NOVELSUncategorized

NAJEEB 43

Kaman granny tasan abunda ibtisam ke tunani, tace ibtisam zaki ga kaman bana goyan bayanki, ba haka bane, yanzu duniya ta canza, komai ya canza, idan mace batai hakuri gidan mijinta ba inta fita bata san wanda zata aura ba, kinga gwara tayi hakuri ta zauna da Wanda tasan halinsa, saita dinga kiyaye wa, amma yanzu in mace
ta nemi saki , inhar mijinta ya saketa bata san wa zata fad’a mawa ba, sai yasa ake cewa hakuri shine gaba da komai, kuma Mai hakuri yana tare da Allah, wlh ibtisam ban taba ganin laifinki ba gaba d’aya na najeeb ne, domin ke aka cuta amma gashi ina rokanki akan kiyi hakuri wata rana insha Allah za kiyi dariya

2gnovel

4medicals

Smidris

Ibtisam nidai burina in ganku tare har abada, shine Fata na, indai kukai haka zan mutu cikin salama……

Da sauri ibtisam ta rungume Granny tana kuka tare da fad’in insha Allah bazaki mutu ba Granny

Granny tayi murmushi tare da fad’in ai mutuwa ta zama dole ibtisam, lokaci kawai ake jira, amma dole ce ko Ana so ko ba’a so

Ibisam tace toh nidai Granny abar maganan mutuwar nan dan Wlh ba son jinta nake ba, gaba d’aya

Granny tace Indai kam baki Sonta saiki koma ma mijinki, yanda zaki sani farin ciki

Ibtisam tace Granny ni Kinga Wlh yunwa ma nake ji, Sosai mai kuka dafa ne Inci

Granny tace ja’ira wato canza firan zakiyi koh??  Yayi miki kyau ai

Ibtisam tashi tayi ta nufi kitchen inda ta dibo abinci domin taci, tana cikin ci sai ga Ummi ta shigo cikin d’akin tana fad’in ah Ashe y’an karanta an dawo

Ibtisam cikin fara’a da murna take fad’in eh Ummi tun dazu na dawo bakya nan

Ummi tace Mun fita da Maman fati ne, ya karatun an Gama jarabawan kenan?

Pls Kuna mana click na ads


Ibtisam tace eh mun gama zamu sha hutu Mai tsawo harna wata d’aya da sati Biyu

Ummi tace Kai Aiko zaku dad’e a gida Sosai Allah ya taimaka bari inje in watsa ruwa duk na kwaso rana, Ummi ciki tayi tabar ibtisam da Granny

*AMERICA*

najeeb ne zaune yana karanta al’qur’ani domin gaba d’aya yanzu ya iya had’a ba’ki, abun har mamaki yaba malamin yanda yayi saurin iyawa, gashi najeeb baya dad’ewa ya gane Abu, wanda yawanci tun a k’aramin shekaru mutum yake saurin haddace Abu haka, amma sai gashi Abun mamaki shi najeeb da girmansa yana haddace Abu da wuri

Malamin ne yazo inda najeeb yake yana fad’in gaskiya najeeb ka gode Allah, wlh komai naka Abun sha’awa babu wuya ka haddace Abu, nan da nan wlh kana da kwakwalwa sosai

Najeeb saida yakai karshen Aya sannan ya kalli malamin Bayan ya ajiye al’qur’ani yace malam ba komai bane yasa kaga Ina saurin haddacewa ba sai Dan Ina son in koya wanda Allah yaga zuciya ta, duk abunda nake da Wlh Ina aikatawa ne ba tare da sani na ba, sannan yanzu dana gane nake son in koya in iya dole in dage, aikina gaba d’aya na dau hutu dan in nemi ilimin addini, inta Kama ma Wlh ajiye aikin zanyi, duk da nayi yunkurin yin hakan amma suka d’age akan bazan ajiye ba, inje inyi hutu, shine nace na d’auki hutun 5mnt

Malamin yace hakan ma yayi tunda gashi yanzu ko wata biyu bamu yiba amma harka iya abubuwa da dama, ko a haka ka tsaya aika gode Allah, domin wani wanda ya taso tun yana yaro yayi karatun ban tunanin zaiyi aiki dashi akan Kai yanda kake aiki dashi, yanzu nima tafiya ta Kama ni dole zan tafi saudiya, domin mahaifina baida lafiya, Kaga bazan zauna ba har inyi wata ukun da Nayi alkawari ko a haka na Barka Alhmdlh Nasan ka koya abubuwa da yawa

Amma idan naje naga yanayin jikin nasa inda hali zan dawo…..

