KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Na iske an kar6o min anko(uniforme) na daga wajen dunki,na tambayi harira ko har yarima ya iso ne,tace min”a,a bai zo ba”,a raina nace shine ni zai sa ni inzo gida wato shi yana can yana shak’atawar shi ko,hmm,na kalleta nace”OK shikenan kun gama abinci ne?”,tace”eh mun gama gashi can mun jera su a dinning”,imaan tace”ok,ta d’auki ankon ta ta haura saman d’akinta,tayi wanka aka kira sallah tayi sallah ta,tana zaune tana addu’o’inta har aka kira isha’i,saï da ta gama komai tayi simple kwalliyar ta ta fito falo ta zauna,ita da su harira,yarima kuwa saï k’arfe 9pm na dare ya shigo,sannu da zuwa tayi mishi shima d’in dan tana ganin su harira ne da bazata mishi ba,hmm kumullon mata Kenan,wato kishin ne ya motsa,su harira suka gaishe shi ya amsa tare da wucewa,su harira ma saï da safe suka min suka fice,ina kallon t.v tazo ya zauna yace”baby na kallo akeyi?”,nace”uhm kawai”,wayarshi ta shiga ruri,ban bi ta kanshi ba,ya shiga amsa wayoyinsa,tashi ma nayi na bar mishi falon na tafi d’akina nayi shirin kwanciya,can saï gashi ya shigo,yace”baby na har kwanciya ne zakiyi?”,nace”uhm,inaso ne in tashi da wuri”,yace”dan yin me?”,nace”dan zuwa wajen d’aurin aure mana”,yace”ba zakije ba”,tace”dan me kuma”,yace”kawai meye na zuwa d’aurin aure kuma saï kace wata tsohuwa,da rana zan aiko a d’aukeki dai”,kyaleshi tayi,ta kwanta,yace”yau nan kike sha’awar mu kwana kenan?”,bata amsa mishi ba,zuwa yayi ya sauya kaya zuwa na bacci ya dawo d’akin…..
Da ya dawo d’akin shima gadon ya hau tare da juyota ya fara bata hot kisses,kwace bakinta tayi tace”ni bacci nakeji”,yace”ai kuwa baki isa ba,kwana biyu ban kusanceki ba,yanxu kuma ina buqatar hakk’ina ne”,bata yi magana ba ya cire mata rigar jikinta ya cire tashi,ya shiga murza kkirjinta yanda yakeso,saï kuma ya kai bakinshi ya kama….saï da tayi d’an k’ara yace”yadai?”,tace”ciwo nakeji”,yace”sorry a hankali zanyi,tsotsa yake cikin kwarewa,kai yarima d’an duniya ne,a haka ya samu ta bada kai bori ya hau,hmm,na kyale dai sis ta hanani magana????
Tunda safiya yarima ya fita saboda d’aurin auren,mutane sun hallara sosai ta kowane 6angare,masha Allah jama’a sun taru kasancewar abbansu jamila shima d’an kasuwa ne, k’arfe 9am na safiyar asabar aka d’aura auren jamila da Dr.Nasser,miyetty Allah…..6angaren su feenat na shiga,tana zaune a falo,nace mata ya nake ganinki a zaune baki shirya ba,kuma nasan ki da nawar shiri”,tace”yanxu nake cewa inje in gani ko kin shirya”,imaan tace”ni nawa ba wahala ba wata kwalliya sosai zanyi ba kinsan halin mutumen nawa”,dariya feenat tayi tace”sosai ma kuwa,bari in tashi in shirya to”,imaan tace”ina mama?”,tace”tana d’akin abba”,imaan tace”lafiya har yanxu bai fita fada ba?”,tace”lafiya klau kawai hutawar shi yake yi”,tace”ok bari in tafi muyi Sauri kar ya kira ni bamu ida ba”,
Basu jima da shiryawa ba yarima ya kirata yace”su fito ga direba nan tana jiransu,tace”to”,dukansu anko ne a jikinsu saï kuma wasu kaya da suka d’auka dan sawa da dare lokacin party…..a gidansu ya saukesu,da suka shiga maryam tana shirin fita ita ma,tace”lah anty imaan Ashe zakizo”,imaan tace”to me zai hanani zuwa bikin babbar k’awa,ina umma?”,tana can gidansu Jamila,tace”ok to mu tafi, abba ma yana wajen maza ko?”,maryam tace”eh yana can”,muka rangaya mu uku muka tafi gidansu Jamila, da shigar mu suka fara min shak’iyanci wai saï yanxu yarima ya barni nazo,banza nayi dasu na wuce wajensu umma na gaishe su ita da maman su Jamila duk na iske su waje d’aya,sannan na dawo wajen amare,imaan tace”armaryar naseer wai k’arfe nawa ne partyn dan ni ban ma ga katin ba”,Jamila tace’k’arfe 9 zuwa 11pm na dare”,imaan tace”ah amaryar zamani har kinsan lokacin ko,haba kin fad’a musu idan kuka shiga hannun Nasser yau”,Jamila tace”ai honey na mai tausayi ne kamili ba ruwanshi”,hmm inji imaan,wato idan ana sallah ba’a magana dai….saï lokacin magrib muka watse saboda kowa yaje yayi shirin shi na party…..
