HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

D su aunty zainab zasu tafi , Aishatu ta cikasu d tsaraba harda tasu mama d Inna akaba aunty zainab takai musu ,itako nawara harda tsaraban dambu ta tafi dashi ta dumama ….

Da dare tayi ,sunata Hira su Aishatu d amaren d wasu daga kawayen su ‘yan uwa d abokan Arzuka , ussaina nata surutu , sufayya tace ke ussy ko kunya Babu ?

Sanan taji kunya ,tace laah aunty nazata kunyi bacci….

Aishatu tace hmmm ussaina manyan gari ,to idon mu biyu y abinki son ranki ,lokacin kine ….

Har sai d Ammy t shigo ,tace su sufayya d Aishatu su kwanta fa su huta karsu biyema su twins ,sune jikinsu yake bukatar hutawa …

Ussaina akasa dariya ,yace Ammy kinaji d surukan Nan naki ,Ammy tace Mara kunyar yarinya Naga falin ki karuwa yayi kwana biyu ,inaji dasu din ba yarana bane ?

Hassana tace halak malak kuwa our Ammy !

Ammy tace ita ai Bata sani ba ,sai magana ,kuyi kwanciyar ku ,ku tabata kun k’oshi kafin kwanciya ,ga fira da nono can yaji Madara d aka dama a fridge ko zakusha kukadai nama tayi ,Aiko ussaina tace Aiko Ammy zansha ….

D sauri Ammy tace baringa hannun ki a wajen sai ranki y bacci !

Hassana tace yauwa,Ammy mu!

Ussaina tace ,to ai na hakura Ammy tunda Abin na surukai ne ,tun yau kin daina ji damu …

Wata acikin kawaye ,tace ehdin ai gidan wasu surukan zaku ,Kuma ALLAH y baku kamar Ammy Mai irin halinta d kyautatawa , ussaina d sauri har suna hada Baki d su Aishatu wajen Amsa rokon Ameen ,….

Ammy tace Mara kunya , ALLAH y shiryeki ….

, Hassana ,tace Amin …

Sufayya ce taje t d’ebo musu furar Mai sanyi sosai Dan har kankara t jefa musu a ciki ,duk d Haka sai d ussaina t sa Albarka ….

 

Su Aishatu ,ba a kwanta b sai d aka gama waya d safwan ,tanata sakar Mai d jiki d kalaman d Bata Mai a gaban sa ,shima sai narke Mata yake Yana cewa dama tana kusa dashi a yanzu ,Haka badan yaso b yamata sallama yace t kwanta t huta yanata Kara Mata gargadi karfa tayi Aiki t hutarma kanta ,be yadda d aikin wahala ba ,toh kawai take cewa ,har suka yi sallama …

Sufayya nata tsokanar t ,har seda taji kunya, sai suffaya CE tace yi abinki ,kiyi Abin d yafi hakama it ur time , ja linzamin makaman soyayyar ki yadda kikeso kanwata , ALLAH dai y bamu dawamamen zaman lpy d mazajen mu , Aishatu tace Amin aunty …..

Washe gari ,za’ayi party ,tun safe ake kokarin Kamala abubuwan d za’aci a raba a wajen party dake meenat restaurant suka ba order Dan Haka basu d case ….

Yamma nayi ,angwaye d ‘yan uwa suka kawo motoci Dan Kai amaren d taron jama’a haka kuwa ,sufayya d Aishatu Suma kowace mijinta ne y dauketa yasan darajar kodan Abun d ke tare d ita, Aishatu ma haka safwan y kwashe su d su nawara d aunty zainab d Noor din ta sai center d za’ayi party ,…..

Waje ya karbi gyara sai uban kida d yaketa tashi g kayan drinks d su snacks d sukema oyoyo a kowane kujeru d tebir …..

Koda safwan y ajiyesu ,Bayan sun fita y dawo d Aishatu y dinga cemata t kula d kanta y barmata Amana ,ba rawa b aikin wahala banyarda kiba kowace katuwa Abin ci ko abin Sha ba , ….

Ta Fara dariya ,tace katuwa Kuma ko my Noor CE? Y harareta a Wasa yace Noor ai takice Abincin t n wajenki ,kinfini sanin yadda Zaki ciyar d ita d abinda tafi so Dan Haka kunfi kusa ,inkin so karki Bari taci komai har ku dawo,tasa dariya ashe b Wanda zesha ko ruwa matuk’ar my Noor bazata karya kashin kaza t kurbi drink zabin ranta ba ,yasa dariya Yana yaba kaunar dake tsakanin su …

Noor ,safwan y dafa yace cwt Noor ,ki kulamin idan aunty tayi rawa kinji? Noor tace Kai Dady ranar farin ciki ne fa ,ai ko su Aunty twins suna rawa ! Aishatu t gyada Kai tace Gaya Masa dai Noor …

Y harari Aishatu ,y rungumo Noor zuwa jikin shi ,yace banace kartayi murna bane ,Kinga Bata d lpy ,ai Tana amai d zaxabi kulin ko? Noor tace eh Dady wlh Ina tausayinta har kuka nake Mata ,yace to my Noor danhaka Nima nace kartayi rawa ki kulanmin intayi ki sanar min zan biyaki d ice cream d Nutella Mai dadinan ,Noor tace yeee Dady ,zan fadama indai tayi ,yace yes my Noor ,sai nadawo d’aukan ku ko?

