KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Anty tace”ai bakinki da gidan nan yau ne,shi ma kuwa ana daurawa zamu kaiki dakinki muga ta gaddama????
Ni babu inda Zani ta fada a shagwabance,
K’awayen amarya kuwa sai shige da fice sukeyi….
Anko ma kala uku sukayi,Wanda kala biyun yarima ne ya dau nauyin yi musu shi….
Jamila ce da wasu k’awayen su ‘yan sshool dinsu suka shigo cikin ankon su na wani yadi mai shegen kyau pink color ne yy musu kyau sosai,
D’akin su Imaan suka shiga inda suka iske Imaan tana kwance ido duk yayi mata jawur alamar taci kuka har ta gode Allah,tunanin ta zata bar gidansu da ‘yan uwan ta da k’awayen ta…
Gashi gidan sarauta ba’ayi musu zirga zirga sai dai lokaci zuwa lokaci…Allah sarki sabuwar rayuwa,rayuwar gidan miji☺…
Jamila ce ta kalleta tace”ke kuma meye abin kuka a nan zaki cikin gidan sarauta gidan angon ki prince shureim,ko da yake nasan kukan dadi ne kikeyi ma,ta fada cike da zolaya????
Imaan ta kalleta tace”jamee banson haka fa ki barni inji da abinda ke damuna tam,
Fiddaussi tayi dariya????tace”babu wani abinda ke damunki kawai tsabar dad’i ne yake damunki kawai????
Su duka suka kwashe da dariya,Imaan tayi banza dasu…
A daidai nan ne aka hasko daurin auren nasu,prince shureim Abdallah with Khadijatul Imaan Haladu…
Daurin auren da ya samu halartar dumbin jama’a na k’asa da na waje,yarima ma abokan shi sun zo daga malaysia inda yayi karatu Kenan indai mai karatu bai manta ba can ne yarima yayi karatunshi…
Can daga d’aya bangaren kuma aka hasko yarima da abokan shi sai tsokanar shi suke shi kuma yana murmushi,dan bai cika dariya ba cikin mutane wai sai a rainaka inji yarima fa bani na fada ba????♀
Yasha kaya na alfarma wata dakakkiyar shadda ce ruwan k’asa tayi matuk’ar yi mishi kyau…
Nan su jamila suka d’auki guda da shewa suna cewa shikenan an d’aura kin zama matar prince shreim,ba gaddama yi nayi bari na bari????
A nan Imaan ta shige cikin mayafinta ta fashe da kuka,
Jamila tace”sai da kika gama kalle angwan ki tsab sannan ki shige cikin mayafi kina mana kukan munafirci????
Daga tsakar gida suka jiyo magud’iya tana gud’a tana kirari tana cewa”alhmdllh aure ya d’auru khadijah ta zama ta yarima Allah ya bada zaman lafiya.ni kuma Maimounath nace ameen!!!
A daki kuwa yarima ne yake Kiran Imaan tak’i d’agawa,
Babu yanda su jamila basuyi da ita ba kan ta d’aga tace babu ruwansu baxata d’aga din ba..
Jamila tace”oho miki karki d’aga din wallahi zakiyi bayani ne in kika shiga hannun shi,duk ki gama rainin sense(hankali)din naki..ku kuzo Muje akwai sauran shirye shiryen mû fa
Yarima kuwa ya kira ta ne dan ya face mata abokan shi sun hada musu dinner yau da misalin karfe 9:30pm zuwa 11pm na dare..
Text yayi mata yace”gdmrng my wife,how are u? Hope kin tashi lafiya na kira baki dauka ba,tsoron ne ko kunyata aka fara ji tun yanxu,daman dan in fada miki ne friends dina da sukazo daga malaysia ne suka shirya mana dinner yau misalin karfe 9:30pm zuwa 11pm so ki fada ma k’awayen ku sai ku zauna cikin shiri 9:00pm za’azo daukar ku OK.
*your husband*
Bayan ta karanta ne ta kira jamila a waya…..
kuyi hak’uri da wannan ina a halin tafiya ne,sai na isa insha Allah zaku jini
ku sani cikin addu’ar ku????????
nagode da k’auna????
yar mutan kazay ce
*Anty Maimounath*????
[10/9, 01:45] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:✍????
*Anty Maimounath*????
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
(D.B.W.A)
Khadijatul Imaan fan’s kuyi hak’uri na rashin jina kwana biyu ina cikin tafiya ne amma alhmdllh na iso lafiya,kuma zan cigaba daga inda na tsaya.inajin dadin comments naku Allah ya bar zumunci.Luv u all????????????