Saï da naji gabana ya fad’i ganin motar yarima a k’ofar gidan mu,muna isowa shi ma yana fitowa daga bayan motar,feenat da maryam gaishe shi kawai sukayi suka shige gida dan sun ga fuskar shi ba annuri,hmm…ina wuni imaan tace dashi”,yace”lafiya,ina ta kiranki a waya baki d’aga ba why?”,ina kika shiga?”,imaan tace”ina gidansu Jamila mana ba gashi daga can ne Muka fito ba,kuma ni wallahi wayar ma banji k’aran ta ba”,tace”ok yayi kyau”,ki shirya ni da ke zamuje wajen partyn”,tace”da ka tafi kawai ni saï mu tafi dasu feenat”,yace”haka nayi niyya sunje da k’awayen amarya,ki zauna cikin shiru zanzo da time yayi”,yana kaiwa nan ya shige mota,tsayawa tayi yake kallon shi,hmm yau ‘yan ikon sun motsa Kenan……
Luv u all fan’s….
*'YAR MUTAN KAZAY CE????*
*ANTY MAIMOUNATH????*
*+22969164943*
*
[02/11, 22:18] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍????
*ANTY MAIMOUNATH????*
SAK’ON TA’AZIYYA ZUWA GAREKI KAWATA KHALEESERT ALLAH YAJIQAN ABBA DA RAHAMA YASA YA HUTA,KU KUMA ALLAH YA BAKU HAK’URIN JURE RASHIN SA….
MU DA MUKAYI SAURA IN TAMU TAZO ALLAH YASA MU CIKI DA KALMAR SHAHADA..AMEEN!!!
RAYUWAR KENAN,WANDA YAJE BAI YI GAGGAWA BA,KAI DA KK NAN BAKAYI JINK’IRI BA…..KAICO DUNIYA????????????
