KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Da suka isa gida,imaan tana shiga kai tsaye d’akinta ta nufa zuwa tayi ta kwanta a gado tayi ta kuka har ta gode Allah,saï 12pm saura yarima ya shigo gidan,saï da yaje tayi wanka ya ida komai nashi sannan ya nufi d’akinta,yana shiga da imaan ta ganshi saï ta koma can k’arshen gado ta fara sana’ar tata,wato kuka,ita a zaton ta dukanta zaiyi,hmm duka kuma cabb….,zama yayi yake sauraron ta,can saï yace”me aka miki kikewa mutane kuka,ko kawai niyya,Kenan kinsan kinyi laifi ko?”,imaan tace”kayi hak’uri wlhy gaisuwa ce kawai”,yace”banson ji,ba laifinki bane,laifina ne da na barki kikaje,toh fa yau naji iko ita da bikin k’awarta guda…tashi yayi ya fita daga d’akin,
Da safe tana falo a zaune ya fito cikin shirin fita saï k’amshin turare yakeyi,imaan tace”ina kwana?”,yace”lafiya,ki had’a min breakfast ana jirana”,imaan tace”in shirya mû tafi?”,ba tare da ya kalleta ba yace”ina Kenan?”,tace”gidan amarya mana”,yace”ba can zanje ba,gaisuwar surukai zamu kuma ba gidan naseer d’in ne za’a had’u ba”,tace”to direba ya kaini mana”,yace”no gobe zan kaiki da kaina”,bata saké cewa komai ba ta tashi take ta had’a mishi break fast,da ya gama yazo yayi mata kiss a kunci yace”sai na dawo by”,hmm Ashe ma zaka sauko ai ko dan ka samu….????yana ficewa ta d’auki wayarta ta kira jamila taji a rufe,a ranta tace hmm wato su k’awata an ji jiki kenan, ita kad’ai take dariya,ni kuwa nace dariyar mugunta…maryam ta kira tace mata”kina gida ko kina ina?”,tace”gamu nan ni da feenat a gidan amarya”,imaan ta zaro ido tace”yaushe feenat ta fita har kuka tafi?”,dariya maryam tayi tace”ai daman a nan gida muka kwana bata koma ba”,imaan tace”shine kukayi musu saukon zuwa gida ko”,feenat ta kar6i wayar tana zolayar ta tace”gamu nan muna shak’atawar mû a gidan amarya”,imaan tace”naji dai ku bani jamila dan na kira wayar ta a kashe”,tace”ok to gata nan”,ta mik’a ma jamila wayar,imaan ta shiga mata shak’iyanci tana cewa”k’awata ya jiki,shine har da kashe waya wato dan ma kar a dameku ko?”,jamila tace”ke ni lafiya ta klau kiji ma,babu abinda ya faru”,imaan tace”k’aryane wannan mijin naki mai rawar kai”,jamila tace wlhy nake gaya miki,kedai bayani saï kinzo”,tace”ok to yace wai saï gobe sannan zai kaini,kinsan halin mutumen nawa”,tace”ok Allah ya kaimu saï kunzo……
‘YAR MUTAN KAZAI CE????
*ANTY MAIMOUNATH????*
*+22969164943*
????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
*STORY*
*&*
*WRITTEN BY:*✍????
*ANTY MAIMOUNATH*????
*OH ALLAH!*
*SHOW US WAY*
*TO THE JANNAH*
*AMEEN!!!*
*JUMA'AH MUBARAQ*
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page4⃣7⃣~4⃣8⃣
Saï da yamma yarima ya dawo gida a gajiye,bayan yayi wanka yaci abinci yace ma imaan muje kiyi min tausa duk jikina ciwo yake,imaan ta kalleshi tace”ka bari mana zuwa dare”,yace”no yanxu nakeso”,tashi muje”,jan hannunta yayi saï d’akinshi,
Tausa take mishi yana wani lumshe idanuwa,hannu yasa yana shafo cinyar ta,yanayin yanda take mishi tausar ya saka shi cikin wani irin yanayi sakamakon lallausan hannunta da ke sauka bisa gadon bayanshi….kyaleshi tayi a haka har bacci y’a d’aukeshi,hmm lallai yarima an gaji,auren aboki ba wasa ba….tashi tayi ta fita daga d’akin ta koma falo ta kunna t.v tana kallo….