Sukayi sallama yanata bin Aishatu d mayen kalo na tsantsan kulawa ,har y fita d motar ….

Bayan sun shiga hall din ,t nufi wajen su nawara ,nawara t Fara Mata mita ,Laila majnun kungama ? Har sai d taji kunya ganin aunty zainab a wajen , Aishatu t harari nawara …

Aunty zainab ,tace karki matsa ma ‘yata fa ,tayi din ,kema ai kinayi fin haka ma ,nawara taji kunya tace Kai anuty ,sukasa dariya ,gabansu cike yake d kayan motsa Baki ,Amman sai d tasa aka Kara musu wasu …..

Aishatu d tayi kyau Dan har hoto safwan y Mata a mota batare d ta sani ba ,noor ma tayi kyau ,amaren ma sunsha kyau ,faden kyansu ko suturar su Bata lokacine …..

Waje y d’au harama ,kida d wakoki masu ratsa zuciya kawai ake saki ,kowa na cikin Nisha ,dangin Ango Dana amaren sunsha liki Dan sun watsar d naira , Haka ankwashi hotuna ba adadi,Kuma sun cashe ,su sufayya Kuma sun juya ,har taro y watse ,aka Fara d’iban su Aishatu,sai d safwan yaje y sauke aunty zainab a gida kafin y wuce dasu gidan Ammy ,nawara dama mijinta yazo sun tafi ……

 

Bayan safwan y ajiye Aishatu ,y dinga kalonta ,Yana cewa kingaji ko , ALLAH y temakeki Noor tace Baki ko juya ma , Aishatu tasa dariya ,yace Amman kin kawoma su nawara Abinci ai ,shima dai Babu damuwa tunda su aunty Kika katama ,tace au nazaji harsu ,d na Mika wuya Dan karban hukunci …

Yasa dariya ,yace kin Haye ai sai gobe Kuma a waje dinner wanan Kuma tunda Ammy tace Dole muje ai muna jone Dan wani magnet zan zamar Miki ko makale hamantan jakarku d kuka taba yayi a baya ,yanzu kunwaye sai side bag kun rabata d hammata ,to Ni baya zan koma makale hamantan zan zamar Miki ,suna shagalin su Ina kula d babyn dake tare dake …..

Aishatu tasa dariya ,tace dadyn su Noor Dan ALLAH kaje ka kwanta wlh idan nayi over dariya cikina ciwo yakeyi ,yace to sorry Kar yayi jeki kawo min irin furar d kukasha jiya d Kika bani lbr …

Aishatu tace Kai dadyn noor daga baka lbr ,ba lailai Akwai yau bafa !Kuma ni kunya nakeji sai naje nacema Ammy abani fura nakaima ,gani Mai mij…….ta kasa karasawa …..

Y kaleta yace ,karasa ,gaki Mai miji ko? To b mijin bane? Barin Miki kankat !

Kawai y daya waya y Kira Ammy y Fara Mata shagwaba ,wai tarena ji dasu tunda aka Fara biki Bata musu tayin girki ba gashi jiya har fura Mai dad’i t raba ko ta musu tayi tasan basic masu basu a gida Kuma ….

Murmushi Ammy tayi tace ,oh safwan Abin y motsa ga aunty balaraba ,kamata shagwabar itace uwar fura ….

Aunty balaraba kanwar Ammy ce sun Saba d safwan sosai tanaji dashi ,safwan y Fara Mata shagwaba ,ta dinga bashi hakuri Tana rarashin sa tace gatanan kawo Mai hadin fura Mai Zuma d kwakwa d ayaba Mai dadin gaske ,d kanta zata kawo Mai mota base y wahalar Mata d Aishatu surikarta ba ,t Mike t nufi hanya wajen harabar gidan …..su Ammy d yayun Ammy sunata musu dariya …..

Aishatu ,mamakine y kamata ,taji Kato n sangarta , y Mata gwalo yace wlh Ni bani d matsala kunya kekika Santa , inma zakiyi course kiyi Dan bakiga komai ba ,…..

Tace ,Kai dadyn noor ka girma fa ,yace a wajen ki ba ? Awajenki ma ban girma ba ,I will show u ,with time ,ki rubuta ki ajiye ,itadai batayi wani dogon nazari ba har aunty balaraba t karaso ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button