KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Kashe kayan kallon yayi yake ya rufe k’ofar falo sannan ya jata sukayi bedroom d’inshi,tana ganin ya shiga toilet ta tashi taje d’akinta dan sauya kata zuwa rigar bacci, ta shafa turaren humran ta mai shegen,ta rufo d’akin ta goma bedroom d’in yarima,a daidai lokacin ya fito daga toilet yana goge jikinshi da tawul,dan Jan magana yace”baby na zo ki goge min jikina mana”,wucewa tayi ta hau gado ba tare da ta kalli inda yake ba,murmushi yayi,saï da ya feshe jikinshi da turare mai dad’i sannan ya fesa Air freshner a d’akin ya kunna A.C haba nan da nan d’aki ya d’ume da k’amshi zuwa yayi ya hau gadon tare da kashe wutar d’akin saï duhu ne ya mamaye ko ina ya shige blanket d’in shima,ya lalube ta yace”baby na juyo kiji wata magana,a rashin wayo na imaan saï ta juyo,bakinsu ya had’e waje d’aya ya tura hannu cikin rigar ta,wasa ya fara da k’irjinta,mutsu mutsun kwatar kanta ta shiga yi,a hankali ya rad’a mata yace”kinsan dai ba wani Abu zanyi ba,just inason in samu nutsuwa ne,wlhy a matse nake”,kyaleshi tayi saï da ya gaji dan kanshi ya kyaleta tayi bacci….
* ****
Da safe,yau imaan ce da kanta ta shiga kitchen dan tayi musu break,dankalin turawa ta d’ora a wuta dan ta sulala shi,ta fasa Kwaï tasa Maggi,onga,da dai sauransu,ta kad’a kwan sosai,ta fere sulalanlan dankalin nan,ta d’ora mai a wuta da yayi zafi saï ta d’auki dankalin nan ta tsoma a ruwanKwaï saï ta zuba a kwaskon tuyar,haka takeyi har ta gama,saï kuma ta had’a ruwan tea mai kayan k’amshi citta da kanumfari,saï da ta jera komai a dinning table sannan taje ta tashi yarima a bacci,ya shirya ya zo sukayi break ya kalleta yace”kai baby na amma gaskiya kin iya dahuwa”tace”da gaske kakeyi tayi dad’i?”,yace”of course,i’m serious yayi dad’i”,tace”thank u dear”,yace”me kikace?inda d’an k’ara fad’a inji”,rufe ido tayi,yace”kai baby na ba dai kunya ba,yaushe ne za’a daina dan ni take cuta”,to ni zan tafi asibiti,inaso in biya in gaishe da su mama tukun,tace”nima zanje,kafin Jamila tazo”,yace”ok mû tafi to”,
Nafeesat kawai suka iske a falon tana kallon t.v,yarima yace”ke yau baki zuwa skull ne kika zauna kuna kallon t.v?”,feenat tace”a,a saï da gamma”,yace”ina mama?”,tace”bata fito ba tana d’akinta”,yace”ok zan kira ta in na isa asibiti,juyowa yayi ya ma imaan pick a goshi yace”baby na na wuce saï da yamma ko?”,a kunyace tace”to Allah ya kiyaye hanya”,yace”ameen my nurul qalb,sannan ya fice…
Imaan zuwa tayi ta zauna kusan feenat tace”wai me kike kallo da safiyar nan?”,tace”uhmm wato saï da kuka gama soyayyar ku sannan kika ganni ko”,imaan tayi mata dukan wasa tace”kai feenat banda sharri a yaushe mukayi soyayya a nan”,tace”hmm ba wani sharri gaskiya na fad’a”,tace”to naji dai,an Sanya ranar bikin k’awata jamila,nan da two weeks”,feenat tace”haba dai?kai amma zamu sha biki,ko dan wannan an bar mû mû shak’ata”,imaan dariya tayi tace”kai duk murnar bikin ne haka saï kace ke za’ayi wa auren”,saï da mama ta fito suka gaisa sannan imaan ta koma 6angaren ta,ta iske su harira suna zaune,bata jima da zama ba saï ga jamila,sun sha hira Wanda rabin hirar duka ta shirye shiryen biki ce….
BAYAN KWANA BIYU
IMAAN yau ta fara sallah amma bata son yarima ya gane saï dai kash tana sallah magrib yarima ya isko ta wani dad’i ne ya ziyarci zuciyar shi,d’akinshi ya wuce dan gabatar da wanka,imaan kuwa bataso haka ba,saboda tasan yau yarima bazai barta tayi baccin dare ba…….
*'YAR MUTAN KAZAY CE*????
ANTY MAIMOUNATH????
+22969164943
[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍????
