KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Kowa saï da ya tausaya mata abba ma dan yana namiji ne,daurewa ne kawai ya yi amma ya tausaya mata saboda Imaan k’arama ce…

Da isar mu, anty khaleesert ce take rik’e dani har cikin gidan,

Subhanallahi fad’in yanda gidan ya tsaru ma b’ata lokaci ne saboda katafaren gida ne da ya k’unshi b’angarori da dama,

Ta ko ina kuwa barorine ke ta hidima,duk ta cikin mayafina nake wannan gulmar,nace hmm lallai Dole ne yarima ya rink’a girman kai..

Kai tsaye b’angaren su hajiya aka fice dani inda mun tarda ta da jama’ar ta itama,ga kuma masu yi mata hidima suma suna aikinsu,

Sun tarbemu da fara’arsu hajiya tace”ku kawo min ‘yata kusa dani”,anty ta kaini kusa da ita na zauna kaina a k’asa,amma har lokacin ban daina zubar da hawaye ba…

Allah sarki aure yaqin mata????????inji hausawa….

Nan naga tarairaya kamar ta maidani cikinta hk takeji dan so,saï da aka gaggaisa sannan ne akai mana rakkiya har b’angaren yarima,

Muna shiga nan ma wata alk’aryar ce,kamar ba a Nigeria ba,

Kowa saï yabon gidan yakeyi,to ba Dole ba gidan saurata????wasa ne????

Nayi mamakin ganin su jamila cikin d’akin,ko ya akayi suka rigaye mû?oho

Muna shiga suka d’auki gud’a wasu na shewa wai ga Amarya ta iso,har bakin gadona anty ta kaini na zauna Wanda shima yasha shimfid’a ta alfarma,zanen gadon milk ne mai kyau…komai na d’akin milk color ne,

Babu abinda ba’a tanadar mana ba kama daga abinci har abin sha kala kala gasu nan ni wani abin mamaki ma hidima suke sosai kamar ba da kud’i ake sayen wani abin ba,

Nan dai su anty da sauran ‘yan rakiya suka ce su gida zasu fice,anty tace ma su jamila ku mû tafi ko,kokuwa sai angwaye sunzo tukun”?

Sukace eh,nace”yanxu anty tafiya zakuyi bazaku kwana ba,

Anty ta zaro ido????ke rufa mana asiri,mû kwana fa sai kace Wanda muka kawo ki daga wani gari hmm,kiyi hak’uri,taso ma kiji…na tashi jiki a sanyaye na bita har falo,

Nasiha ta k’arayi min sannan muka koma cikin dakin,su anty suka fice suna cewa asuba ta gari mudai munyi gaba,

Suna fita na cire mayafina nazo zansa hannu a cikin kwanan abincin da su jamila suke ci,nan jamila ta rik’e min hannu tace”ke wa yace miki amarya tana cin abinci ranar da aka kawota”?ba’a cin abinci fa tam nidai ba ruwana,

Nace inji uban wa?ni ba rai ne dani ba ko,to saï naci din saï me zai faru,na murgud’a mata baki????

Dariya tayi???? tace”wannan kuma yarima ne zai fada miki abinda zai faru????

12:00pm daidai mukaji sallamar abokan ango,nayi Saurin rufe fuskata da mayafina,suka iso har inda muke,sukace”yan matan amarya ya kuke”?

Suka amsa da alhmdllh mun gode Allah,

Sai naseer yace”to ku nawa zamu saye bakin amarya dan munga tak’iyin magana,

A nan ne yarima yayi magana yace”kai tak’i bazatayi ba din????

Dariya naseer yayi yace”to muyi addu’a a gurguje dan naga wannan angon in aka jima korar mu zaiyi,

Nan dai sukayi addu’a muka shafa sun d’an tab’a barkwanci har naseer yake fada ma yarima cewa”friend a dai bi a sannu dan yarinya ce????

Duka yarima ya kai mishi yace”friend banson iskanci fa”,

Naseer dariya ya sakeyi ya kalli inda jamila take yace”dear taso in kaiki gida,dan bazan yadda ki shiga motar kowa ba????

Bayan yarima ya rakasu ya dawo dakin..ya tadda Imaan tana kuka,

Ya isa kusa da gadon yace”sorry baby,kiyi hak’uri”

Kyaleshi nayi,ya hayo gadon ai kuwa nan gabana ya fada dukan uku uku…

Hhhhh ba dukan uku uku ba,yayi tara tara dai????????

Ku biyo ‘yar mutan kazay kuji ya zata kaya tsakanin ango da amarya????

*Anty Maimounath*????

+22969164943
[10/9, 01:45] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????

Story & written by:✍????

    *Anty Maimounath*????

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
( D.B.W.A)

OH ALLAH! RESPOND TO OUR DU’A,HEAL OUR SICKNESSES,DEFEAT OUR ENNEMIES,GUIDE OUR LOVED ONES & GRANT US JANNATUL FIRDAUSSI,YA RABBIL ALAMIN.JUMMAH MUFEEDAH.

