HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Ussaina nata dariyar mugunta , hassana ko sai cewa take Dan ALLAH pass tens ,muyi abinda yake Akwai …

Suffaya ce tace ,ai abinda yake Akwai shi akeyi ,Amarya kedai ,jeki ki kwanta ko ki Gama wayar ki d gwarzon ki tunda kin kasa an d’auka tuni ,ba jinkiri ba jira ,miji kinsamu Yana sonki kina sonshi bake Kika bishi b bare ki kamu d hawan ruwa ko n jini. …

Huzna t Fara zargin d ita ,suffaya take ,ganin Kar Abin y musu b Dadi kawai tace ….

Ai dangin mu Akwai farin jini ,jinin baya jinkiri ,Haka ake biyomu ,harda masu wanke wanke ,tayi hanyar waje batare d tajira amsa daga suffaya ba …

Aiko cikin daga murya ,suffaya tace bashi Kika d’auka ,kowa yaci tuwo damu miya yasha ,ki jira biya …..

Ussaina sai dariya ,kinmin daidai aunty na Aishatu kema kinyi try sai kin Kara dagewa ,wlh Yaya safwan takema wanan haukan …

Suffaya tace kowa ma y sani harshima , hassana tace Baki d mutunci ko ussaina aunty kice fa ! Ussaina tace and so what! Bakiga abinda takeyi b ,kema fa kinsan komai …..

Hassana tace kici gaba ,tunda ke ba’a fada Miki kiji….

Aishatu ce tace, gaskia usy kiji abinda ake Gaya Miki ,sis dinki n Miki mgn kun kusa rabuwa fa ,y Kamata ki koyi biyaya gaba take d ke ….

Aiko ussaina Tana dariya t rungumo hassana wayo my twins hakane fa wlh jinake kamar afasa kaini sbd Kar araba mu ,tsahon shekaru b Abinda yake rabamu sai yau kawai zuwa gobe ace Aure zau rabamu ….

Tun Abun anayi d wasa dariya ,mutane n sako nasu zancen Akan shakuwar su ,har Abun y zama na gaske kuka ya kwacema hassana d ussaina ,kukan gaske hawaye sharban a fuskokin su ,suna kukan rabuwa d juna zuciyar su Bata tab’a karyewa irin ta yau ba ,tun suffaya d Aishatu n rarashi har Abun yafi karfin su ,Suma suka kusa zubar musu d hawayen Dan har y Fara zuba nasu hawayen suka mayar dashi d kyar , Aishatu ce taga Abin b na Wasa bane Kar kansu yayi ciwo t tafi Kiran aunty balaraba ….

Koda t shiga ,huzna n gefen aunty balaraba suna hirar zumunci ,sai huzna t Bata Rai ganin Aishatu ,itako Bata ko kaleta ba ,tace aunty kizo ki lalab’a Mana su twins daga Wasa Abu y koma gaske ,tun d’azu suke kukan rabuwa munyi munyi sunki rabuwa sunki Dena kuka harmun tayasu mungani ….

Balaraba tace ,shashanci harkuma kuka tayasu kukan d girman ku ga yanayin d kuke ciki?

Ammy najin su sai murmushi d takeyi ,sai suka tuna Mata d rabuwar d zatayi dasu itama ,d da Hali itama d tayi kukan Amman Inna …

Harda yayar Ammy d kanwar Alh su akatafi Dan rarashin twins har huzna …

D kyar d ban Baki sai d aka raba musu daki suka sasauta d kukan ,Dole aka maida ussaina wajen su Ammy ,ita Kuma hassana Tana tare d su huzna d suffaya d Aishatu ,huzna sai rarashi takeyi adole g yayar amare….

Daga baya ganin sunce kansu duk ciwo yake
Aunty balaraba t Basu magani sukasha ,tace ussaina t kwana a tare dasu ,huzna aka Sami madogara t gudo daga cikin su suffaya t dawo wajen ussaina Dan su kwana tare ….

Suma sukayi kwanciyar su d hassana abinsu ,Bayan mazajen su sunkirasu a waya sun gama Shan love din su ….

“NAWAL angayace ta bikin su twins har ta waya hassana t tura Mata d gayata ,sanan ankai musu lV d na d’aurin Aure d na party d na wunin iyaye kowane anbasu ,mama t zata NAWAL zata leka ko party 1 daga cikin ,Amman shiru batayi mgn zuwa ba Suma su twins Basu damu dama d zuwanta ba …

Mamace cikin Daren take cemata ,ta Dena Abin da takeyi ba Hali na gari bane! Dan Haka ko tanaso ko Bata so t shirya gobe wunin iyaye d dinner sai ta zabi Wanda zata aciki Dole taje t musu ALLAH y Sanya Alkhairi ,ganin b sauki sai ALLAH har Tana Kai karar ta wajen Abban ta ,shima yace taje ko plashing ta musu t dawo ,mama t dinga mamaki ,Tana ganin Abban NAWAL kamar yadan Fara saukin Hali yanzu Amman fa ra’ayinsa Yana Nan ,Jin mgn Abbanta yasa tace zata dinner it’s d kawarta ,mama tace to !

