HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

“`Dukkan Yabo d kirari d jinjina sun tabata ga ubangiji Mai kowa Mai komai maiyin yadda yaso d y bani dama d iko na fara rubuntun wanan littafi , Abin d zanyi daidai Allah kabani iko Abin d zanyi kiskure Allah k haneni d rubutawa , in Ang a ba daidai ba Amin afuwa ajizancin Dan Adam ne“`

Indo ! Indo !! Indo!!!
Naam Aunty !
Bakiji ni bane tun dazu inata kiranki kinmin shiru?
Aa wlh Aunty banjiki bane d zan fito kiyi hakuri Dan Allah …..

Toh naji , ki gama gyara ko Ina na cikin gdn Nan in su Noor sun dawo dg makaranta ki musu wanka su danji iska a jikin su sanan ki shiryasu zuwa islamiya ki tabbata kin dafa musu zabin ransu kinji ko?

Maybe bazan dawo d wuri ba Dan zamu tsaya group discussion d fanc Dina Kar asami akasi kinji Koh?

Toh! Aunty insha Allah , su Noor sunce dambun shinkafa sukeso d hadin salad Wanda yaji zogale ,Kuma b zogalen ….. Kafin t karasa NAWAL ta katseta eh na sani zan Aki Dan bala driver yaje gdn Hindu tasa adibo min a bishiya a garden din ta…..

“So” ze kawo Miki ki gyara ki tabata kin wanke d gishiri ki dafa musu ki samusu komai “enough”aciki kinji Koh?

Toh ! Aunty insha Allah,sekin dawo Adawo lpy…….

Allah yasa na tafi ……

 

Fitar NAWAL keda wuya , Indo t dukafa Aiki gyara can kalkale Nan Nan d Nan komai y zama “very neat “na gdn Dan Akwai Aiki ….

NAWAL Ana Hall anata daukan lecture , hannun su rike d “handout” “Attention” din su gaba daya Yana ga lectura …….

Indo ta gama komai na danbu b Abin d ya sura ta jere a dining t hada komai na bukata har na me fada ajin gdn , wato megidan Dan zedawo lunch ….

Shi ya fara shigowa cikin kamala d kwarjini yayi sallama ,lndo t amsa tamai sannu d zuwa ,ya tmby ta “lunch is ready” ta daga Kai Alamar eh ….

“Direct Dining ” ya nufa,y duba yaga Abin d Aka girka y jijiga Kai kawai yasan favorite din su Noor ne Dan haka ya ziba kafin y fara Kai Loma sai naga ya Dan tsaya Alamar” he thinking something about her wify or her child ” l d’nt no wooo …….Dan ba kowani time neke kutse cikin mind din mutum ba “lol…..

 

Sai daga baya yayi wani malalacin murmushi sanan y yi bisimillah! Y fara cin Abinci …..

Yakai Loma na 4 kenan su Noor d Haneef suka shigo d gudu sakamakon 2eyes d sukayi d dad din su ……

D gudu Noor ta tafi gareshi Haneef ma haka ,shiko dama y gama bude hanayen sa yana sauraran Jin dumin yaran a fafadan kirjin shi ,yanajin su y lumshe ido Yana sumbatar su ,Suma suna mayar Mai ….

Yace hasken idanuna kun dawo? Sukace yes Dad we came back ‘ Nima haka yarana kuje kuyi wanka kuzo muyi lunch kun ji?

Haneef ne y tabe baki yace ware is mom dad? Noor ko cewa tayi Ni gaskia sai naci mutumin kafin nayi wanka l’m hungry dad wlh Tana mele baki irin n ‘yan Madara d bonvita lol…..

Indo Ce ta fito Tana musu sanun su d dawowa , tace suzo amusu wanka suyi sallah kafin suci Abinci …..

Shiko safwan dad din su Noor ,

Haneef yake b amsa d cewa mom Bata dawo ba Amman munyi “telephone d ita right now ” Tana hanya insha Allah kaji….

Kuje kuyi wanka kuyi sallah , Noor d Haneef atare sukace dad Dan Allah abari muci Abinci kafin wlh mungaji g yunwa ,Nan SAFWAN yace ma lndo to ki bari suyi lunch sai amusu wankan suyi sallah,Bata d zabi tace to dadyn su Noor ,Nan t kwashe lunchbox dinsu d school bag dinsu zuwa room din su domin ajiye musu …

Sunacin Abinci cikin kwanciyan hankali d Jin Dadi d farin ciki ,har suka kamala aka musu wanka sukayi Alwala sukayi sallah ..

SAFWAN kuwa mik’ewa yayi zuwa bed room dinshi domin watsa ruwa shima kafin y fita Dan Akwai inda zashi …..

Bayan sun idar da sallah ne Indo ta feshesu d bodyspray na “ALHARAMAIN” ta sa musu uniform dinsu ta Basu islamiyabag dinsu ta kamo hannun su zata sadasu d Dan bala driver domin kaisu islamiya …..