Feenat ce tayi sallama ta shigo,zuwa tayi ta zauna bisa kujera sannan ta kalli imaan saï ta fashe da dariya,imaan tace”ke Kuma fa lafiya daga zuwa kin sani gaba kina dariya?”,tace”wlhy jiya na tuna,amma gsky yaya bai kyauta miki ba,bikin babbar k’awa guda ace mutum ya dawo gida”,imaan ce ta jefe ta da filon kujera tace”eh d’in naji dai,Allah yasa wani ustaz ya aureki ki zama matar kulle gaba d’aya”,
Feenat cikin dariya tace”wlhy a,a ba ameen ba gsky karkiyi min baki”,dariya imaan tayi tace”hmm yayi kyau mudai a kawo mana na kirki”,tace”insha Allah,ke jiya na samo wani handsome fa”,
Imaan tace”ke haba dai bani labari”,tace”hmm kin ganshi kuwa mai bala’in kyau,abokin naseer ne a can wajen party muka had’u sunanshi Affan”,imaan tace”ba wani kyau ai duk kyan shi bai kai mijina ba ah to”,feenat tace”cabb lallai ma anty imaan d’in nan to ya fi yaya shureim kyau”,
Imaan ta zaburo takai mata dukan wasa tace”ke wlhy k’aryane ba dai mijina ba,ai shi cikin maza saï an tona kiji ma da kyau”,feenat tace”hhh mai da wuk’ar anty na kowa nashi dai ya sani,bari wata rana zan kawo muku shi”,imaan tace”to Allah ya kaimu”,feenat tace”ameen,wai ina yayan ne?”,imaan tace”yana bacci”,feenat tace”cabb bacci Kuma a yanxu da goshin magrub d’in nan?”,tace”tun d’azu ya kwanta wai ya gaji yace”,
Feenat tace”hmm kedai aiki ya sameki Allah ya k’ara miki hak’urin zama dashi”,imaan tace”kamar ya?”,tace”zafin zuciyar wannan nashi mana”,imaan tace”hakan ma ni yayi min tunda babu damar wata mace da zata shigo min gida ah to”,dariya feenat tayi tace”hhh su anty iyayen kishi lallai”,…….
Saï da imaan taga an kusa Kiran sallah magrib sannan ta nufi d’akin yarima ta iske ya tashi yana toilet,fita tayi taje d’akinta dan ta gabatar da sallah itama…..
* *
Da dare suna zaune a palo wayar imaan tayi k’ara tana dubawa taga jamila ta d’auka tace”assalamu alaiki amarya ina kika bar angon naki ne?”,cikin d’ar d’ar jamila tace”ke ni ba wannan ba,ya fita wai sayen kaza,wlhy na tsorata me yake nufi da sayo kasar ne?”,
Ai kuwa me imaan zatayi in ba dariya ba,har saï da ta kular da jamila,ta kashe wayar ma,hhhhhh,
Yarima ya kalleta yace”ke da wa haka kike dariya?”,tace”jamila ce”,yace”to me tayi kike mata dariya?”,imaan tace”sirrin mû ne na k’awaye”,yarima yace”hmm yayi kyau,tashi muje nima akwai sirrin da zamuyi dake”,ta mak’ale kafad’a tace”nak’i wayo ko,ni kallo zanyi”,yace”ai kuwa baki isa ba saï munje”,tashi muje kawai”,tashi tayi shi Kuma ya kashe t.v d’in tare da kama hannunta suka nufi sama….
KASHE GARI
Su imaan suna break fast yarima yanaso zai fita wajen aiki,wayarshi tayi ringing ya ciro ta a aljihun wandon shi,ya kara a kunne yayi sallama yace”friend ya akayi ne?”,naseer yace”please ka bani imaan in tana kusa”,yarima yace”lafiya dai ko?”,yace”da sauk’i dai bani ita dan Allah”,yarima yace”ok gata nan ya mik’a ma imaan wayar bayan sun gaisa ne yace”dan Allah taimako nkso kiyi min”,imaan tace”wane irin taimako Kenan?”,
Dr.naseer yace”please kizo ki tayani ba k’awarki hak’uri wlhy akasi ne aka samu banyi da niyya ba,amma saï kuka take tak’i ma in taimaka mata wai ita gida zata”,nan take imaan ta harbo jirgin inda zancen ya dosa,wata irin kunya ce ta kama ta,tace”to gamu nan zuwa karka damu”,yace”ok nagode ba ma prince wayar”,ta mik’a mishi wayar tare da zama a kujera ta dafe kai,amma kuma cikinta cike yake da dariya,bayan yarima ya gama wayar ne yace”d’auko hijab d’inki mu tafi in na saukeki saï in wuce”,tace”ok to…..
A lokacin da suka isa gidan naseer yana palo dafe da kai,yarima ya mik’a mishi hannu suka gaisa,imaan ma ta gaishe shi,yace”tana d’aki ta rufe daga ciki kiyi knocking idan taji muryar ki ta bud’e”,
Imaan zuwa tayi tayi mata knocking kyalewa tayi jamila,a zaton ta naseer ne,saï da imaan tayi magana sannan ta tako da k’yar tazo ta bud’e mata tare da fad’awa jikinta ta fashe da kuka……..
*YAR MUTAN KAZAY CE*????
*ANTY MAIMOUNATH????*
*+22969164943*