KHADIJATUL IMAAN COMPLETE HAUSA NOVEL
Ido imaan ta zaro a ranta tace”jakadiya kuma warhaka me tazo yi,????kar ace dai yarima ne yaje ya fad’a a gidan su, amma kuwa ya gama da ni in ta tabbata haka,can kuma tace jakadiya lafiya meye?tace”uward’akina hajiya ce ta aiko ni,
Tace”shigo to”da ta shigo wasu abubuwa na gani a hannunta,tazo kusa da gadon tace”ina kwana gimbiya ta yarima daga yau kin zama ‘yar lele a gidan nan,itadai ta amsa da lafiya lau amma sauran maganganun bata fahimci komai ba,
Jakadiya ce tace”gimbiya ki tashi ki shirya zamuje b’angaren uward’akina…nan naji haushi wato yarima zuwa yayi ko kunya babu ya fad’a musu ko,jakadiyace ta fito daga toilet tace”an gama had’a komai gimbiya,na tashi da dubara dan kar ta gane irin tafiyar da nakeyi,hmm ni kuwa nace ai an gama sani tuni????
Kafin na fito an gyara min d’akin saï da nayi mamakin gyaran da akayi cikin d’an k’ank’anin lokaci,juyawar da zatayi saï taga jakadiya dauke da zanen gadon da suka kwana bisan shi jiya,saï da ta tsorata????me ya kawoshi hannun jakadiya?
Tace”jakadiya bani wannan zanen gadon zan wanke shi a toilet, saï jakadiya tace”a a barshi ai dashi zan tafi can,????can ina kuma tace da ita,ta amsa mata da cewa,ai wannan b’angaren su mai martaba za’a kaishi kedai ki shirya akwai masu miki hidima mata su uku ne yanxu zasu iso,ni na gama nawa aikin amma kuwa naji dadin al’amarin nan a gaishe da d’ana,yayi sa’ar mata tagari na barki lafiya,tana gama fadar haka ta fice…
Imaan kuwa mutuwar tsaye tayi,tana cewa na shiga uku meye haka kuma,hmm duk laifin yarima ne ai meye na zuwa ya fad’a a gidan su,wannan kayan kunyar…
Shiri akayi min Wanda ko d’à nake amarya ba’a min,cikin gidan su yarima ya ka je dani,da muka shiga ma naga ana ta shige da fice hidima akeyi babu kama hannun yaro,kamar yau ne ake auren namu….
D’akin nafeesat aka shigar dani sakamakon zaxxabi da ya saukar min lokaci guda,
Ina nan kwance saï wayata tayi k’ara ina dubawa sai naga yarima ne, k’in d’auka nayi saboda wani haushin shi da nakeji,text yayi min yana rok’ona da in dau wayar shi…
Sake kira yayi na d’auka amma banyi magana ba saboda ina jin kunyar shi da kuma haushin shi,hello yace dani,banyi magana ba,ya sake cewa”please baby yi min magana mana ko zanji dadi,am so sorry kiyi hak’uri mana”
A hankali tace”ina jinka ai”yace”baby lafiya naji muryar ki kamar bakijin dadi”?
Tace”zaxxabi nakeyi”subhanallahi srry kina ina yanxu gani nan zuwa,ai tanajin haka tace”a a bâ sai kazo ba nasha magani ai kuma ina b’angaren su mama,su imaan anji jiki????
Murmushi yayi dan ya gane tsoron shi takeyi,hhh
Yace”ok nan din ma ina iya zuwa inga matata ai ba laifi bane,zumburo baki tayi kamar tana gabanshi tace”nidai a a kayi zamanka na warke ma????
Bai k’arayin wata magana ya kashe wayar….ina nan kwance naji ana gaishe shi yana amsa musu ya shigo d’akin yazo har inda nake ni zai hayo gadon na matsa can k’arshen gadon na fara matse hawayen da suka zo min,cikin kuka nace”nidai ka fita banso wallahi zan had’aka da mama,shi dariya ma ta bashi,komai rashin kunyar shi ya zai mata wani Abu a b’angaren su mama,kuma a d’akin kanwar shi salon ta rainashi,hmm yarima Kenan….yace”to yanxu a nan meye abin kuka”,me na miki uhm,
Ita dai batayi magana ba,hannu tasa ta goge hawayen da suka zo mata,yace”ya jikin,ya kikeji yanxu,banda zaxxabin akwai inda yake miki ciwo”?Saurin girgiza kanta tayi tace”a a babu”yace”good haka nakeson ji….to d’an zo mana inji jikin naki yana fada yana k’ok’arin janyo ta,
K’ara ta saki Wanda sai da su mama sukaji,da kanta ta taso ta shigo d’akin, nan ta same mu, kunya ce ta kamani,kallon yarima tayi tace”lafiya me kayi mata”?yarima ya sosa k’eya yace”ban mata komai ba wallahi mama”tace”baka mata komai ba take ihu,shureim ka kiyayeni kaji ko,wai ma ya akayi ka shigo nan ko kunya bakaji duk mutanen da suke cikin gidan nan da falon nan ka iya tsallake su ka shigo ko saboda kai gaka maras kunya,mama kiyi h….bai k’arasa ba tace mishi zo ka fice min daga nan,
Sumi,sumi ya fice….ni kuma kaina k’asa kamar in nutse dan kunya tace min”sannu ‘yata ya jikin baki?,da sauk’i nace da ita,tace”to yayi kyau Allah yayi miki albarka”nace”ameen”,
Da yamma bayan sallar la’asar,sai ga jamila ita da wasu ‘yan makarantar mu Wanda basu samu damar zuwa bikina ba,
Nafeesat ce tayi musu jagora har d’aki…da shigowar su jamila ta kama yi min dariya,fuska nayi nace mata”ke kuma lafiya daga shigowarki sai dariya kamar wata mak’aryaciya,sai da tayi mai isarta sannan suka nemi waje suka zauna a bakin gadon muka gaisa dasu,jamila ta kalleni tace”k’awata ya jikinki”ban sani ba da iskanci na fada tare da murgud’a mata baki????
