KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin bikin jamila sai k’aratowa yake yanxu yayi saura sati d’aya ranar muna zaune ni da yarima a gida kasancewar week-end ne,naseer yayi sallama ya shigo,nayi mishi sannu da zuwa,muka gaisa ina zolayarshi ina ce mishi ango ya shirye shirye kuma?”,dariya yayi yace”alhamdulillah muna cikin yi”,yarima ya bashi hannu suka gaisa yace mishi to bismillah sai ka zauna ko wato an Sosa maka inda yake maka k’aik’aiyi ko”,dariya yayi ya zauna yace”har na kaika,karka manta a lokacin naka ko baccin dare bakayi”,dariya sukayi su duka,yarima yace”kai friend banda sharri fa”,yace”ah to ai gaskiya ce ba wani sharri malam”,IMAAN tashi tayi ta kawo mishi ruwa da jus yace”thank u gimbiyar yarima,sunkuyar da kai IMAAN tayi cikin kunya,sannan yace”to daman zuwa nayi inji dame dame ake buqata na shagalin ‘yan matan amarya?”,yarima yace”kai shine kuma sai wajen matata zakaxo ka tambaya,kaje ka tambayi sauran mana”,naseer yace”saboda gani nayi itace babbar k’awarta shiyasa”,yarima yace”to a cire matata a ciki ah to”,naseer yace”meye nufinka na a cireta,kana nufin bazata je ba ko me?”,yace”zataje mana,amma me ya had’ata da wani shagalin ‘yan matan amarya ? “,naseer yace”ok daman na tambayi jamila ne amma tak’i ta fad’a min wlhy”,sai a lokacin IMAAN tayi magana tace”to kawai ka basu abinda ya samu,kuma ma ai da abokai zakuyi shawarar abinda ya kamata ku bayar ko?”, ya kalli yarima yace”to kai kaji,tashi mu tafi dan Allah kazo ka mak’ale a gida kamar mace”,dariya IMAAN tayi mishi,yarima yace”haba dai mutum a week end d’in ma bazai huta ba”,naseer yace”kai da hutu sai an gama biki kaji ma da kyau,please tashi muje akwai mutanen da ke jirana a gida”,yarima yace”to ai ka bari in yi wanka ko?”,yace”naji to amma kayi Sauri”,yarima ya kalleni yace”baby na muje ki shirya ni kar wannan angon mai zumud’i ya cika ni da surutu”,imaan kuwa kunya taji ganin naseer yana wajen,tace”kaje dai ka shirya,ko nima in shirya sai muje ku saukeni a gida,yarima yace”me akeyi a gidan,bazaki ba sai jibi dan bazaki fita yau ba kuma jibi kice wajen saka lalle ko me ma ake cewa,dan haka kiyi zamanki har in dawo,yana gama fad’ar haka ya fice zuwa d’akinshi…..

Suna d’an ta6a hira ita d’à naseer,yarima ya sauko,subhanallahi IMAAN ta furta a cikin zuciyarta,tace”wane irin kyau ne Allah yayi wa yarima na,hmm wai fa yariman ta kunji fa jama’a,wato IMAAN an fad’a tarkon so…k’ananan kaya ne yasa bak’in jeans da farar riga mai ratsin ja a jikinta,tamkar wani balarabe haka yarima yake,gashin kan nan nashi sai walk’iya yake idon shi manne da bak’in glass,zuwa yayi yace”to ango mai zumud’i tashi mû tafi,naseer a zolaye yace”kai friend wannan wanka kamar kaine angon,ka ganka kuwa,yau zaka had’a fad’a a duk inda muka wuce”,dukan wasa yarima ya kai mishi yace”kai karka had’ani da baby na mana,kana ganin yanda ta had’e fuska ba”,dariya nasser yayi yace”ah to ai da gaskiyar ta ka fita a haka ai yau mata sai sun kawo maka hari”,IMAAN kuwa ta cika kamar ta fashe,yarima ne yaje kusanta a hankali yace”baby na rabu dashi dan kawai ya tsokane ki ne,ai kinsan ke kad’ai ce a zuciyar prince,prince naki ne ke kad’ai,a haka ya lalla6a ta ya samu suna fita…..

Ba yarima ne ya dawo gida ba sai dare saboda shirye shiryen da suke kuma an had’u da abokai aka zauna aka shirya komai kan party da komai,an shiya party ne na ango da abokanshi amarya ma da nata abokan,wannan kuma yarima ne ya d’auki nauyin shi,hmmm biki budiri Kenan…da ya shigo babu kowa ko su harira ma sun tafi 6angarensu,kai tsaye sama yayi d’akin gimbiyar tashi ya nufa,da ya shiga tana kwance a k’asa tana kuka,a ranshi yace toh fa ai kuma aiki ya sameni baby rigimar ta motsa, da Sauri ya isa wajenta ya tasheta zaune yace”baby na lafiya kike kwance a k’asa kuma kina kuka,me ya faru?”,cikin kuka tace”ba kaine nayi tafiyarka ba sai ni kad’ai a gida,kun tafiyarku wajen ‘yan matan ku”,ya salam yarima ya fad’a,yace”baby na wane irin ‘yan mata kuma,inda muke ko matan ma babu,kuma ko da akwai ma me zanyi dasu”,ita dai kukanta takeyi,ya tasheta tayi tsaye,janta yayi suka je bakin gado suka zauna yace”baby na kalleni”,juya kanta gefe tayi ya juyo da ita yace”please just look at me”,kallon shi tayi cikin ido yace”baki yadda dani bane ko me?”,bata yi magana ba,yace”karki manta a k’asar waje na zauna inda ga mata sai wacce nakeso zan za6a,amma ko kallo basu isheni ba,ni mace bata isheni kallo ba harkar gabana nakeyi kawai,shine ban bi mata a can ba sai a nan kuma inada matata”,tace”to ba kaji abinda naseer ya fad’a ba,mata suyi ta kallonka,ai shiyasa nace mû tafi tare”,murmushi yarima yayi ya lak’uce mata hanci yace”kai baby na akwai kishi,ki daina shakku a kaina, babu wata bayan ke,hmm uhm uhm yarima mû dai ba ruwan mû ko sis….