Dedicated to:
Maman Ahmad(mardiyya ka’oje)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Page8⃣
Jamila tana dawowa saï tace mata”amarya meye kike kirana lafiya ko?”
Imaan ta kalleta tace”cewa akayi ku shirya anjima akwai dinner karfe 9:30 za’a zo daukanku,jamila tayi dariya tace”ya kike fidda kanki kice za’a zo daukan mû dai,ai kece ta farko a tafiyar ma????
Shiru ta mata bata ce komai ba.
Karfe 9:30 kuwa nayi sukaji dirar motoci a k’ofar gida,
Daman kuwa k’awayen amarya sun shirya,amarya ce dai taso yin gaddama wai ita babu inda zata,
Saï da anty khaleesert ta zare mata ido sannan ta shirya saï kumburi take tana k’arawa ita a Dole wai an takura mata…wannan Kenan
Suna fita kowa ya rikice sakamakon wasu irin mahaukatan motoci da suka gani masu shegen tsada,
Motar da amarya ta shiga daga ita saï angonta prince saï kuma dreba Wanda bai ganin su ma..
A hankali suke tafiya,nan yarima ya janyo Imaan yana shaqar dadaddan kamshin turaren jikinta,
Ita kuwa saï kiciniyar kwatar kanta takeyi ita a Dole batason abinda yake mata,amma fa kuma ya birgeta sosai cikin shigar shi da shadda galilah ga wani fitinannan k’amshi da yakeyi shima har wani lumshe ido takeyi????
Hhhhh ni kuma maimounath nace anaso ana kaiwa kasuwa????
Prince yace da ita cikin sansanyar murya mai dadin sauraro”hey baby calm down karki manta fa yanxu i’m ur husband”,so ki tsaya karki ba kanki wahala dan nasan kema kinason kwanciya jikin mijinki ko,
Murguda baki tayi????kai mijin ake murgud’a ma baki..hmm
Tace”Allah ya kiyaye yaushe nace inason kwanciya jikinka”?
Yace mata”ba saï kin fada min ba ina ganewa a haka ma,kuma idonki,jikinki ya nuna hakan,
Murmushi yayi ya k’ara cewa”karki damu yau a gidan mijinki zaki kwana OK”
Ko kallon shi bata yi ba…
Sun iso wajen dinner,kofar motar ma saï da aka Budé musu nan da nan yarima ya sauya fuska jinin sarautar ya motsa????bare ma da yaga dogarai gaba daya ya rikid’e zuwa yariman shi…
A hankali suke takawa har zuwa inda aka tanadar dan ango da amarya,
Kowa saï kallon su yake,dan couple din nasu yayi,sunyi bala’in dacewa da juna…
Anci ansha masha Allah,a nan ne kuma doctor naseer abokin yarima ya kyalla ido yaga jamila ai fa shikenan shi ma yace ya samu matar aure..
Time din tashi bai yi ba Imaan ta farayin hamma wai ita bacci takeji,yarima ya kalleta yace”bacci ne kikeji”?
Kai ta d’aga mishi,shi kuwa mirmushi yayi dan ya gano ta yace”to tashi in kaiki gida da kaina,kafin sauran suje gida kin shirya,
Ta kalleshi”shirin me zanyi kuma,da naje wanka zanyi in kwanta,
Dariya ya mata yace”baby kin cika tsoro dayawa fa so please ki rage,dan gidan miji zaki..ban ce mishi komai ba…
Mun iso kofar gida na yunk’ura zan fita saï naji k’ofar motar a kulle,
Na waiwaya na kalleshi nace”ka budemin in fita ni bacci nakeji,
Kallonta kawai yakeyi sai can yace”to ko dai in juya motar mû tafi gida in sunzo sun biyomu a baya,
Ido ta zaro????tace”wane gida kuma ban da nan”?
Murmushi yayi ya janyota
Saï da ya tsotse mata baki tas sannan ya saketa shi ma din dan kuka ta saka mishi wai ita ba ‘yar iska bace????????
Yace” ai ba haramun bane ko,ni mijinki ne Wanda dubban jama’a sun shaida hakan,so daga yanxu banson in k’arajin wannan maganar a bakinki.,Har na fara bacci naji ana cewa ku fito da amaryar mana dare yanayi ai,saï da gabana ya fad’i,hhh su Imaan anji tsoro????????dole aje gidan miji????
Allah sarki haka aka fito da amarya tana kuka aka kai ta dakin abban su,
Nasiha mai ratsa jiki yayi mata a nan kukan nata ya k’aru,umma ma tayi mata..
Nan fa ta rukunk’ume umma ita bazata je ba,tana kuka umma na kuka da k’yar aka banb’are ta a jikin umman…