Washe gari gidan y kacame anata fama d karbo order Abinci d aka bayar sbd ‘yan d’aurin Aure Dan around 10:30am za’a d’aura Auren Dan wasu bakin ma samako sukayi kamar anan suka kwana ,gidan Ammy y dinke d jama’a maza d Mata anata fama d Abin Karin kumalon safe ,wasu alale d kunun gyada wasu tea d bread ,wasu waina d Miya ,gasunan dai wasu kunu d awara kowa d Abin d yake burin ci ….

Anata fama har time ya gabato ,su Yaya d safwan anci babbar Riga sunsha anko na malum malum d sukayi anko har Alhajin su suka dinka ma sunyi matuk’ar kyau ,suka shigo gidan suna gaisawa d maza ‘yan uwan Alh d Ammy daga baya suka shiga cikin gidan Dan gaishe d su Ammy d yayunta ….

Anata tsokanar su sunata fara’a d wasa d dariya ,huzna anci kwaliya tun farar asuba ansaka amwani swees lece anata Fadi anci kwaliya kamar ‘yar baby,tunda tayi tozali d safwan taji komai y kwance Mata ji tayi kamar ta rungume shi ko zata Sami skuni ,ga wani haiba d kwarjini d y Kara yi Mata ,shiko koyasan anyi halitar huzna a wajen ,y kula kowa amman ko kalon inda take beyi ba ,yau b ranar fushi bace Dan Haka t karya bilenta tace Yaya S Ina kwana ?

Ba tare d y kaleta b yace lpy ,huzna matafiyan dare,tace Kai dama yasan Tana wajen kawai dai haline irin n y s ? Tace Kai y s wai matafiyan dare b gani n kwana har na hantse ba !

Yace kwarai kuwa y gajiya ? Taji dadin tmby tace akwaita y s ,Dan ban wani huta ba ,yace sai a Baki daki Kita hutawa zuwa Bayan Gama biki ko Kya huta gajiyar?

Tace Kai y s to me akayi kenan ? Yace hutu ! Tace haba hutu be ganni b bikin twins guda dama nazo a makare Kar na Kara laifi Kan laifi Mana !

Can Yaya yace huzna b mgn ne? Sai taji kunya tace laa Yaya Ina kwana y katashi ?

Yace hmmm lpy Lau na tashi ,y gajiya ? Ko da yake naji kina fadama Dan uwanki akwaita ,….

Tace eh wlh ,Amman zan huceta sai mungama d shagalin biki ……

Aunty balarabace tace ,kunje kunga lpy iyalan ku kuwa? Yaya yace aa bamu hadu ba naji twins nacewa suna wanka ,sai anty balaraba tace ok shiryawa sukeyi kenan b matsala …

Can suka tashi suka fita ,huzna t dinga bin safwan d wani mayunwacin kalo kamar zata hadiye shi ……

Koda suka fita sukaci Karo d suffaya tayi matuk’ar kyau cikin wani d’inkin shadda Mai masifar kyau Kofi d yalon Aiki d sunyi kyau matuka mayafi yalo takalmi d jaka yalo ,suka gaisa d safwan t Fara Hira d mijinta ,safwan y Gaza hakuri yace Ina my wife ?

Suffaya tace ,masu wife barin maka magana d ita nasan b iya shiga zakayi ba sbd Mata …..

Tare suka fito d Aishatu ,ita kawai yake kalo ,ta matuk’ar kyau kayan sun karbeta d’aurin head d’inta y zauna komai ya hadu ,Bayan t gaishe d Yaya t koma gaishe d safwan ,sai g aunty balaraba t fito ita d huzna zasu waje gidan Don gaisawa d wasu Baki maza ..

Aunty balaraba n ganin kowane d matar shi g adon ciki ,sai t Fara kashe musu hotuna Tana yabon tsarin su d kyawun da sukayi ,sunsha hotuna a wayar ta ,huzna Kam gaba tayi t barta Dan ji tayi bazata iya jurar ganin hakan b ,kowa y hango kuluwar d tayi Dan Haka safwan d wayarshi y koma d’aukan su a hoton Yana canja style …..

 

Biki yayi biki ,har angama had’uwa antafi d’aurin Auren a babban masalaci kusa d gidan su ammy …..

Bayan andawo aka Fara raba takeaway abaci anasha …

 

Cikin gida kuwa kuka y zamarma su twins sabo Jin anata tsokanar su andaura sunzama masu igiya 3 akansu ,sai d aunty balaraba t Hana tsokanar sanan su Aishatu suka dinga rarashin su sukayi shiru ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button