SAFWAN ne y fito cikin shiga Mai kyau yanata kamshi shima , yace u guys ko salama ma baza’amin ba nayi Adu’ar Adawo lpy Koh?

D gudu Noor taje gare shi tace sorry dad mun sha’afane bamaso muyi latai kasan y sayadi in akayi lati maimakon yayi dukan lati saidai y Kori mutane su koma gd sede su hakura d karatun ranar shiyisa bamason mu makara ……

Dad yace hakan shine daidai tsarin islamiyar aini yamin sai ku Kara hima d bin doka Dan azauna lpy …..Indo
Na tsaye Tana sauraran uba d ‘ya’yan sa ,sai SAFWAN ne yace Mata t bari zai saukesu a makaran tar kafin y wuce inda zai je ,Dan haka t koma ciki Tana musu Adawo lpy ……

 

NAWAL ba ita ta shigo gdn Ba Sai After 2 ,ita kanta bataji dadin rashin ganin iyalan nata ba ,

bayan Indo t gama Mata sannu d zuwa tayi room din ta Dan taking shower……….

 

_FATEEMAH ABUBkAR_
[12/28, 6:58 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na biyu_

Bayan NAWAL ta fito dg watsa ruwa tayi sallah ,sanan ta afkama Abinci d ci …

Kiran Indo tayi tatambaye ta dadyn su Noor y dawo ne, Indo t sheda Mata y dawo yaci abinci y fita, tace ok ,su Noor sunci Abinci sosai ko ,tace eh sunci tare ma suka fita d dadyn su ze saukesu a makarantar ….

Tace ok hakan ,yayi jeki karasa aikin ki (Allah sarki su injin sarkin Aiki)
Nan Indo t koma kitchen Dan karasa wanke wanken ta ..

*WACE CE NAWAL*?

*NAWAL* Yarinyace ga Shareef Ahmad ‘yace Kuma ga hasiyatu tanada kanne 3 maza biyu mace d’aya Autar su …

Shareef ba wani shahararen Mai kudi bane Amman yanada Arziki daidai nasa NAWAL itace ‘yarsa ta fari , kafin a haifeta saida suka kwashe shekra 3 kafin Allah y Basu cikin ta hakama Akwai taxarar shekaru 5 tsakanin ta d Auwal kafin Aka haifi Ahmad sai husnah Auta (Asma’u) …..

Shareef Ahmad baza’ace Mai hamshakin Mai kudi ba Aman yanada wadata d rufin Asiri ko Ace karamin Mai Arziki ne ya Malaki gdn kanshi Mai kyau ginin zamani sanan yanada motar hawan shi Kuma yanada jarin Dan Kasuwa ne Kuma yayi karatun Boko d yayi aikin gomnati daga baya y fada kasuwanci nan yake duk wata hidimar gd d y’an uwa …..

Shareef Yana wadata iyalin sa ,musamman NAWAL taga gata dake bashi d ‘yayan d yawa kafin a haifi su Auwal y sangarta ta y Mata yadda takeso har zabin ransa ma duk hakan Yana faruwa ne badon San ran Mama (hasiyatu) ba Dan takan yawaita musu mgn kan y’a mace ce gdn wani zata kodan kalubalen rayuwa ma Bai dace y sangarta ta haka ba , Abbah (Shareef Ahmad) Yana cewa abarshi y nuna Mata k’auna in Basu nuna kulawa akanta ba a kan ‘ya’yan makota zasu nuna ,ita suka Haifa Kuma ita kadaice a gaban su har sai d ta shekara 5 sanan aka Mata kani cikin shekara t 6 Dan haka still gata d sangarta Tana Nan …

Ahmad ma y taso y joining din su NAWAL fagen sangarta ,haka duk y sangarta yaran Amman yara matan sunfi sangartuwa ,itako mama fadan d yafi karfinta wasa ta Mai dashi aka zauna lpy ,Amman haka besa in sukayi ba daidai ba ta tsawatar musu Dan ko Mai Aikin gdn su dake Abbah y samo ma mama Mai tayata Aiki wai yara sunmata yawa t dinga tayata ba yadda mama batayi ba Dan ganin y rabu d Mai Aiki Amman Sam yace in Bata bukatar taimako yaransa na bukata Dan haka dole tayi Aiki agdn haka ta hakura ,Inna dije Tasha fama d su NAWAL Dan dai biyan ta akeyi Kuma Bata d karfi d tuni tabar aiki a gdn …,..

NAWAL tun Akan Abban ta d maman ta taci burin ko Aure tayi sai d taimakon Mai Aiki zata iya sarafa kanta d yaranta Dan haka Koda ta girma cikin ikon Allah suka hadu d SAFWAN a shop wright ,cikin lokaci kankani kuwa saoyaya Mai karfi ta fizgi zukatan junan su ,cikin salo d iya sarafa soyaya suka Aminta d junan su kan cewa daya baze iya rayuwa ba sai d daya ,zuciyoyin su dai suka zama Abu guda ……

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button