WANNAN SHAFIN NAKU NE YAN GRP HAUSA NOVELS ONLY,KUNA RAINA BAN MANTA DAKU BA,LUV U ALL????????????

Bismillahir Rahmanir Rahim

Page9⃣

Yarima yana hawa gadon rungumota saï ta fara kiciniyar kwatar kanta hmm Wace ke Imaan… Yarima yace”tsaya mana wai duk wannan tsoro ne ko kunya,in tsoro ne kuwa ai kince bakijin tsoro na in kin manta in tuna miki…

Ta zumburo baki tace”ni ba tsoron ka nakeji ba,kawai ka sakeni da daina tab’ani bacci nakeji,

Yarima yace”bacci kuma a daren amarcin naki zakiyi bacci,akwai tsarabar da nazo miki da ita ai kinaso ko?

Girgiza kai tayi,sannan tace” a a nagode ka rik’e kayanka,yarima dariya yayi yace”kenan kinsan tsarabar ko,tace”a a kawai ban buqata ne,

Yace”ok tashi kije kiyi wanka ki d’auro alwala nima zanje in dawo,nafila zamuyi ta godewa Allah da ya kawo mana wannan rana,…yana fad’ar haka ya fice…

Da ya dawo har ta rufe k’ofar,su Imaan sarkin tsoro????

Saï dai kash abinda bata sani ba shine ko ta rufe zai iya budewa..key yasa ya bud’e da ya shiga saï ya hangota lullube cikin bargo har ta fara bacci,

Cikin sanda ya shigo sai kace wani b’arawo????????

Kai tsaye wajen gadon ya nufa ya hau ya shige bargon shima,cikin bacci ne taji kamar alamar da mutum a bayan ta..zumbur ta mik’e zaune ta shima tashi yayi,

Ta kalleshi tace”dan Allah meye haka ina cikin bacci na ka tasheni,yace”yaushe na tasheki,ke dai kika tashi kanki ke wai mai wayo ko,kin jiki jikin mijinki,

A shagwabance tace”ni ka daina fada min banso,

Yarima yace”to tashi kiyo alwala da nace ko,

Tace”ina off banyin sallah,

Kallonta yarima yayi yace”haba amaryata banson k’arya fa nasan da kina sallah,dan nasan lokacin da kike menses din ki,

Ido ta zaro????ka sani fa kace”?,yes ya bata amsa,dan haka tashi kina b’ata min time,sum sum ta fice dan ganin fuskar shi ba wasa,

Sun gabatar da nafila yarima yayi musu addu’o’i sosai saboda masanin al’qur’ani ne duk da ba a Nigeria ya zauna ba,wannan Kenan….

Kafin yarima ya gama komai nashi ita har ta Haye gado????shima yana idawa ya bita gadon…

Da yawan shi gadon ya janyota ya fara mata kiss ita kuwa sai nok’ewa takeyi abinka da ba saban ba hmm,

Yarima fa ya fara sakin layi sumbata yake kaiwa ko ina????sai kuma a hankali kid’an ya fara canza Salo,

Yana a wata duniyar kukan Imaan ne ya maidoshi hankalinshi,

Kuka take tana cewa”ni ka daina min haka wallahi ban tab’a yi ba????

Yarima ne ya rungumeta yace”is OK yi shiru bazan miki ba,kwanta kiyi baccin ki,

Da k’yar ta iya bacci a k’irjinshi dan gani take idan tayi bacci zai sakeyi mata ne…

 *WASHE GARI*

Kiran sallah ne ya tashe su daga bacci,yarima ne ya fara bud’e idon shi ya kalli Imaan tana ta baccin ta,

Tashi yayi ya shiga toilet, sai da yayi wanka sannan ya d’auro alwala,ya fito har yanxu bata farka ba..

Zuwa yayi bakin gadon ya yaye bargon da ta rufa dashi yayi d’an bubbuga ta yace”baby na wake up,ki tashi kiyi sallah zan tafi masallaci,

Ko da ta bud’e ido,sai sukayi ido biyu dashi,tayi Saurin shigewa cikin bargon wai ita kunya hmm..murmushi yarima yayi dan yasan dalilin rufe idon nata,

Har ya kusa k’ofar dakin ya dawo yazo ya rad’a mata a kunne yace”karki manta sai kinyi wanka sannan,

Daga cikin bargon tace”ana wannan sanyin babu abinda zai sani inyi wanka,

Yace”ai kuwa wanka ya zama Dole,ko ki tashi kiyi kafin in dawo ko kuwa ni in miki,

Ido ta zaro????tace”wai dolene sai yanxu zanyi,anjima nayi,me zai sani wanka da asubar nan ta k’ara fad’a cikin mak’oshi Ashe yaji abinda tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Leave a Reply

Back to top button