Yace”tashi kiyi wanka duk kin 6ata kwalliyarki please ki daina kuka kunji?”,kai ta d’aga mishi yace”good girl,bari nima inyi wanka sai muci abinci dan na tabbata kema bakici ba,ana nan ana kukan kishin miji ya fita fuska ta rufe tace”banso fa tam”,dariya yayi yace”baby na rigima sannan ya fice……..

  *'YAR MUTAN KAZAY CE????*

ANTY MAIMOUNATH????
+22969164943
[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

       *STORY*
             *&*
          *WRITTEN BY:*✍????





       *ANTY MAIMOUNATH*????

WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA,KAI HAR DA MA MAK’IYANA????????

DEDICATED TO:
MAMAN AHMAD(ANTY MARDIYYA KA’OJE)
MAMAN FAIRUZA

Page4⃣3⃣~4⃣4⃣

Ana gobe d’aurin aure IMAAN ta rok’i yarima da tanason zuwa wajen amarya,kallon ta yayi yace”baby na ki bari mana gobe ba sai kije ba”shagwa6e mishi tayi tace”haba dan Allah duk k’awayen mû a can fa,saï ni kad’ai kuma ni ce babbar k’awarta idan ban je ba ai bazata ji dad’i ba”,yace”ai ita kanta tasan cewa yanxu aure ne a kanki so dan me zata zarge ki da k’in zuwa,ai ba zaman kanki kikeyi”,kyaleshi tayi ta koma kan gado ta kwanta,murmushi yayi dan yasan fushi ne tayi,yace”fushi ne kikayi baby na,sorry tashi ki shirya in muka saukeki zan wuce wajensu naseer suna jirana,saï kira yake yi min a waya”,dad’i taji tace”Allah da gaske kakeyi?”,kai kawai ya d’aga mata,sannan yace”ina falo kiyi Sauri,ai bata d’auki lokaci ba wajen shirin,ta fito cikin shigarta na wani tissu coton blue mai kyau ta d’auki jakar ta da takalmi su kuma farare ne mayafin ma fari ne,tazo tace”to mu tafi na gama”,yarima ya kalleta sama da k’asa,yace”amma bakiso zuwa ba ko?”,tace”why?,inason zuwa mana,me ka gani?”,yace”da wannan shigar haka zaki tafi,kalli mayafin da kika saka”,tace”basu yi bane ko kuwa?”,yace”eh mana,ina fa sukayi kinsan kuwa yanda nake da kishi,kinzo kinyi kwalliya kamar kece amaryar,kije ki saka hijab,in zamuje party tare kin saka mayafin shima babba zaki sa”,komawa tayi ta sanya hijab d’in duk dan ta samu tafiyar ne,ta gane take taken shi duk dan ya hanata ne,tace”to yanxu fa?”,yace”yauwa ko ke fa mu tafi”,

Saï da suka sauketa a gida sannan suka wuce,daman direba ne yake tuk’in motar,IMAAN gaishe da su umman ta kawai tayi ta fice gidansu Jamila,na shiga inda na iske wasu k’awayen mu,suna gani na waje ya d’au shewa,wai ga imaan,mun gaisa suke cewa hmm kaji manya ba’a ganinku saï da dalili,nace”baku je inda nake ba ai”,na kalli jamila na fara mata”amaryar naseer daga yau shikenan ‘yar baiwar Allah kwana saï gidan naseer”,jamila tace”naji dai dan ki sani kuka ne kuma bazanyi ba”,imaan tace”hmm zaki fad’awa ‘yan garinku,dan wlhy da ganin mijin nan naki ba wasa”,dariya suka yi su duka,jamila tace”oho dai,wato dan ke kin tsallake shiyasa kike min iskanci ko?”,imaan tace”yes,ni kam yanxu na huta,dan wannan abu kam ba’a magana dai,in kinje kin bani labari,hhhhh,kuma in nine naseer bazan d’aga miki k’afa ba har safe,hhhhh…jamila dukan wasa ta kai mata tace”wai yaushe kikayi baki haka”,imaan tace”oho”…..nan na wuni saï wajen 5 na yamma na koma gida dan in taya umma aiki,gashi daman maryam bata nan taje k’unshi da kitso,nidai yarima ya hana inyi k’unshi yace wai indai dan auren ne bai amince ba,ban jima da shiga gidan ba yarima ya bugo min waya wai za’a zo d’aukana,nace mishi ka bari mana bayan sallah magrib,yace”in nak’i fa,ki shirya kawai ki jirashi yana nan zuwa”,kashe wayar nayi ina gunguni,umma ta kalleni tace”mijin baki kikeyi wa gunguni?”,zumburo baki tayi tace”umma to ya bari mana zuwa bayan sallah ba saï in tafi ba”,umma tace”to yak’i bazai bari d’in ba,kin ganki ko banson sakarci”,zama nayi har direba yazo muka tafi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button