Najeeb yace a’a karka damu, nida kaina zan biyo ka saudiya, zanje Nigeria insha Allah daga nan Zanzo harda iyayena domin su ganka, ku gaisa

Malamin yace haka yayi, tare dayi MA NAJEEB addu’an samun nasara a rayuwa

Najeeb Bayan ya koma gidansa gaba d’aya baya son zama shi d’aya sai yaji gidan yayi masa girma, kwanciya yayi akan kujeran falon inda ya lumshe ido, lallai sai yanzu yasan yana rayuwa, a da yana rayuwa ne amma kaman matacce, domin bai San yanda zai bauta ma Allah ba, gaba d’aya wannan canjin daya samu ya sameshi ne ta sanadin rayuwarshi da ibtisam ta shigo

Ya fara tunanin yasan mai yasa shan giya ya zama haramun da zina, lokacin da tace mishi duk manyan laifin da Allah ya hana kana aikatawa, tun daga ranan ya fara tunanin sanin Mai yasa ya zama laifi har yakai shi ga kiran malam, wanda gashi yanzu gaba d’aya rayuwarshi ta canza, sai dai abu d’aya da yake fatan shima ya canza

Lokaci d’aya ya tashi ya nufi bedroom d’inshi inda ya fad’a toilet yayi wanka ya fito daga shi sai boxer da singlet Kai tsaye kitchen ya nufa inda ya Tarar damai mishi aiki yace ta Kawo mai coffee, yana fad’in haka ya juya falon ya zauna yana danna wayarshi dake hannunsa

Bayan Mai aikin ta kawo mai coffee ta ajiye Mai akan center table har zata wuce najeeb yace ta tsaya tare da fad’in gobe zani Nigeria so zaki iya d’aukan hutu, but amma ki dinga zuwa kina duba gidan coz ban son in dawo inga datti ko k’ura

Ta amsa da OK sir

Najeeb d’aukan coffee din yayi inda ya fara sha…..

Washe gari kaman yanda yace hakan ko ta faru domin kuwa jirgin k’arfe 10 yabi inda ya tafi Nigeria Kai tsaye a abuja ya sauka inda aka turo mai driver yazo ya d’auko shi,.

Bayan sun k’arasa gida, Zarah da saurinta ta nufeshi tana fad’in Wlcm bros

Murmushi ya sakar mata tare da kallonta yace ya gida da skul?  Yana ganki a gida??

Tace lafiya bros munyi hutu ne

Yace OK

Nan suka shiga ciki abunda najeeb bai taba yiba yau yayi gaida iyayenshi cikin girmamawa, gaba d’aya daga Dad har Mum sunyi mamaki tare da kallon juna

Najeeb ya lura da hakan sai yayi murmushi tare da fad’in kai am so tired I need to rest hope d’aki na a gyare yake??

Mum tayi murmushi tare da fad’in eh my only son, a gyare yake, AI ban barin dakinka da datti, domin Nasan yaron nawa baya son kazanta, amma before ka huta Aida kaci abinci koh

Yace Mum bari in huta na gaji Sosai wlh, nayi missing food d’inki amma tunda kika ga na kasa ci, toh na gaji ne

Tace OK a huta dakyau

Yayi murmushi tare da shiga d’akin nashi wanda yana shiga ya fad’a gado ya kwanta sai bacci

Mum da Dad sukam zama sukayi inda Dad yake fad’in kinga yanda yake gaidamu cikin girmamawa, gaba d’aya harta magananshi ya canza kaman bashi ba

Mum tace Wlh kuwa abun ya bani mamaki, bari dai ya tashi muji ya akayi

Ibtisam ce zaune tana ta wanke underwear d’inta, a wajan fanfo din dake waje, a tsakar gidan

Granny ta fito tana fad’in in banda kazanta mutum saiya tara su wando da skirt da yawa Kafin ya wanke, ai wannan kazanta ne

Ibtisam tace kazanta?? Lallai Granny Wlh kina shiga sabga ta da yawa, d’ago wani pant d’inta tayi tare da nuna mata da tace ina kika ga alaman kazanta a nan??  Kuma pant d’in ga sunan gudu biyar ne duka amma kina wani kiramun kazanta, salan wani yaji kisa a d’auka haka nake

Granny tace toh aji mana, AI gaskiya na fad’a Inba Kazami ba, taya mutum zai dinga tara pant da yawa haka babu wanki, ko ni da nake tsohuwa bana irin haka saike yarinya karama saboda lalaci.

Ibtisam tashi tayi tana d’iban kayan domin ta gama zata toilet ta shanya tace Kedai kika sani, nidai banda lokacin wannan surutun dake inada abunyi da yawa

Granny tace ai kyace haka mana t…..  Wani irin K’ara ta saki tare da yin k’asa, da sauri ibtisam ta saki roban dake hannunta ta nufi Granny tana fad’in Granny lafiya kuwa? Maiya sameki tana tambayar Granny tana kuka

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button