KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Murmushi yayi yace”bari in na dawo zan fada miki,????toh fa…
Bayan ta gama sallah tana zaune kan dardumar tana addu’o’in ta,sai taji ana sallama a falo,tace wacece warhaka, ta tashi ta lek’a sai taga Ashe jakadiya ce,zuwa tayi ta durk’usa har k’asa tace”ranki ya dade gimbiya ina kwana”,
Ta amsa da lafiya lau,jakadiya lafiya kuwa meke tafe saké?,
Jakadiya kanta a k’asa dan kunya tace”eh uhm..daman uhm..Imaan tace”ki fada mana,tace”daman hajiya ce ta aiko ni tace ko da abinda zan taimaka muku dashi na aiki,
Imaan kuwa da batasan dawan garin ba,wai amarya da tayi kashi a mod’a inji hausawa????
Sai tace”ayya mun gode babu wani aiki a yanxu dai,ki gaishe min dasu kafin inje,
Jakadiya tace”to to ranki ya dade umarni naki cikawa tawa, an gama,nan ta tashi zata fita sai ta had’u da yarima zubewa tayi k’asa jiki yana karkarwa dan tsoro ta gaishe shi ya amsa da k’yar dan haka yake amsa musu gaisuwarsu,
Ya kalleta yace”lafiya me ya faru”,cikin in ina ta maimaita abinda ta fada ma imaan,da yake yarima yasan al’adar gidan su nan take ya gane abinda take nufi,yace”tashi ki tafi”,nan ta tashi tana cewa godiya nake yarima mai jiran gado…
MENENE AL’ADAR MASARAUTAR?
A al’adance indai yarima mai jiran gado yayi aure wato dan sarki Kenan,idan yayi aure to a washe garin ranar za’a tura jakadiya wacce itace tayi renon yarima tun yana k’arami,za’a tura ta dan taje daukan zanen gadon da suka kwanta da amaryar shi,a gani ko ta fita kunya????
Wannen Kenan,
Yarima ya shigo d’akin tana nunke abin sallar,yazo ya rungumeta ta baya yace”good morning baby na da fatan komai normal ko”?
A hankali ta amsa,yace”kinyi wankan kikayi sallar ko kuwa dai,
Kwace kanta tayi daga gareshi saboda cikin kunne yake mata maganar ita kuma duk kasala yake saukar mata irin wannan abinda yake yi…
Tace”banyi ba,yace”to inda zonan in gani ko gaskiya ne,nok’e kafada tayi sannan tace”nak’i bazan zo ba,
Yace”naji to muje mû kwanta ko,fiddo ido tayi tace”a ina cabb bazan kwanta ba,ka rink’ayi min abinda akace mana haramun ne namiji yana tab’a mace..????imaan Kenan,murmushi yarima yayi dan yasan imaan batasan komai ba na rayuwar aure,sai ana kwatanta mata,
Yace”naji bazanyi miki komai ba zo in fada miki wata magana,nan ma ta nok’e,hmm su yarima an sha fama kam…
Zaunar da ita yayi ya fada mata komai na aure babu abinda ya b’oye mata,nan imaan taji wani irin kunya ta kamata ai ba shiri ta gudu falo,
K’arfe 9:30am Nafeesat tayi sallama ta shigo,in bazaku manta ba nafeesat kanwa ce ga yarima,kuma bazata wuce imaan din ba,zan iya cewa sa’annun juna ne,
Zuwa tayi ta zauna bisa kujera tace”anty ina kwana”,
Imaan tace”lafiya lau nafeesat ya kike,meyasa zaki ce min anty bayan ni da ke babu Wanda yafi wani…sai dai kice min k’awarki,
Dariya nafeesat tayi tace”a a matar yaya guda ai Dole ince miki anty????ina yaya yake ne ko bacci yakeyi?,
Imaan tace”nima ban sani ba”,hmm bari dai in tashi in koma kar ya fito ya ganni a nan,
Imaan tace”to meye dan ya ganki,daga zuwanki sai kice tafiya zakiyi,please ki zauna muyi hira anjima sai mu taxi tare nima in gaida mama,
Muna hirar mu yarima ya fito daga cikin d’aki yana ganin nafeesat ya d’aure fuska,tace”yaya ina kwana”,ya amsa mata da lafiya” kawai,ya kalli imaan amma bai mata magana ba saboda kar ta disga shi a gaban nafeesat????
