KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Yarima yace”kana asibiti ne?”
Naseer yace”eh yanxu na shigo wallahi duk ruwa ya jik’amin jiki,

Dariya prince yayi yace”ai ni bazan iya zuwa ba cikin wannan ruwan,idan ya tsaya zan shigo akwai hira..

Nasser yace”ta samu Kenan,

Eh yace dashi,sai anjima bye…

Yar mutan kazay ce????

    *Anty Maimounath*????

[10/9, 01:44] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

Story & written by:✍????

  *Anty Maimounath*????

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
(Allah ka bamu da kanka inka basu su bamu basa bamu????)

wannan shafin naku ne writers na grp da bazarmu,Allah ya kare min ku a duk inda kuke,ya rabamu da sharrin masu sharri.ameen!!

Bismillahi Rahmanir Rahim

Page5⃣

Sai wajen karfe 5:00 na yamma ruwan ya tsaya,a lokacin ne yarima ya fito dan zuwa asibiti wajen abokin shi docto naseer..

Yana shiga cikin asibitin kowa ya tsaya yana kallon shi bare ma matan,

Saboda sun ga yaro dan kwalisa ga kudi ga mulki,da k’yar yake amsa musu gaisuwar wanin ma sai yan bayan shi suke amsawa.

Nocking yayi ya shiga cikin office din, Naseer yana ganin shi ya taso ya rungume shi yace”ur welcome my friend”zauna ka bani labari,

Prince yayi murmushi yace”ai ka bani abin sha tukun ko? kai mai son jin labari,dariya naseer yayi yace”na matsu inji da me kazo ne ai.

Prince ya nisa yace”friend aure fa za’ayi min kwanan nan,

Dariya naseer yayi mai isar shi sannan yace”a mafarki ka gani ko?dan a iya sani na baka da wata budurwa da kake so bare akai ga maganar aure.kai da kake wulak’antasu yaushe ma ka tsaya da yarinya da har maganar aure ta shigo,ko da yake cewa kayi za’a yi maka,maybe abba ne ya ga ya dace kayi auren.

Yarima kallon shi yake yana murmushi har ya gama,sannan yace”to ka gama ko da saura”?

Naseer yace”na gama to fada min”
[10/9, 01:45] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

Story & written by:✍????

    *Anty Maimounath*????

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
(D.B.W.A)

Wannan shafin naku ne fan’s na khadijatul Imaan, naga sak’onninku nagode kwarai Allah ya bar k’auna,Luv u all????????

Bismillahir Rahmanir Rahim

Page6⃣

Sun tarda umma na zaune a bakin gado Imaan kuwa saï baccin ta takeyi saboda allurar da akayi mata mai sa bacci ce,

Har k’asa yarima ya duk’a ya gaishe da umma,duk k’asaita irin ta yarima yana da ladabi da biyayya dan ya samu tarbiyya sosai a wajen mahaifanshi,

Yarima yace”umma ina kwana,ya mai jiki?”

Umma tace”lafiya lau,jiki alhmdllh da sauk’i ta samu bacci ma ai,

Yace” me ya sameta umma?

Tace”ga doctor nan yayi maka bayani,

Yarima ya kalli naseer yace”friend me yake damunta ne”?

Naseer yace”ku duka ya kamata inyi ma bayani tunda ku duka abin ya shafa,kai a matsayinka na babban doctor ita kuma mahaifiyarta ce…

Muje office dina can din zaifi saboda nan ba’ason yawan surutu ana buk’atar ta samu hutu sosai…

Suna shiga yace musu su zauna,

Naseer ne ya nisa yace”a gaskiya bincike ya nuna mana menses ne ta fara kuma a iya tunani na idan akayi mata aure zai daina,ma’ana akwai mata dayawa irinsu Wanda saï an musu aure sun sadu da mijin sannan ya daina,

Dan haka nake baku shawarar ayi auren dan samun lafiyar ta ta…..

Umma kunya abin ya bata,tashi tayi ta fita daga office din..

Tana fita yarima ya kai ma doctor naseer duka yace”amma kai dai ba karamin dan iska bane wallahi,a gaban in law(sarakuwa) na kake fadar wannan magana,

Naseer saï da yayi dariya mai isar shi sannan yace”to laifi nayi ai gaskiya na fada????

Yarima yace”Wace gaskiya bayan kasa naji kunya,

Naseer yace” amma fa a gaskiya ina tausaya wa wannan yarinya,ina zata iya da fitinar ka..

Yarima yace”kai iskancin ka ya isheni fa,waye mai fitinar”?