Dariya jamila tayi tace”bani na kashe zomon ba,in kin isa kiyi ma yarima ki ga matakin da zai dauka”????????
Dukan su suka kwashe da dariya,nace”wai daman abinda ya kawoku Kenan gulma ko,dariya suka sakeyi sukace”a a amaryar prince shureim zumunci dai mukazo,hmm….can kuma yarima ne yake bawa naseer labarin korar da mama tayi mishi,dariya naseer yayi sosai sannan yace”friend wallahi kai d’an duniya ne sai da ka kashe arna jiya ashe????????ko tausayin yarinyar nan bakaji ba,murmushi yarima yayi yace”wallahi friend ni kaina ba haka naso ba,kawai idan nazo kusa da yarinyar nan ne nakejin wani irin feeling,nayi iya k’ok’arina dan hana faruwar hakan amma na kasa,gashi har ta farajin tsoro na,dariya naseer yayi yace”kasan wani abu?,ka barta kwana a hakan zata daina tsoron ka,amma fa idan kace kullum sai ka kusance ta to wallahi bazata daina jin tsoron ka ba,y’a k’arasa maganar sa cike da zolaya,yarima ya kai mishi duka yace”friend kai fa d’an iska ne wallahi…..
Da misalin k’arfe 9:00pm a lokacin kowa ya watse,sai akace in fito a rakani gidana,haba wa ai a nan nace bansan zancen ba,babu inda zani har da kukana,mama ce ta shiga rarrashi na tace”kiyi hak’uri ‘yata haka aure ya gada,ai muna tare in kinji kad’aici ga nafeesat sai taje kuyi hirar ku,hmm ita mama bata ganewa ni ba wannan nake ma ba,tace”bari to in kira yarima sai ku tafi,daman inason magana dashi…..hmm
kiyi hak’uri da wannan idona,need ur prayers
*yar mutan kazay ce*????
*ANTY MAIMOUNATH*????
+22969164943
[09/10, 01:19] Yar Niger Frd Husaini: ????????????????????????
KHADIJATUL
IMAAN
????????????????????????
Story & written by:✍????
*Anty Maimounath*????
PERFECT WRITERS FORUM
????P.W.F????
cette page est pour vous les nigériens,merci pour vos soutient, je vous aimes tous,on es ensemble
niger c mon pays,niger c mon continent????????????????????????
Dédicace à:
Maman latifah(Zulaihat)
Ma chérie (Husnah)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page1⃣1⃣
A waya mama ta kira yarima,jim kad’an sai gashi nan ya shigo tare da yin sallama,ba shigar shi ta safe bace ya sauya kaya zuwa k’anana blue jeans ne da farar shirt mai ratsin ja,kayan sun matuk’ar yi mishi kyau,Dole ne duk inda ya shiga mata suyi ribibin shi,dan dai basu ga fuska bane saboda in ya fita waje ba ya yin dariya saï ya dawo gida(yes haka akeson jinin sarauta)
Zuwa yayi kusa da mama ya zauna kamar yanda nima nayi,kallon masu mata hidima tayi tace”ku bamu waje zanyi magana da ‘ya’yana,tashi sukayi d’aya bayan d’aya suka fita suna kirari,mama ta kalli yarima tace”shureim”ya amsa da na’am mama,dan yasan idan ta kirashi da wannan sunan to ba wasa,tace”maganar da zan fada maka itace ka rik’e Imaan amana wallahi in tayi kuka da kai ni kuma zan d’auki mataki da kaina ba tare da sarki yaji ba,kuma kasan in ka b’ata mata yaji to wallahi ran ka zai yi mummunan b’aci so nake ku zauna lafiya,kaga yarinya ce batasan komai ba in tayi ba daidai ba kayi mata magana cikin tattausan harshe ba fada ba dan nasan halinka da zuciyar tsiya….