Kai tsaye dinning table ya nufa ya zauna yayi break fast din shi,sannan ya shige d’akin shi dan ya shirya yaje fada wajen sarki daga nan ya d’an fita yaje asibiti amsar magani dan kanshi yake so ya matsa mishi da ciwo…
Yarima yana da ciwon kai mai tsanani Wanda ya samo asali ne tun yana k’arami ya buga kan wani waje,anyi magani har an gaji amma sai dai sauk’i daga wajen ubangiji,idan kan ya tashi sai ka tausaya mishi saboda yana shan wahala sosai…
Fitowa yayi cikin shirin shi na fita yayi matuk’ar yin kyau,manyan kaya ne a jikin shi,kuma sun karb’eshi sosai,hmm imaan ma ta yaba dan kallon shi takeyi bata sani ba har yazo kusan ta ya zauna,
K’amshin turaren shi ne ya maido ta daga abinda takeyi,
Yace”yadai wannan kallo haka ko kina tsoron in fita a kwace miki ni????
Kunya ta kamata tace”nifa ba kai nake kallo ba”yace”naji to wa kike kallo ko kuma tunanin me kikeyi”?
Tace”ba komai ba,yace”ok ni zan fita daga fada zan wuce asibiti,
Tace”nima zan bika inje b’angaren su mama,yace”ke,kinaso muje ta tuhume mû ko,bayan kuma duk laifin ki ne,
Ita dai bata fahimci me yake nufi ba,tace”tuhuma kuma akan me,laifin me nayi ni kuma”?
Yace”au baki sani ba ma Kenan,to su suna jiran ki fita kunya su sha biki ne,
Fita kunya,tame kuma?
Yarima yace”to ba kin hana in girma ba jiya da dare,wai ke mai tsoro…
Sai a nan ne imaan ta gane nufin shi,ta rufe idon ta,yarima yace”ah to ai gaskiya na fada,gwara ki daina tsoro…hhhhh
Da yamma su jamila suka zo a lokacin ina bacci ban san bama anyi sallar la’asar zuwan su ne ya tasheni,
Bayan nayi sallah,muna zaune muna hira jamila tana tsokana ta wai ramuwar bacci ne nakeyi,
Duka nakai mata nace”jamila banson iskanci fa”tace”hhhh bakison a fad’i gaskiya dai”????
Nace”kedai kika sani”bari in shirya muje b’angaren su mama,sukace”OK to ba matsala amma kiyi Sauri munason mû koma gida da wuri,
Shiga irin ta gidan sarauta????imaan tayi tasha lullub’i,suka fice b’angaren su maman su yarima,
Da sallamar su suka shiga,aka amsa musu,mama tana zaune kusanta da masu yi mata hidima…..
please manej wallahi idona ke ciwo
yar mutan kazay ce????
*Anty Maimounath*????
+22969164943
[10/9, 01:45] Prince Abdul 3 Star: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:✍????
*Anty Maimounath*????
PERFECT WRITERS FORUM
????P.W.F????
cette page est pour vous les nigériens,merci pour vos soutient, je vous aimes tous,on es ensemble
niger c mon pays,niger c mon continent????????????????????????
Dédicace à:
Maman latifah(Zulaihat)
Ma chérie (Husnah)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page1⃣1⃣
A waya mama ta kira yarima,jim kad’an sai gashi nan ya shigo tare da yin sallama,ba shigar shi ta safe bace ya sauya kaya zuwa k’anana blue jeans ne da farar shirt mai ratsin ja,kayan sun matuk’ar yi mishi kyau,Dole ne duk inda ya shiga mata suyi ribibin shi,dan dai basu ga fuska bane saboda in ya fita waje ba ya yin dariya saï ya dawo gida(yes haka akeson jinin sarauta)
Zuwa yayi kusa da mama ya zauna kamar yanda nima nayi,kallon masu mata hidima tayi tace”ku bamu waje zanyi magana da ‘ya’yana,tashi sukayi d’aya bayan d’aya suka fita suna kirari,mama ta kalli yarima tace”shureim”ya amsa da na’am mama,dan yasan idan ta kirashi da wannan sunan to ba wasa,tace”maganar da zan fada maka itace ka rik’e Imaan amana wallahi in tayi kuka da kai ni kuma zan d’auki mataki da kaina ba tare da sarki yaji ba,kuma kasan in ka b’ata mata yaji to wallahi ran ka zai yi mummunan b’aci so nake ku zauna lafiya,kaga yarinya ce batasan komai ba in tayi ba daidai ba kayi mata magana cikin tattausan harshe ba fada ba dan nasan halinka da zuciyar tsiya….
Na dawo kanki ‘yata,ku zauna lafiya kinji kuyi hak’uri da juna haka aure ya gada,duk abinda ya shige miki duhu ko shureim ba ya gida to ki turo a fada min ko kizo da kanki,gobe insha Allah za’a kawo muku Wanda zasu rink’a muku hidima,Allah ya muku albarka,ameen!!…