Kai mana naseer ya bashi amsa sannan ya cigaba da cewa”she is too young prince,so please ka bi musu yarinyar su a hankali nidai na fada maka,

Wai me ka daukeni ne naseer?sanin kanka ne mata basu dameni ba ko a lokacin da muke malaysia ko kallonsu bana yi.

Hhhhh yarima Kenan ita wannan ai ta daban ce,kuma na jinjina mata ta saye zuciyar prince mai wulak’anta mata…mai ja musu aji..

Saï washe gari aka sallamo su Imaan daga asibiti,umma ce takeyi ma abba bayanin abinda likita yace game da ciwona,


BAYAN SATI DAYA

An kawo kudin auren Imaan da komai har an saka musu rana, nan da two weeks saboda sun ce basu son a d’auki lokaci sosai.

A makaranta kuwa,su Imaan ne da wasu k’awayen su a zaune a bayan ajinsu suna hirar shirye shiryen su da zasuyi na auren k’awar su Imaan…

Jamila ce ta kalli Imaan tace”ke kuma fa,lafiya kikayi ma mutane tagumi bakiyin magana kodai tunanin angonki kkyi?????

Imaan ta kalle ta tace”ke banson iskanci wallahi jamila,dan bani da aikin yi saï in rinka tunanin shi,akan me”,

D’aya daga cikin su mai suna fiddaussi tace”wallahi k’arya kikeyi kice bakison shi,kina ganin yaro kamar balarabe dan gayu dashi,ai wallahi yarima yayi ba k’arya????

Jamila tace”ke fiddaussi a gaban matar shi kike kod’ashi haka

Saï fiddaussi tace”to ai gaskiya na fada,

Jamila tace”to wai ma bari in tambayeki,a ina kika tab’a ganin prince din har kika san yana da kyau kamar balarabe”?

Fiddaussi tace”a t.v na ganshi ana hira dashi,Ashe babban doctor ne,hmm su Imaan matar doctor????

Imaan tace”ke fiddaussi ya isheki fa,ba doctor ba dai matar asibiti ce ta murgud’a mata baki????


Kwanci tashi asarar mai rai,yau bikin su yarima yayi saura kwana hudu….b’angaren biyu sai shirye shirye akeyi bare ma gidansu yarima,abinka da shine d’a d’aya a gidan,kuma yaro mafi soyuwa a zuciyar sarki…

Gidan su Imaan ma ya cika da ‘yan uwa,anty khaleesert ma sunzo ita da yaran ta,yaya Habeeb ne bai iso ba sai ana gobe daurin aure zai zo..

Kanwar umman mu ma tazo daga Kano dan can take da zama ita da mijin ta da ‘ya’yanta…tare da ‘yar ta sukazo wacce muke kusan shekaru daya da ita,sunanta Aseeyah,tanada shekara 17 da wata shidda ni kuma 17 years gareni….wannan kenan…..

please kuyi maneji da wannan ina buzy ne wallahi na gaji????‍♀

*’yar mutan kazay ce????

 *Anty Maimounath*????

[10/9, 01:45] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

Story & written by:✍????

       *Anty Maimounath*????

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
(D.B.W.A)

Dedicating to:

PRINCE ABDALLAH(yayana)
UMMU BASHEER
BADEEYAH(Queen beauty)
HUSSAIN(Atk)
HASSAN(Yayana na kaina)
DADYN FATEE
KING BOY(Isah)

Bismillahir Rahmanir Rahim

Page7⃣

Rana bata k’arya saidai uwar d’iya taji kunya inji hausawa,

Yau ranar daurin auren PRINCE SHUREIM AND KHADIJATUL IMAAN,

IMAAN tasha kyau har ta gaji dan tunda aka Sanya musu rana ake gyarata ciki da waje????

Ga wasu abubuwan sha da na turare anayi mata,

Yau ma Anty khaleesert ce a daki tasa Imaan ta sanye wani had’in kayan mata daga sokoto tasa a kawo mata musamman dan wannan ranar,

Imaan kuwa tace ita abun ya isheta bazata sha ba,

Anty khaleeseet ta kalle ta tace”wai Imaan bada ke nake ba kika hau gado kika kwanta,ki sauko shi sha nace fa,wallahi zan kira umma tam….

Ina ma buntsuro baki tace”nifa anty na gaji da wannan abun da kike ta bani,haba dan Allah ba ya isa haka nan ba,

Wai ma na meye ne?

Dan naji wasu ma ko dad’i babu kamar magani,

In magani ne to a daina bani dan ni lafiyatdakinki babu abinda ke damuna….

Anty tace”ai kuwa Dole ki sha kuma kina gamawa ga kaza nan tana jiranki,

Zaro ido????tayi tace”haba anty Wace irin kaza kuma,ni bani da yunwa,gaskiya ana takura min a gidan nan ta fada a shagwab’e…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button