”wai nufinta ina damunki wajen kwanciya”,take IMAAN ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya tace”ka daina ni banso”,yace”an gama gimbiya matar yarima”,

* *

Cikin dare IMAAN ta farka tana murk’ususu har YARIMA ya tashi,ganinta a zaune yasa ya tashi da sauri ya kama ta yace”baby na meye”,da k’yar tace”marata take ciwo duk sanyin A.C da ke d’akin amma ita zufa takeyi dan wuya,ya rungume ta yace”oh my God,sannu baby na kinji,zai daina bari in miki dubara kafin safe in kira doctor”,shimfid’eta yayi ya tashi ya nemo ruwan zafi da d’an karamin tawul yazo ya cire mata Riga tana k’i ma yace”meye kuma ki bari magani ne zan miki dan ki samu bacci”,y’a barta daga ita sai pant,yana tsoma tawul a ruwan zafi yana d’an dadanna mata a marar yana kawo sauqin rad’ad’in ciwon,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button