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page4⃣5⃣~4⃣6⃣
K’arfe 9pm na dare tana bugawa yarima yana isowa a ya kirata a waya yace ta fito yana k’ofar gida,bai sauko ba daga motar kasancewar babu kowa a gidan duk suna gidansu jamila…..cikin shirinta na wani material mai shegen kyau da tsada,anyi mata ado a gaban rigar,dunkun riga da skirt ne,yayi mata kyau sosai, ko da ta fito yana zaune cikin mota a gidan baya,da Sauri wani ya bud’e mata sharin guda ta shiga kusa da yarima,shima ya d’au wanka kamar shine angon,IMAAN ta kalleshi ta 6ata fuska tace”wannan shigar irin ta angwaye ce Kayi,saï kace kai ne mai amaryar”,murmushi yarima yayi tare da shafa fuskar ta yace”nima ango ne ai”,IMAAN ta kalleshi fuskar ta da alamar tambaya,yace”yes ba gaki nan ba,ai kece amaryata ko?”,6oye fuskar ta tayi a jikinshi,hmm wato IMAAN an fara cire kunyar yarima ko….motocin su jere suke da na ango da amarya har zuwa inda aka shirya partyn,fitowa sukayi suka jera,ango da amaryar shi IMAAN da prince d’inta,zuwa sukayi suka zauna inda aka tanadar dan ango da amarya,imaan tana gefen amarya,shi kuma yarima yana gefen ango,
Kid’a kawai yake tashi a wajen inda k’awayen amarya suke cashewa,har da su maryam da feenat,can aka buqaci ango da amarya su fito fili,kid’a ya canza a lokacin da suka fito akace suma su taka,su IMAAN dai ‘yan kallo ne,dan yarima yace bbu wata rawa da zasuyi salon a rainashi cikin yara,hmm yarima akwai son girma….bayan sun sha raye raye kowa ya nemi waje ya zauna akaci gaba da shagulgulla,yarima ya bada tarihin naseer hk IMAAN itama ta bada na jamila,an raba abinci da abin sha,yarima wayarshi tayi k’ara ya tashi ya fita saboda wajen akwai hayaniya..IMAAN ma tashi tayi tace ma jamila”k’awata ina zuwa”,ta nufi inda ta hangi su feenat,tana zuwa tace”hmm wato ko nemana bakuyi ko?”,feenat tace”me zamu baki ai mun san kina tare da mijinki ne,kuma k’awar amarya”,ya bamuga kinyi rawa ba?”,IMAAN ta kai ma feenat dukan wasa tace”banson zolaya fa,kinsan dai yayanki bazai ta6a barina inyi rawa ba”,dariya suka mata feenat da maryam sukace”kai amma an baroki a baya gaskiya,mû dai mun cashewar mû sosai”,IMAAN tace”oho muku dai”,suna cikin hirar ne saï ga yayan jamila nan yazo suna gaisawa da imaan,yake tambayar ta ya kwana biyu,tace mishi lafiya klau,ya hidima?”,yace”alhamdulillah”,basu Ankara ba saï ganin yarima sukayi a tsaya yana kallonsu,imaan gabanta ne ya fad’i ras,yayan jamila ya mik’a mishi hannu dan su gaisa,amma yarima ya k’i,d’aga mishi hannu kawai yayi,yace”sa’ar ka d’aya kai yayan jamila ne da saï na hukuntaka,yanxu ba da bane,yanxu ita matar aure ce,dan haka ka fita harkar matata”,yace mishi”kayi hak’uri gaisawa kawai mukeyi walhy ko a da ma babu komai a tsakanin mu”,yarima yace”gaiduwa da izinin wa?”,ya juyo ya kalli imaan yace”da izinin wa kika zo nan har kuke gaisawa?”,shiru tayi,tsawa ya daka mata yace”ba dake nake ba?”,su feenat kuwa tuni sun fice dan kar a had’a dasu..nace”nifa wajensu feenat ne nazo shine da ya ganni yazo muka gaisa,bbu komai a tsakanin mû dashi”,ficewa yayi yaje ya zauna,imaan kuwa har idonta ya ciko da ruwa dan ta gama tsorata da yanayin shi,imaan cikin d’ari d’ari haka nan ma taje ta zauna kusan shi,tace”kayi hak…..a zuciye yace”enough,yana huci kamar mayunwacin zaki”,naseer ya kalleshi yace”friend meye haka ne wai,meyasa ka cika zafin rai ne?”,d’aga ma naseer hannu yayi yace”kaima excuz me dan Allah”,tuni idanuwanshi sun rine dan fitina,hmm,waya ya d’auka ya kira direba,yace”ka jira a waje za’a maidata gida”,da Sauri imaan ta d’ago ta kalleshi tace”ba’a tashi zan tafi,kuma ai saï mun kai amarya”,yace”ba zakije ba,gida zaki in kuma kina musu dani bismillah”,Jan bakinta tayi shiru dan gudun kar tayi magana kuma ya k’ara mata tsawa,naseer ne yace”haba ya zaka mata haka ranar auren k’awarta ta kace ta tafi gida tun yanxu”,yace”eh haka nayi niyya,tashi yayi yaja hannunta bai tsaya ko ina ba saï a waje,yace ma direba kai ta gida….