*ANTY MAIMOUNATH????*
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page4⃣1⃣~4⃣2⃣
Bayan sallah isha’i,suna zaune a falo yarima ya kalli IMAAN yace”baby tashi mu tafi d’aki”,cikin zokana IMAAN tace”tun yanxu,gaskiya ni banjin bacci kallo zanyi,amma kaje ka kwanta mana,ni saï na ida kallo tukun”,kallon ta yayi yace”baby na banson zolaya fa,kinsan abinda nake nufi ai,please tashi mû tafi”,nok’ewa tayi,kashe t.v d’in yayi cak ya d’auketa,tace”ni ka saukeni zan tafi da k’afafuna”,yace”no bari dai in kaiki da kaina,saï tsoro kamar wata sabuwar amarya”,rufe fuska tayi,bai direta ko ina ba saï bisa gadon baccin shi,yace”ina zuwa ya shiga toilet,tashi tayi ta cire zanen da ta d’aura bisa rigar baccin ta,ta shige blanket tayi baccin k’arya,ko da ya fito bai tsaya wani b’ata lokaci ba,direct gado ya nufa,kiss yayi mata a baya yace”nasan ba bacci kikeyi ba”,kyaleshi tayi,hannu yasa ya juyo ta yace”baby na meyasa har yanxu kike tsoron in kusanceki?”,ya k’ara cewa”ko har yanxu ciwo kikeji?”,kai ta gyad’a mishi,yace”dan kina tsoro ne yasa kikejin ciwon ai,so please ki daina tsorona,ni ne fa prince d’inki,babu abinda zai faru,wannan tsoron ko sabuwar Amaya bazata yi ba ai”,murmushi tayi ta cusa kanta a k’irjinshi Wanda yake d’auke da yalwataccen gashi mai santsi,kissing d’inta ta shiga yi yana wasa da ita duk dan ta saki jikinta,a hankali yake isar da sak’onshi zuwa gareta Wanda a halin yanxu ta fara kar6ar sak’on dan yaji alamu,duk ta saki,da haka ya samu ya cire mata rigar jikinta,ya gangara k’asa saï ta kama hannunshi,a hankali ya rad’a mata”please baby na kiyi hak’uri a matse nake kuma ke kanki kinsan da haka”,a haka dai har ya samu kanta,amma fa taji jiki dan in tak’aice muku labari saï da yarima yayi round biyu kafin safiya kuma ko wanne saï ya gamsu yake kyaleta,hmm amma yarima yanason kashe ‘yar mutane,amma kuma yasa shagwa6ar babyn tashi dan kuka take mishi yanda kukasan sabuwar Amaya haka ta koma mishi saï raki takeyi bayan,k’ugunta,k’irjinta haka dai take fad’a har safe,
* ****
Da asuba yarima da kanshi yayi wa IMAAN d’inshi wanka sannan tayi na tsarki ta d’auro alwala,da ta fito yarima ya tafi masallaci,d’akinta ta nufa a can tayi sallah ta koma bisa gado tayi kwanciyar ta dan bacci ne a idonta,da yarima ya dawo bai isketa a d’akin ba murmushi yayi ya wuce zuwa d’akinta ya isketa a kwance hawa gadon yayi tare da rungumar ta,gabanta ya fad’i ras,dan tana tsoron yace zai k’ara dan kad’an ne daga cikin aikin yarima,marar ta ya shafa yace”Allah yasa na samu baby a daren jiya”,lub tayi ta kyaleshi har bacci ya d’auketa,
Ko da ya shirya zuwa asibiti bai tashe ta ba dan yasan baccin gajiya ne takeyi,Allah sarki baby na saidai ki rink’a hak’uri da buqatata,nasan kina da k’ok’ari da juriya,hmm….imaan kuwa sai k’arfe 12am na rana ta tashi a lokacin har su harira sun ida abincin rana,da ta sauko taci abincin suna zauna a falo ita da su suna bata labari mai dad’i suna ta dariyarsu,wayarta ne tayi ringing d’auka tayi dan tasan mai kiran, ringing d’inshi na musamman ne,hmm masoya Kenan….tace”shine baka tasheni ba kayi tafiyarka”,yace”sorry baby gani nayi kinajin dad’in baccin ne,kuma nasan kin gaji jiya shiyasa”,a shagwa6e tace”banso ka daina”,yace”an gama ranki ya dad’e gimbiya matar yarima”,tace”uhm zolaya ko,to ya aiki?”,yace”lafiya klau saï kewarki”,tace”kai dear duk ma yaushe ne muka rabu”,yace”da safe mana yanxu kuma wajen awa nawa nayi ban ganki ba”,tace”to ka dawo mana ba saï ka ganin ba”,yace”idan na dawo akwai abinda zaki bani?”,tace”eh ga abinci an gama”,yace”haba dai me zanyi da wani abinci ni ke nakeso”,tace”ai ni daman taka ce”,yarima mamaki yakeyi wai yau IMAAN ce take mishi wannan maganganu ko dan ba a gabanshi take ba,yace”da gaske kike baby na”,ita kanta saï da yace haka sannan taji kunya,ba tare da tayi mishi sallama ba ta kashe wayar tana murmushi,su harira ma murmushin suke kansu a k’asa,ta kallesu tace”na gan ku shine kuke min dariya ko”,sukace a,a ranki ya dad’e,6ata fuska tayi tace”zamu 6ata da ku fa,ban ce muku karku sake ce min ranki ya dad’e ba?”,harira tace”au mantawa mukeyi ne wlhy kiyi hak’uri”,IMAAN tace”to shikenan ya wuce,inaso ku d’aukeni tamkar k’awarku kunji ko”,sukace to,